Chptar 21

7 3 0
                                    

*ADDININMU*

               *S REZA...✍️*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

*Kafin kufara karanta wannan page ɗin, inaso kutuna abunda nace a page ɗin farko, Pls* 🙏

          *PAGE. 2️⃣1️⃣*

......... Innah! Innah! Innah!  Cikin murna da ɗokin son ganin Innar tasa yake ranƙaɗa mata wannan uban kiran kai ka rantse da Allah irin ya hangota daga nesane amma bata jisaba. Saboda tsabar ɗoki da AJ keyine yasa bai ko kula da kurarr da gidan ya ɗanyiba, sai kawai ya nufi ɗakin Innah da sauri yana cigaba da kiran sunanta, wannan karan harda sunan Nana yake haɗawa. Cikin mamaki yake kallon ƙofar innar tasa abuɗe gakuma kwanukan abinci da sauran abincin dake ciki alamar dai andaɗe ba'a cikin gidan, da sauri ya fito daga ɗakin Innah ya nufi ɗakin Nana. Yana zuwa itama yaga ƙofar ɗakin abuɗe, har yanzu bai daina kiran sunan Nana ba, yana shiga idonsa ya fara sauƙa a kan kadonta, sai ya hango wayarta a kan gadon, ai kuwa da sauri ya ɗauka yana ƙoƙarin kunnawa, amma wayar taƙi kunnuwa, domin kuwa babu caji. Fitowa yayi da wayar izuwa tsakar gida jikinsa har rawa yakeyi domin kuwa izuwa yanzu jikinsa ya fara aiyana masa mugayan abubuwa a kan su innah. Sai a lokacin yabi ko'ina na gidan da kallo yaga  tabbas babu kowa a gidan. Afili ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ina su inna suka tafi!? Cikin zafin rai ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran Hajiya Babba, ai kuwa kira ɗaya ta ɗaga, tana cewa "Pls ina zuwa zan kiraka. Tana gama faɗa ta kashe wayar batare da tajira abunda zaiceba.

Sai a lokacin kuma ya fashe da wani irin kuka ya ce "No no no yana faɗa yana girgiza hannunsa yana jabaya, ya ce "Noooooooo! tabbas bai yarda da abunda zuciyarsa take cemasa akan su innha ɗinba, hakanne yasa yayi waje izuwa ƙofar gidan su, yana zuwa kuma ya tsaya yana kallon al'ummar gurin cikin rikicewa yarasa abunyi sai kawai ya nufi gurin taron samarin da ke kusa da wani ɗan shago, wanda shi a tunaninsa dai idan bai mantaba bai taɓa zama a gurinba ko kuma yayi musu mgn ko sallama aganin sa su ƴaƴan talakawa shima haka to me slamar zata ƙara musu, saidema idan yazo hucewa ya dinga musu kallon banza yayinda sukuma suka ɗaukeshi mai gyrman kai, domin kuwa sunsan bai ajiyeba kuma bai baiwa kowa a jiyaba sai shegin iyayi da nuna shi wanine.

Ko sallama baiyiba ya ƙarasa gurin tsabar a rikice yake ya ce "Ina kuka kaimin Innah ta da Nana Pls? Yayi maganar ne baisan cewar abunda yafito daga bakinsa ba kenann yaci gaba da cewa...Dan Allah ku fito min dasu sune kaɗai gareni pls dan Allah kuyi mgn Walhi zan iya shiga wani hali, idan laifi nayi muku a kaina zaku sauƙe basuba. Kamar haɗin baki yana kaiwa aya duk samarin gurin suka watse suka barshi babu wanda ya tamka masa sai wani guda ɗaya wanda daga gani kasan yafi kowa jin haushin Aj ɗin ya ce "Kai amma Walhi kama raina mana wayo, watoma mune ɓarayin da zamu sace maka u'wa ko? To me suke dashi da har zamu sacesu, kaje can gurin da ka aikata satar ka kanemesu amma ba nann ba. Kasan cewar sunji wai-wai AJ ɗin sata yiyi daga bakin duniya. Saurayin na gama faɗar haka ya bar gurin cikeda jin haushin AJ ɗin.

Shiru yayi yana tauna maganar yaron ta ƙarshe wai sata! sata! sata! Haka yaketa mai-maita sunan sata ko zai tuno lokacin da yayita amma ya kasa ya ce "Nine nayi sata!? To a ina! Kuma yaushe! ƙaryane walhi ƙaryane ni ban taɓa sataba saide wani amma baniba. Ya ɗaga kai domin tambayar gayan amma ko alamarsa bai hangoba, ya juya izuwa hagunsa sai yaga yara suna klonsa kamar wani mahaukaci. Tabbas sai yanzu yasan cewar ashe abokima wani ɓangarene da zai dinga taimaka maka a rayuwa, shi baida abokai duk yaci mutuncin su, ya koresu wai abota ƴaƴan talakawa a tare batada amfani. Chak ya tsaya bayan ya tuno da abokinsa Kamal, Wanda babu irin cimutuncin da bai masaba amma kamal ɗin yaƙi haƙura domin yana zuwa nemansa kokuma yaje su haɗu a gidan bredin da yake aiki a da. Da sauri yatashi domin nufar gidan su kamal ɗin amma ya ji ankira sunansa AJ.

Chak ya tsaya yana juyowa fuskarsa duk ajiƙeda hawaye, idonsa yayi ja duk ya fita a haiyacinsa. Kadija ce ƙawar Nana wacce itama ta samu labarin abun daga bakin ƴan unguwar domin kuwa kowa yaji lokacin da sojojin suka shigo unguwar kuma suka tafi da su Nana ɗin. "Sojojine sukazo suka tafi da Innah da Nana yau kwana huɗu kenan basu dawo ba kuma bamusan inane suka kaisuba. Ya manta da cewar yarinyar ta ce masa basu san me su Nana  sukayiba amma tsabar ruɗewa ya ce "Sojoji! mai sukayi, ya faɗa yana ruƙo hannun kadijar kamar itace zata sanar masa da komai. Ta sake cewa Walhi abunda na sani kenan. Tafaɗa cikin rawar murya domin riƙon da ya mata. Kafin  aj yayi magana wani saurayi da yasan AJ tare da Sarah ne ya ce...

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMDonde viven las historias. Descúbrelo ahora