*ADM*
*S REZA...✍️*
*First Class writer's asso...*
*PAGE4️⃣6️⃣*
........ Zama ya yi a gurin yana faman nazarin komai dake faruwa a cikin rayuwarsu shida ƙanwar tasa, haƙiƙa suɗin marayune gaba da baya basu da kowa a cikin wannan duniyar daga shi sai ƙanwarsa sai kuma Hajara da a ka haifa masa, a i'rin wannan ranar ya ƙara jin cewar Innah bango ce majingina a cikin rayuwarsu yasan da Innah tana raye zata yi fushi amma daga baya komai zai huce domin ita ɗin bata dogon fushi da su, da yanzu a kan cenyarta zai kwantar da kansa ya sanar mata da damuwarsa. Yana zaune a gurin Nana ta fito daga wanka cikin mamaki take kallon sa, ta ƙaraso kusa dashi ta ce "Yaya har kadawo yanzu nake shirin tafiya ni da Kadija fa? Ɗago kansa yayi ya kalleta sai kukan nasa ya ƙaru yana tausayin Nana sosai domin duk shine ya jefasu a cikin wannan halin. "Haba yaya yau ai ranar farinciki ce a garemu amma kana zubar da hawayenka for noting Please yaya ka ka ka daiiii na! Itama ta ƙara sa tana kuka domin ta gano dalilin kukan nasa.Rungumota jikinsa yayi suna sakin kuka a tare. Sai da suka yi mai isarsi kafin AJ ya sanar mata da matsalar sa. Ta ce "Yanzu yaya kaman nawane zai siya maka Ragon? Ya ɗan yi murmushin ƙarfin hali ya ce "Ai ni Nana ko na dubu sha biyar na samu na saiya ai na fita kunya. Nana tayi shiri tana tunani sai ta ce "Yaya bari na shirya Allah zai kawo mana mafita da yardar sa. Aj ya ce "To Amin ya
Rabbil Alamin.Yarinya taga gata domin kuwa iyayen nata da yawa ga yayu suma ba'a barsu a baya ba. Dangin Hajiya Babba da basu san uban yarinyarba sai tambayar dangin mijin sukayi, ai kuwa matar Kawu ta ce gamu nan, matar Kawu da yaranta biyu sai mamar Kadija da wasu ƴan uwan Matar kawun sune a matsayin dangin AJ. Hajiya Babba ce da kanta ta hana kowa ya sanar dasu waye uban yarinyar. Ai kuwa Laɗifa ta fasa kwai kowa yasan waye mijin Hajiya Babba ɗin.
"Wani ɗan yarone wanda koni na girmeshi sannan ɗan matsiyata ne hasali ma yaron gidan Salis ne, daga zarar Salis yazo dashi gidannan shikenan Hajiya ta ɗauke shi suka bar ƙasarnan sukayi aure, yanzu haka yaron ko Naira baya magani, idan kuka ganshi wlhi sai kunyi tir da wannan abun kunyar. Laɗifa ta faɗa tana kuka, yayinda Hajiya Babba ta sun kuyar da kai ƙasa tana jin kunyar maganganun da Laɗifa tayi. Take ɗakin ya kaure da salati, kowa na mamaki. Wata daga ciki ta yi ƙarfin halin yin magana, domin kuwa gaba ɗaya danginnasu suna mutuƙar girmamata dalilin arziƙin ta. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Yanzu wannan wani irin abun kunyane? Shine tsabar rashin ta ido harda gaiyato dangi, mukuma muka ɗauko ƙafa mukazo wannan wani irin abun kunyane, auran abokin ɗanki harda ciki!!! An shiga uku wai Namiji da cikin haihuwa. Nan fa suka mata tatatass wanda har suka gama bata ce komai.
A na cikin wannan biki bidurin ne kuma saiga AJ ya shigo gidan riƙe da ɗan ƙaramin ragonsa, ƙafarsa ko taƙalmi babu, da ga shi sai wata baƙar riga wacce ta kawo masa har idon sau, rigar dai kamar jallabiya amma ba jallamiyar bace kawai dai yawa ta masa, sai fuskarsa da ko gyaran fuska babu, gashi yayi tumu-tumu da ƙura a da lilin kokuwar da sukeyi da ragon. A wannan lokacin gaba ɗaya labarin ya karaɗe cikin gidan domin kuwa kowa yayi tunanin Aj ɗin babbane. Duda cewar wasu sun fara tafiya amma dai gidan cike yake da matan manyan mutane da dangin Hajiya Babba ɗin harda su Mama da Momy.
Da farko Laɗufa bata ganeshiba domin kallo ɗaya zaka masa ka gane cewar yana cikin tsananin rashi da ƙarancin shekaru. Kallo ɗaya Hajiya Babba ta masa ta gane shi, ai kuwa kafin kace me ta bar gurin cike da jin kunya. Lokacin da AJ ke gabatar da Ragon sunan da yazo dashi ne kuma Laɗifa ta gane shi.
Caraf ta ce "Ƙarya kake ɗan maziyata dangin marasa mutunci dangin rashin kunya da rashin ganin ta'ido! Kai inba ma tsabar rashin kunyaba har kanada idon da aka iya kallonmu bayan abunda ka ma, to wallhi idan baka ɗauke wannan ƙazamar fuskar taka daga cikin gidannan ba sai na sa an ɓata maka rayuwa banza wawa ɗan akuya wanda baisan karamciba. Ai kuwa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba. Wannan ta ɗazun ta ƙara ce wa "Ni tinda nake ma ban taɓa ganin irin wannan rashin kunyarba sai yau. Ta faɗa tana bin AJ da wani irin kallon ƙasƙanci. A wannan lokacin ba kowa a gidan, domin su Salis sun fita zaga gari tare da su Zainab da Zara. Laɗifa ce kaɗai a gidan, shima Muhammd baya gidan. Ganin cin mutuncin yayi yawa ne yasa Nana kamo hannun yayan nata wanda ya tsaya a gurin yana kallonsu kamar gungi. Laɗifa da sauran dangi sai ci masa mutunci sukeyi. Allah ma ya rufa a siri bata gane Nana ba. Haka suka fita suka bar Ragon ba tare da Aj ya ce komai ba.
STAI LEGGENDO
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AzioneThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3