🤷♀️ *ADDININMU* 🤷♂️
*BY S REZA ...* ✍️
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...✍️*
*KUYI HAƘURI DA WANNAN BABU YAWA*
*ADDININMU.* *BABU EDITING*
*PAGE1️⃣4️⃣*......Police ɗin ya kallesu cikin ƙas-ƙanci da cin mutuncin ya ce "Idan baku rufe mana baki a'nan ba sai na gyara muku zama yanzunnan, kodan kunci sa'a tunda kukazo babu wanda ya taɓaku shine har kuke samun damar cika mana kunne da surutu, to karna ƙara jin tarinku agurin nann idan ba hakaba kuma...babu ruwana da ku matane cin ubanku zanyi tunda ai ku ɓarayine. Cikin tsananin tsoronsa Innah da Nana suka ƙuntse kukansu suna takurewa a guri ɗaya. Haka Innah da Nana suka wayi gari a cikin seel ɗinnan babu ci babu sha, sannan babu wanda ya zo garesu. Misalin ƙarfe 8 nasafene Nana ta ce da Innah "Innah yunwa nakeji bazan iya ba a kwai kuɗi a gida da yaya ya bani zanje na ɗauko sai mu dinga siyan abinci.
Innah ta ce "Nana addu'a kawai zamuyi in ba hakaba bamuda kowa in ba Allah ba, sannan kike maganar zuwa ɗauko kuɗi yaushe yayan naki ya baki kuɗin? "Ranar da zai tafine kuma sunada yawa, zasu ishemu harda Berlin kanmu, bari na ƙwada zuwa ko Allah zaisa ya barni. Innah ta ce "Nana daga yau har zuwa lokacin da zan mutu a cikin wannan gurin to wallhi bazan ƙara taɓa komai na Abdul jabaru ba, indai shine zai fitar dani, kokuma kuɗin satar da ya saba samowa to na ƙwammace mutuwa a haka, saboda haka nidai babu ruwana da komai da ya shafi Abdul jabaru, tunda har zai iya jawo masifa ya gudu ya barmu, to haƙura! na haƙura!!! Inna ta ƙara maganar ƙirjinta na mata wani irin zafi, ga hawaye da ya wanke mata idanu.
Nana ta ce "Haba Innah dan Allah karkici haka, shima yanzu ai bakisan halin da yake ciiiba dan Innah ki yarda da yaya bazaiyi abunda kike tunaniba, Please ina ki yafe masa dan Allah!? Itama ta fashe da kuka tana faɗawa jikin Innah wacce kana ganita kasan bata cikin haiyacinta. Inna ta kasa magana sai kuka takeyi tana shafa gadon bayan Nana. Nana ta ce "Innah yunwa wallhi ina jin yunwa zan mutu! rabona da abinci tun jiyafa! Please ki yarda naje na ɗauko kuɗin dan Allah Innah ta? Tafaɗa tana ɗagowa daga cinyar Innah tana riƙe ciki.
Domin itama yunwar takeji kamar ta yi ihuu amma haka ta danne ta ce "Nana idan har zasu barki kije to kije ki samowa kanki amma nidai ƙwara na mutu yau ɗinnan, tashi kije Allah yasa ya saurareki. Nana ta ce "Amin. Bakin sell ɗin tazo tana kallon ƴansanda da suke kaiwa da kawowa a gurin, shikuma mai jiran nasu yana tsaye da wani alamar dai wata maganar sukeyi. Sai ta rasa me zatace masa domin ya sauraretNa, ai kuwa ta tuna ba Hausa ya keji ba, domin tunda sukazo bataji yayi Hausa ba.
Ta tsaya a bakin gurin ta ce "Am am am yalla'bai". Bai jiba. Sai ta ɗaga muryar ta ce "Oga. Nan ma baijiba alamar dai zancen nasu ya ɗauki hankalin sa. Sai ta sake cewa "Ogaaaa! Da ƙarfi wanda yasa dukkanin yan sanda seda kowa ya juyo yana kallon ta.
*LAƊIFA. SALIS. POV*
Haba Umar meyasa baka sanar dashi ba? Cewar laɗifa tana waya da Umar tana sanar masa da cewar ta kira number Samuel amma ba'a ɗagawa, shikuma yana sanar mata da cewar ai Samuel baya ɗaga baƙuwar number. Yanzu ina zamu haɗu domin zuwa gidan nasu?, cewar Laɗifa? Umar ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "Bazai yiwu muje gidansu yanzuba amma dai ki tsaya zan kirashi zuwa gobe domin ina tunanin bai dawo bane?
Cikin muryar da kana ji kasan tayi zurfi cikin soyayya ta ce "No Umar please yanzu nakeso muje, wallhi ina son ganin sa, idan ban ganshiba a kwai matsala? Umar ya ce "Ok tom kisameni a unguwar mu sai mu tafi yanzu. Ai kuwa cikin sauri ta ce "Tom jost minti goma.
Haka da yamma Salis ya koma gidan su Nana ko an sakesu amma yaga har yanzu basu dawoba. Nan fa hankalin sa ya tashi domin zuwa yanzu yasan babu lafiya sosai. Haka ya zauna a gurin har zuwa wani lokaci kafin ya bar gurin cikin rashin kwarin gwiwa. Washe gari ma da safe ya kira number Nana amma no amsar, haka ya koma gidan ya sake ganinn sa a rufe kamar yanda ya rufe jiya, domin farkon zuwansa a buɗe ya samu ƙofar Shine ya rufe.
KAMU SEDANG MEMBACA
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AksiThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3