Chptar 29

5 1 0
                                    

*ADDININMU*


             *S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

                *PAGE2️⃣9️⃣*

.........Ko wa da ke cikin ɗakin tsorata ya yi saboda ƙarar harbin bindigar, hakan ne ya sa gaba ɗaya suka cure a guri ɗaya ko wa na neman hanyar da zai tsira da rayuwar sa, shi ku wa Salis lokaci ɗaya idon sa ya sauƙa a kan abokinsa wanda ya ke gefe ɗaya cikin tsananin wahala. Da ƙarfi ya kira sunan sa ya na ƙarasawa gurin da ya ke. Da sauri Momy ta ƙara sa gurinda Samuel ke kurma ihuu domin harbin da a ka masa a ƙafar dama. Shima Daddy da sauri ya je gurin ya na kamo yaron nasa cikin tashin hankali. Yayinda ita kuma Hajiya Babba ta bi bayan yaron ta domin jin kiran sunan AJ da ya yi. Itama Sarah cikin kuka tayi gurin ɗan uwan nata  haɗi da rushewa da wani sabon kukan. Ita kuwa Laɗifa tsayawa tayi a bakin ƙofar ta rasa gurin wa zata je, domin ganin jini a ƙafar Samuel ya tasher mata da hankali, hakanne ya sa ta tsaya ta na kallon sa cikin damu wa, ai kubwa bata san lokacin da kuka ya kuffce mata ba tana rufe bakin ta kar kowa ya ji.

Da sauri Salis ya ɗago Aj da ga kwancen da ya ke yana kiran sunan sa AJ...AJ... Amma ina AJ ko magana ma yakasa domin kuwa ya daku ba da wasaba, shi kuwa sai gir-gizashi ya kayi ya na ƙara kiran sunansa, kuma yana tunanin me ya kawo AJ ɗin cikin wannan gidan! Daddy ku wa ganin Hajiya Babba na ƙoƙarin shiga ɗakin ne yasa da sauri ya sha gaban ta ya na tambayarta ina zata je? Cikin tsananin ɓacin rai da tsanar da ta kewa yayan mijinta ta fara surfa masa masifa ta na cewa idan bai bata hanya ba zata zabga masa mari, ai kuwa Hajiya Babba ta man ta a gaba wa take domin kuwa ranta yayi mugun ɓaci idon ta duk sun rufe, har wani ruwa ne ya cika a cikin idanuwan na ta. Kafin ta gama rufe baki taji sauƙar mari guda biyu hagun da dama. Cikin ɓacin rai da ganin komai ya lalace ya nunata da hannu ya fara magana cikin fushi.

"Walhi saina kashe ki idan baki bar gidan nan ba, shegu dangin tsiya, ai dama nasan mutuƙar mutam ya zama mai yin salla to shikenan kun gama shanyeshi, to dan uwarki harda ubanki ki bar gidannan ko kuma na sa a"...Bai ƙarasa ba yayi ido biyu da Salis reƙe da AJ ya fito daga cikin ɗakin. Da sauri dukkansu suka kai kallon su izuwa gurin da Salis ke tsaye. Da sauri Sarah ta bar gurin da Samuel ke ihuu har zuwa yanzu wanda dukkansu kuka sukeyi an kuma rasa wanda zai ɗauke shi izuwa asbiti sai ihuu sukeyi. Da sauri ta ƙaraso gurin ta na mai kamo hannun AJ ɗin cikin wani sabon kukan. Sai ji kayi itama Daddy ya ɗauke ta da mari sannan ya turata waje, yana ƙara tabbatar ma da cewar babu ita babu AJ.sojoji ku wa Tinda sukayi wannan harbin suka shiga cikin tashin hankali ganin Samuel suka samu ba Salis ba, sannan tunda Ogan na su ya zo bai ce musu komai ba sai yanzu. Ya basu umarnin fita da Samuel. Ai kuwa da sauri sukayi waje dashi. Hajiya Babba kuwa ta na riƙe da hannu a kunci.

"Eh tabbas shekarun da ya wa, kuma abubu wa da dama sun sauya, sannan kuma yanayi ya sauya ha ka zalika duk wani abu mai rai to tabbas yana ƙara girma ne, sannan abu mai muhimmanci baya taɓa gushewa da ga mahalli da. Tin lokacin da ya yi ido biyu da yaron da ya shigo ɗakin jikin sa ya sanar masa da cewar tabbas yau Allah ya karɓi addu'ar da suka daɗe sunayi, ya  na cikin kallon yaron ne har yaron ya taso riƙe da ɗaya yaron da a ka shigo da shi ɗa kin nasu ɗazunnan. Kukan da yazo masa ne yasa ya kasa yiwa yaron magana har ya fita. Yana cikin haka ne yaji muryar da ba zai taɓa mantawa da itaba koda kuwa mutuwa yayi kuma ya dawo wannan duniyar bare kuma bai mutu ba. Tabbas baiyi niyar tashi ya fito gurin ba, amma jin yanda yayan nasa yake cin mutuncin Addinin nasa da kuma yana jin cewar Allah ne ya turo wannan ranar domin ta zama warakar damuwar da suke cikin Sudan ƴan u'wansa, hakanne ya sa ya miƙe daga gurin da yake zaune cikin wa su kaya yagaggu sun gama fita a haiyacinsu ga tarin gashi da ya gama mamaye masa fuska, gashin kansa yayi jaa ,sannan ya mur-murɗi, ha ƙoran sa sunyi jaa sun fita a haiyacin su, gaba ɗaya kamarsa ta canja, daga gurin da kake zaka hango ƙashin ha ƙaƙƙarin sa a waje. Ganin yayi hanyar fitane yasa sauran mutum ukun da suke ciki suma miƙewa suka biyo bayan sa, suma cikin irin halin da yake ciki.

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMDonde viven las historias. Descúbrelo ahora