*ADDININMU*
*S REZA...,✍️*
*First Class writer's asso*
*PAGE3️⃣7️⃣*
.......Mai a ke nufi da Aure? Sarah ta tambayi Laɗifa cikin tsoron amsar da zata bata, koda bata jin hausa amma bata yarda da wannan kalmarba. Shiru ta yi ta na son gano mai Sarah ke son faɗa domin Hausar ta ta bata wani fito yanda za'agane ba. Laɗifa ta ce "Sake faɗa niji ban ganeba? Ta ce "Aure da saki mai ake nufi da su a English? Sai a lokacin ta gane mai ta ke nufi. Ta ce "Waye ya ce zai aureki? Laɗifa ta faɗa cike da matsuwa. "Pls Laɗifa let me no ina son sanin kalmarne kawai? Sai ta yi dariya sannan ta sanar mata da abunda aure ke nufi da kuma saki da English. Sarah ta yi shiru ta na tunani sai ta ce "Amm Hajiya your Mother tasan AJ ne dama? Laɗifa ta ce "Wannan shegen yaron ai Hajiya ta taɓa ɗaukarsa aiki a matsayin drebanta harma sunyi tafiya tare, ke idanma a kansa kike wannan tambayar to walhi karki yarda shi, shiɗin ɗan iskan gaskene yana bin yaran masu kuɗi yana musu ƙaryar soyayya domin ya samu kuɗine. Sarah ta kawar da kanta gefe tana jin wata faɗuwar gaba ta ce "Hajiya tayi wani auranne bayan ɓatan Uncle? Cikin jin haushe ta ce "A'a batayi aureba, amma ke meyasa kike ta wannan tabbayoyin? "Noting. Ta bata amsa tana miƙewa ta bar ɗakin.Ta daɗe tana tunani kafin ta yarda da abunda zuciyarta ta bata, kuka tayi sosai tana ta kaicin wannan halin na AJ. Tabbas tasan yana son kuɗi amma bata kawo zai iya auran babbar mace kamar Hajiya Babba saboda kuɗiba. Taso ace tanada waya da sai ta kirashi ya sanar mata da gaskiya, dukda wannan abun sai taji ta ƙara sonsa .
Hajiya babba ku wa ta na shiga ɗakinta tashiga dube-dube ta ɗauko wata tsohuwar jakarta ta buɗe ta zazzage komai dake ciki, ta shiga dubawa har ta gano takardar da take nema. Ta ɗauki wayarta ta kira Numbar da take buƙata, bayan ta sanar masa gurinda zasu haɗune ta kashe wayar tana sauke a jiyar zuciya. Palon ta fito lokacin su Muhammad basu dawoba sai ta koma ɗaki ganin laɗifa da Samuel da Usha a palon. Shigarta dakin baifi da minti biyar ba saiga Anty Titi ɗauke da shayi ta shigo ɗakin nata. Titi ta ce "Aisha wai lafiyarki kuwa? Naga gaba ɗaya kamar baƙya cikin kwanciyar hankali, kodai za'akoma asbiti ne? Ta ce "No Titi i'm Ok.
, Kawai dai nima bansan me ke damunaba. Ta ce "Ok to ga shayi kisha naga baki karyaba? "Hajiya Babba ta ce "Walhi bana jin yunwa bana sha'awar cin komai bari zuwa anjima idan anyi abinci sai naci. Titi ta ce "No kiɗan sha shayin mana ai ba abinci bane? Haka dai Hajiya Babba ta ɗan sha kaɗan sannan ta sake ce mata zata fita wani guri amma yanzu zata dawo. Ita dai Titi haka kawai Hajiya Babba take bata tausayi barinma yanda taji ance wai batayi wani auranba, ga kuma yanzu tunda mijin ta ya dawo ta ƙara shiga damuwa.*AJ POV*
ATM ɗinsa ya ɗauka ya fito ya kalli Innah da Nana ya ce "Lokacin da mukaje tonon zinaren gol ɗinnan ko? Innah ta ce "Ina jinka? Ya ce "mun samo fa sosai amma da yake ogan namu mugu ne sai ya ce wai muje zai nememu. Kumafa masana abun sunce idan zai bamu sai kowa ya mallaki gida da mota hardama na jari? Innah ta ce "To ai sai kuyi haƙuri indai rabonkune zai nemeku tunda ya ce zai nemeku ɗin. AJ ya ce "To Innah Allah yasa dai da gaske ya ke? Kuma ana bani nawa zamu bar unguwar nan zan siya mana ƙaton gida mukoma. Innah ta ce "Au wato dai bazaka daina wannan shegen son kuɗin naka bako? Abduljabaru ina guje maka ranar da kuɗi zasu jefaka a damuwa. Nana ta ce "Haba mana inna wannan ai hakƙinsane kuma ai ya sha wahala a baya kinga yanzu ai sai jin daɗi. Ta ƙarasa tana faɗawa a kan innar. Itama innar tayi dariya ta na cewa "To amma dan Allah Abduljabaru ka sake kula da mutuncin ka da kuma namu, domin a dundiya babu abu mai wahalar samu kamar mutunci yana zubewa shikenan, idan baka samu wannan kuɗin ba ka koma aikin ka na gidan bredin nann dan Allah karka sake jawo mana abun magana.
AJ ya taɓa ATM Ɗinsa dake jikin sa a zuciyarsa ya ce "Innah kenan ai yanzu saide ma ni na samo dareba ya dinga tuƙani. Afili kuma ya ce "Ok Innah, yanzuma gidan bredin zanje domin susan na dawo. Har zai fita sai kuma ya dawo ya ce "Yauwa Innah da ma akwai sauran kuɗin da ogan namu ya bani lokacin da zamu tafi, yanzu zanje na sayo waya da layi idan naga ya rage to zan zo da ɗan abunda yasamu, kar sai na kawo ki tsareni kina cewa a ina na samo kuɗi. Inna ta ce "To a dawo lafiya amma dai karka daɗe kaga dai ba lafiya gareka ba? Haka ya bar gidan cikeda jin komai yazo masa cikin sauƙi.
YOU ARE READING
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
ActionThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3