*ADDININMU*
*S REZA...✍️*
*First Class writer's asso...*
*PAGE3️⃣5️⃣*
..........Kuka Nana takeyi ta na mai gir-giza AJ wanda har zuwa yanzu bai motsa ba, Tashi ta yi cikin sauri ta ɗebo ruwa ta watsay masa ta na binsa da ido kamar wacce bata taɓa ganinsa ba, ganin bai motsa bane ya sa ta ƙara watsay masa ruwan a karo na biyu. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke ya na mai buɗe idonsa a kan Nana, sai kuma ya riƙe kansa ya na jin yanda kan ke juya masa, hannunsa ta kama ta na masa sannu cikin kuka. Ya buɗe baki ya ce "I'na Innah? Sai a lokacin Nana ta kai kallonta gurin da ta bar Innah ta na ce wa "Ga ta ce"...."Tsaya wa ta yi da hannun na ta a yanda yake ta na bin gurin da kallon mamaki. Da sauri ta miƙe da gudu ta shiga kiran innar ta ko ta ina. Da gadu ta ƙara fitowa ta na ce wa "Yaya Innah ta gudu walhi bata gidannan ta taffi. Ta na magar ta na kuka. Da sauri AJ ya miƙe tsaye yana nufar waje da sauri riƙe da kansa dake mugun sara masa. Itama Nana tabiyo bayansa ta na kuka. Ya na fita ya ci karo da Innah a ƙofar gidan a duƙe tana kuka tana sharar hawaye.
Da sauri ya faɗa jikinta yana fashewa da kuka ya kasa magana, itama Nana ta na zuwa ta faɗa jikinsu ta na mai sakin nata kukan. Kuka sukeye duk su ukun babu mai rarrashin wani a cikinsu, inna ta shiga shafa kan AJ tana mai jin tausayin sa a ranta. Cikin kuka ta fara magana "Tabbas bazan iya tafiya na barkuba domin bakuda kowa sai ni, kaman yanda nima bani da kowa saiku, amma tabbas Abduljabaru ka ɓata min rai wanda bazai musaltuba, amma na maka uzuri kaman yanda mahaifinka ya ce min a kanka, tabbas kai ɗin ɗan arziƙine, ka ɗauki nauyinmu alhalin kai kanka kana buƙatar mai tallafa maka, cinmu shmmu suturarmu gurin kwanan mu duk kaine, amma ka ƙi ka tsaya ka faɗa min gaskiyar sana'ar da kakeyi, sannan meye ya haɗa ka da wannan ar'nan? Allah dai yasa ba da gaskene sata kamasa ba? Shin Abduljabaru me kake ɓoye mana a tattare da kai? Muna son sanin gaskiya amma dan Allah kar ka ƙara mana ƙarya?
Cikin kuka AJ ya ce "Tabbas Innah nayi muku ƙarya wanda yanzu haka ta sakani a halin da na sani, kuma tabbas yau zan sanar muku da komai a kan kuɗin da nasamu, amma dan Allah Innah karki gujeni kisan cewar duk abun da na ai kata danku nayi pls innah? Innah ta ce "Innalillahi wa inna i'laihim raji'un, Allah dai yasa ba wani abun kaje ka ai kataba, shin ka manta lokacin da kake cemin AJ baya sata? AJ baya neman mata? AJ ba zai aikata duk wani abun da Addininmu ya yi hani da shiba? To Allah dai yasa baka ai kata ko ɗaya daga cikiba? AJ ya ƙara jin cewar lallai ya aikata kuskure, ita kuwa Nana ta ke ta tuno da zancen Kadija na cewar ya yi wa yarinyar cikine, sai kukanta ya ƙaru domin izuwa yanzu ta fara yarda da hakan.
AJ ya ce "Innah mushiga gida sai muyi zancen a ciki.Bayan sun shiga gida Nana ta ɗora ruwa saida yayi zafi sannan ta juye a bokiti ta ɗauka izuwa banɗaki. Saida AJ yayi wanka sannan ya ɗauki kayan adides riga da wando ya saka sannan Innah ta ce yaci abinci tukunna. Itama innar wanka tayi tazo ta zauna kusa da angon na ta ta ce "Abduljabaru kaji tsoran Allah karka sake ɓoye mana damuwarka, kasani duk abunda ya sameka muma ya samemu, duba fuskarka tunda ka shigo na ganka a haka saida gabana ya faɗi, yana daga cikin abunda yasa kaga na kasa tafiya na barku, kullum addu'a'ta Allah yasa kana lafiya ya kuma dawo mana da kai gida lafiya a duk inda kake, haƙiƙa kullum cikin dare sai na tashi na roƙi Allah a kanka, amma a fili ina nunawa Nana cewar bazan yafe makaba domin ta gane cewar abunda kayi ɗin ba dai-dai bane. Inna ta ƙara sa ta na ruƙo hannunsa tana mai kallon fuskarsa dake a kumbure. Inna ta ce "Bari kaji halin da muka shiga a dalilinka?
Take Innah ta kwashe komai abunda a ka musu ita da Nana, tun daga marin da a ka fara mata a cikin gida izuwa gidan ƴan sanda da a ka kaisu, ga cin mutuncin da ƴan sandan suka musu, da taimakon da Salis ya musu shida abokin AJ ɗin, har sallamosu da a kayi, sannan ta ɗora da zamansu a asbiti da kuɗin da Dr ya kashe a kansu da irin kulawar da ya basu, aikuwa dai inna labarin ne ya ƙara dawo mata da komai sabo ta ci gaba da kuka ta ce "Tabbas Allah yayi i'nada sauran numfashi a duniya badan haka ba saide ka dawo kaga bana duniya, bansan lokacin da Nana ta kaini asbiti ba ban sani ba!
ESTÁS LEYENDO
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AcciónThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3