🤷♂️ *ADDININMU* 🤷
( *BY S REZA* ✍️)
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
*ADDININMU*
*PAGE* 👉1️⃣0️⃣.... *ABDALLAH.* Cikin tsananin mamaki yake kallon address ɗin gurin da zata gabatar da taron nata, tabbas unguwar sune, sannan kuma ƙofar gidan maƙofcinsa, kenann hakan nanufin yau zatayi rawa da waƙa a ƙofar gidan sa!. Afili kuma ya ce "Jiya taje bikin abokina har ta samu damar cin mutuncina, shine yanzu ma take son ta ƙara samun damar yi a karo na biyu ko!. Kallon sunan sabuwar ƙasidar da tace zata sake a gurin taron yayi, afili ya karanta sunann waƙar. *BUƊAƊƊIYAR WASIƘA.* Take ya saki dariya sannan ya kashe wayar yana mai aiyana cewa kodai shi takeson tama martani.
*MARYAM.* Wani ihuu tayi haɗi da kwashewa da dariya irin dariyar da kana gani kasan ta muguntace. Da gudu tazo gurin Mommy sannan ta ce "Mommy albishirin ki? Tayi tambayar cikin dariya. Mommy ta ce "Lafiyar ki kuwa? Kinzo sai dariya kikeyi kamar wacce ta zauce?. Tsabar dariya Maryam ta kasa magana sai kawai ta miƙawa mommy wayar tana cewa... "Mommy karanta kiga Ikon Allah.
Bayan Mommy ta gama karantawa ne ta ce "Na gani za'a ayi walima ne a unguwar su yayanki kuma shine abun dariya? Maryam ta ce "To ai Zainab Ambato ce zata gabatar da waƙoƙin ta a gurin, kuma kalli wannan sabuwar waƙar kigani, itamafa agurin zatayi, kuma Allah daga jin sunann waƙar zatayi sweet. Tafaɗa haɗi da cewa ai kuwa baza'a barni a bayaba, dama bamu taɓa haɗuwa da itaba saide daga nesa, yau kan har ƙawance zamu ƙulla. Cikin mamaki Mommy ta ce "Amma ai yayanki ya hanaki shiga lamarinta ko? To saboda haka ban yarda kije ba. Maryam ta ce "Mammy kirabu dashi ni nasan komai, shimafa Allah yana son ƙasidun yarinyar kawai dai..."kafin ta ƙarasa Mommy ta kai mata duka tana cewa ai zai nado mara kunya kawai. Ita kuwa Maryam cikin dariya ta je domin shiryawa.
*ZAINAB. POV*
Kallon taron al'ummar dake gurin takeyi wanda kusan rabunsu basu taɓa ganinn taba. Cikin farin ciki da ƙwanar mosoyan nata take takowa izuwa gurin da a ka ware domin ta. Gurine wanda a ka masa ado da hotunan Shehu Ibrahim inyasa da dai sauran shehunan su, kowa burinsa ya gaisa da ita, yayinda matakan tsaronta da mai gidan da ya gaiyatona ya haɗasu da ita domin bata kariya, sai tare mutane sukeyi. Ita kuwa Zainab faɗuwar gaban da takeji tin a gida sai ƙaruwa yakeyi.
A haka ta ƙaraso gurin sanan ta samu guri ta zauna tana sakin murmushi, halifan ta guda biyu mace da namiji, sune suka zauna a kusa da ita, can zuwa wani lokaci kuma ta tashi ta shiga bin layin duk wani malami dake kurin saida ta gaida shi. Saida malamai suka buɗe taro da addu'a kafin aka fara wa'azi a kan aure. Saida malamai biyu suka yi kafin a ka bata. Manyan malam gurin sai binta sukeyi da ido, daga mai aiyana cewa yau zai gabatar da kansa sai mai cewa yayiwa yaran kamu, sai masu jin cewar wannan ai irin tasu ce.
Cikin muryarta mai tsaki wajan yabon Annabi Muhammad S a w. Ta fara da addu'a sannan ta shiga gaida manyan malamai da dai sauransu. Nan fa aka saki kiɗa tafara yin wata ƙasida mai taken.... *INDAI KAASONI BANI DA FAR GABA, ANNABI NA BIKA BAN BI WANIN KABA* Nann fa al'ummar gurin suka ɗauka harda malamen dake gurin.
*ABDALLAH* kuwa yana cikin gidansa, yana jin duk abundake faruwa, damuwarsa ta saki wannan waƙar domin da ita zai yi amfani wajen kamata da hujja. Har cikin kunnuwansa muryar ta ke shiga wanda ya nutsu yana jin abun da take cewa a cikin waƙar. Saida tayi waƙoƙi guda uku, izuwa lokacin kowa nason jin wannan sabuwar waƙar, ai kuwa take aka kunnata. Kasancewar babu wanda yasan ƙasidar sai gurin yayi tsit ana sauraron ta.
*A.J. SARAH.*
Kallon mamaki sarah kebin A.J dashi ganin irin abubuwan da yake sawa a kawo kan teburin su, bata tashi ruɗewaba saida taga wasu daga cikin abokansa yaran masu kuɗi sunzo sun zauna a teburin, kuma suma yace su karɓi duk abun da sukeso. Nan fa sarah ta shiga zare ido, domin kuwa tasan abubuwan da a ka kashe sun fi ƙarfin kuɗin ta. Bayan an gama abun da za'a yi ne, kowa ya kama budurwar da yazo da ita suka fara aikata abunda ke kaisu gurin. Hannusa ta kama ta miƙar dashi sannan ta jawoshi izuwa gurinda ake rawa. kallon ta yakeyi ganin yanda take shafa shi ta ko ta ina, nann shima ya fara mayar mata da mar tani. Tin suna shan bakin juna har A.J ya jawota gefe, suka faɗa kan ɗaya daga cikin do kwayan gujerun gurin. Cikin fitar tunanisa ya fara kai hannusa izuwa ƙirjinta, wanda hakan ya bata damar ƙara tura masa ƙirjin nata, bata an karaba taji hannuwansa a fatar ƙirjinta, ya zame rigar maman ta ya sa hannunsa. Tin da AJ yake a duniya bai taɓa shiga irin wannan yanayin ba, haka ya dinga jinsa kamar ba a wannan duniyar yakeba.
BINABASA MO ANG
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
ActionThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3