🤷♂️ *ADDININMU* 🤷
( *BY S REZA...✍️* )
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
*ADDININMU*
*PAGE* 1️⃣3️⃣....... *HAJIYA BABBA.* Saida ta ji komai zam-zam daga gareta kafin ta sauƙa tana mai jin komai ya mata dai-dai, lumshe idanuwanta tayi tana jin wani irin nutsuwa na shigarta ta ko ta ina, afili ta furta... Auran namiji mai jini a cika shine rayuwa, kai gaskiya addinin musulunci yayi wajan halarta auran ɗan cikinka, kai A.J Allah ya saka maka, aure kuwa mutu ka raba, yau ɗinnan ma zamu bar ƙasar domin kuwa bana son komai ya taƙura mana daga cin amarci. Hannunta ta kai tana shafo angon nata domin taji ko yana jin me take cewa, ita a tinanin ta shima idonsa biyu. Sai taji kamar ma a sanƙare yake, ai da sauri ta sauƙo daga kan gadon ta kunna hasken ɗakin.
Mai zata gani!. Ganin A.J tayi a kwance kamar babu numfashi, ai da sauri ta hau kan gadon tana mai taɓa ƙirjinsa ko zataji yana motsi. Toilet ta shiga ta ɗebo ruwa ta watsa masa, amma bai farkaba. Ita kanta ta manta da cewa babu komai a jikinta. Ruwa mai sanyi ta haɗa sannan ta je ta ɗaukoshi kamar wani ɗan jinjiri. Dama ba komai a jikinsa, ai kuwa ta tsoma shi a cikin ruwan, itama ta shiga ciki. Ruwan take ɗiba a hannunta sannan ta zuba masa a kai, saida tayi sau biyar ana shidanne ya saki wani dogon ajiyar zuciya, wanda yasa Hajiya Babba yin wani murmushi.
Buɗe idonsa ya keyi a hali har ya saukesu a kan ƙirjin ta wanda idon nasa ya tsaya a haka yana kalllonta kamar yasumu tibi. Tariyo abunda ya faru yakeyi wanda cikin lokaci kaɗan ya fahimci abunda ya faru. Kafin yayi magana yaji hannuwata a wani ɓangare daga jikinsa. Sai a lokacin ya sake dawowa cikin haiyacinsa, ganin dagashi har ita tsirara suke, ya meƙe tsaye wanda yayi dai-dai da miƙewar Hajiya Babba itama, aikuwa sai gasu tsirara shida ita, wanda lokaci ɗaya A.J ya koma cikin abun wankan yana rufe ido.
*ZAINAB VOP*
Kowa dake gurin ya nutsu sosai domin kuwa waƙar ta ɗau hankalin mai sauraro. Kaman yanda ta ce, sunan waƙar buɗaɗɗiyar wasiƙa, tabbas hakane, buɗaɗɗiyar wasiƙarce, domin kuwa tayi maganganu masu kamada tanayi da wanine ko wasune. Ana cikin haka, manyan mutane suka fara mata ihisani, wasu suna mata kyutar guɗi wasu mota wasu kuma addu'a. Saida ta gama tsaf, suna cikin haɗa kayan su zasu tafi, taji ana kiran sunan ta cikin dariya.
Da gudu Maryam ta ƙaraso gurin haɗi da rungumeta ta na cewa "Saiyada Zainab ni masoyiyar kice sosai tin ba yauba naso in ganki amma Allah baiyiba. Cikin mamaki Zainab take kallon Maryam domin kuwa tasan ta, Kasan cewar duk family Shek Kabiru kabuga, ba ɓoyayun fuskoki bane ga al'umma. Amma Zainab ta kawar da mamakin ta ce "Aiya ya kk?
Maryam ta ce "Ina lfy ya ƙoƙari da haƙuri da mu?
Zainab tayi jimmm! Sannan ta ce "Haƙuri ai sai ma'aiki...mudai muna kwai-kwayansa ne.
"Hakane...to yanzu zan iya samun number ki? Ta faɗa har yanzu tana murmushi.
Zainab ta ce "Ba damuwa. Sannan ta bata wayar tana satar kallon Maryam ɗin, tana ganin yanda yarinyar ke kama da Abdalha kamar an tsaƙa kara.
Saida Maryam ta gama sa sunan sannan ta kira, tana kira sai taga wayar na ƙara, ta ce "Maryam shek Kabir kabuga.
Itama ta ce "Zainab A Ambato.
Maryam ta ce "Waye baisankiba a faɗin Nijeriya?
Zainab ta ce "Shek Kabir kabuga shine ma haifinki?
"Kin san shi ne? Tafaɗa domin taga me Zainab ɗin zatayi.
Zainab ta buɗe baki da nuyar yin mgn sai tayi ido biyu da Abdalha wanda ke fitowa daga cikin gidansa ganin al'ummar gurin sun ragu, ai kuwa dama idonta gurin yake kallo, ai kuwa shima dayake yafito a zuciye sai kawai ya kai kallonsa gurinda yake tinanin zai ganta. Ai kuwa yana ɗaga kai sai suka haɗa ido.
DU LIEST GERADE
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
ActionThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3