Chptar 18

7 1 0
                                    

*ADDININMU*

                  *S REZA...✍️*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

*Masu satar fasaha kuna bani mmk wlhi! Kuma zakaga mutum ko a jikinsa tsabar ƙoƙari! To littafin _ADDINIMU_ dai gashi na dawo.*Mai dubun masoya duniya shike da maganin ƙunci, ( M inuwa) tabbas badan kuba da na haƙura da rubuta littafin ADDININMU. Happy Sallha to all my... I'm back.*

    *PAGE* 1️⃣8️⃣ *Babu editing*

..........Cikin tsananin mamaki Abdalha yake kallon Mommy wacce ta ɗaga hannu ta mareshi a kan abunda batada  tabbacin sa, ya kalleta cikin mmk ya ce "Momy ban saniba bansan komai ba wasune  suka saceta amma ni bani bane pls Mommy ki yarda dani karki bari zuciyarki ta aminta da wannan zancen. Momy ta kalli ɗan nata cikin tausaya masa tace "Shin me ya kaika gurinta lokacin da abun zai faru? "Mommy bansan komaiba kamar yanda na sanar miki, kuma nuda kaina zan gano komai pls ki yarda dani. Yana gama faɗin haka yabaar gidan cikin tsananin mamaki abubuwan da ke faru kamar wani shirin Film.  Lokacin da Abdalha ya isa ƙofar gidan nasu har police ɗin nan sun kama na kamawa sauran kuma sun gudu, kallon police guda biyu da ke jikin ƙofar gidan nasu yayi wanda a ka bari domin basu tsaro yayi,  kallon su yayi cikin takaici domin kuwa kallo ɗaya ya musu ya gana ba musilmai bane, a zuciyarsa ya ce "Tabbas wannan shirine kuma zan kawo ƙarshensa yau. Police ɗin dake nufoshi ya ɗagawa hannu a lamar bayan tsaron nasa , amma police ɗin yace  ai hakan umarnine  dole sai yayi. Haka badan Abdalh yasoba suka shiga motar shida ɗan sandan suka fita.

Ɓangaran gidan su Zainab kuwa har yanzu babu labarinta, yayinda Isa ya dinnga yaɗa cewar Abdalha ne ya saceta kuma tabbas yanda labarin ke bazuwa idan kagani dole ka yarda. Ƴan gurgiyar Abdalh da sukaga abun ya fara yawa sai suma suka fara mayar da martani akan ai shi Abdalh baɗan bidi'a bane yana amfani da ilimin sa, saide kaga majalista ta samari daga hira sai zage-zage sai faɗa. Har takai ta kawo wasu daga ciki suna tono tsoffin asirin wata gurgiyar. Budurwa da saurayi aboki da aboki mata da miji, malami da ɗalibai, uba da ƴaƴansa, maƙofci da maƙofci, dukkan su mutuƙar ba kungiyar su ɗayaba to Tabbas sanadiyar wannan abun Kai ya ƙara rabuwa. Kai abundai ba'a cewa komai domin kuwa lamarin ya gawarta.

*SALIS LAƊIFA POB*

Cikin sauri kamar zata tashi sama tsabar ruɗewa ta banko ƙofar palorn tana ƙoƙarin haurawa sama, sai tayi ido biyu da Salis yana zagayawa a ɗakin cikin tashin hankali. Da gudu ta ƙaraso gurin da yake ta buɗe baki zatayi mgn, cikin harɗewar murya  ya ce "Com com comand  Comandar Daniel ne ya kullesu?. Ya ƙarasa maganar yana kallon laɗifa wacce Salis ɗin ya ƙara sakata a cikin duhu domin ita bata gane me yaceba, ta daiji yace Daniel amma fata fahimci gaban ba. Ta ce "Pls Yaya banji me kace ba, itama ta faɗa tana kallon cikin idonsa? Salis ya ce "Gajiya Babba dole ta dawo yau ɗinnan domin kuwa a kawai matsala?.

Laɗifa ta ce "Pls Yaya sanar dani abunda ke faruwa ban ganeba fa? Ni nashigo da maganar Comandar kuma kaima naji kana min shin wani abun ya haɗoka dashi ne?

Cikin sauri Salis ya fasa danna kiran numbar Hajiya Babba ya dawo da kallonsa izuwa gurin Laɗifa ya ce "Me zaki sanar min akan Comandar ɗin?

Da sauri Laɗifa ta ce "Shine baban wannan yaron da nace maka inaso wannan Kristen ɗin..."Ai tin kafin ta ƙarasa Salis ya ce "No no  no, ya miƙe tsaye yana kallonta wacce itama ta miƙe tsaye ya ce "Bakida hankaline kin matan waye Daniel da har zakije kifara soyayya da yaronsa ko? Kafin ya samu matsayin Comanda ma ya muka ƙare dashi bare yanzu...damade baki sanarwa da yaron cewar kina sonsaba? Ya tambayeta yana son yaji tace masa bata sanarba.

Cikin kuka ta ce "Wallhi Bro bansan shine babansa bane ban saniba, ta faɗa tana ƙara fashewa da wani sabon kukan.

Salis ya ce "kin faɗa masa?

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMWhere stories live. Discover now