*ADDININMU*
*S REZA...✍️*
*First Class writer's asso...*
*PAGE3️⃣8️⃣*
.... Innah da Nana harma da AJ duk bakunannsu sunƙi rufuwa tsabar farin ciki da abun alherin da ya samesu, Innah ta kamo ƴan jikokinta guda biyu ta rungumosu tana saka musu albarka kamar ba gobe. Kallon kuɗin da mutum ya ajiye musu a cewar sa wai AJ ɗin ya kama wata sana'ar. Nana ta ce "Shekinan yaya yanzu babumu ba zama a wannan gidan. Ta faɗa tana jin wani sanyin daɗi na ratsa zuciyarta. Innah ta ce "Kai amma gaskiya wannan ogan naka ɗan arziƙine Allah ya saka masa da albarka. Dukkansu suka amsa da amin sannan AJ ya kwaso wannnan kuɗin ya ƙirga su naira dubu ɗari biyu ne dai-dai. Innah ta ce "To Abdauljabaru kaga dai yanda Allah yayi damu cikin lokaci ƙan-ƙani sai ka sake nutsuwa domin kaima yanzu Allah ya baka naka, kuma ba ruwanka da surutu domin kasan halin wannan zamanin namu ana jinka da ɗan abun harziƙi sai kaga ana neman halakaka. "AJ ya ce "Haba Innah a naira dubu ɗari biyun za'a wani damu dani, to walhi a wani gidan ma wannan shine kuɗin abincisu na rana ɗaya. Innah ta rafko salamulai tana tafa hannaye a lamar mamaki. Haka dai tai masa faɗa sosai kafin ta ce masa ba yanzu zasu koma gidan ba sai ya fara sana'a tukunna, AJ da yake son a gobe subar unguwar ya ce "No no no ai kawai tattarwa zamuyi gobe-gobe mubar wanga unguwa, sannan ya ce yanzuma zasu tafi da Nana domin ganin gidan. Innah ta ce "A wani unguwa gidan ya ke? "Innah ai ba a kusa muke ba can wajan gidan kwamna nefa. "Har kusa da gidan kwamna, to ai naga gurin yayi nisa, to amma Allah dai ya kyuta. Haka Nana da AJ sukayi wanka suka shirya izuwa sabon gidansu. A'jinkin takardun gidan ya duba yaga sunan unguwar da gidan harda Numbar gidan. Gidane ɗan dai-dai mai ɗauke da ɗakuna shida, sai toilet a kowani ɗaki kicin guda ɗaya palon biyu babba da ƙarami, sai filin gidan mai ɗan girma sai gurin da motoci kamar huɗu zasu faka. Gidan yayi asalin haɗuwa, da a lama dai sabon gidane domin babu komai a ciki. Haka suka dawo cike da shawƙin gidan. A ranar kuma suka ƙara fita da Nana domin siyan wasu kayan su fara kaiwa gidan batare da Innah ta saniba.Dubu ɗari biyun da Hajiya Babba ta basu ya haɗa da sauran kuɗin da Hajiya babbar ta bashi tun kafin su tafi Cemeron ya haɗa suka shiga kasuwa da sabuwar motarsa. Duk gurin da yaga wanda ya sani sai ya sauƙe glas ɗin motar ya ɗaga musu hannu, masu mamaki sunayi masu tambayar junansu nayi. Burin AJ kenan a ce yau ya mallaki gida da mota ga kuma kudaɗe masu yawa, burinsa ya ganshi a cikin mota wacce kowa ya ganta sai ya ƙara kalla. Yana cikin tafiya wata zuciyar ta ce masa "Yanzu meme burinka na gaba? Yayi shiru yana tunani sai kawai yaji wata zuciyar ta ce "Sarah ce burinka na gaba, ta maka hallacci ta soka da zuciya ɗaya. Afili ya ce "No ƙaryane ba gaskiya bane ba zai taɓa faruwaba Addininmu ba ɗayaba.
*HANYAR KATUNGU*
Salis ya kalli Sarah wacce gaba ɗaya tayi nisa a cikin tunanin da takeyi, izuwa yanzu ta haɗa komai da zai tabbatar da cewar AJ aure sukayi da Hajiya Babba. To amma yaushe kuma a ina? Batasan hawaye na mata zirya afuskartaba tana jin wani sabon son AJ ɗin na shigarta, ita koma me zaiyi tana sonsa, tana haka har saida taji Salis ya kira sunanta. "Sarah! Sarah!.
Da sauri ta goge idon ta ta amsa da "Yes Bro?
Sai ya ciro wayar da ya sayo mata ya miƙa mata ba tare da yace mata komai ba, amma yana lura da ita ta gefen ido. Hanunta tasa ta karɓa tana kallonsa, domin jin ƙarin bayani. "Wayar ki ce idan muka dawo kije kiyi welcome bak.
Taji daɗin kyutar har cikin zuciyarta, amma a fili sai ta kasa nuna masa cewar taji taɗin sai kawai bata ce komai ba ta ajiye wayar a kan cinyarta ta ci gaba da kallon waje. "Sarah inason muyi magana da ke akan saurayinki, kuma banaso kimin ƙarya? Lokaci ɗaya ta ɗaga kai ta kalleshi sai kuma ta gyara zamanta da kyu tana kallonsa yana tuƙinsa kamar ba shine yayi maganar ba. "AJ saurayinki ne, ni kuma a bokinane to saboda haka inaso na miki tambaya akansa? Ya sake yin maganar yana cigaba da tuƙinsa.
YOU ARE READING
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
ActionThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3