🙆♂️ *U'WATA CE SILA🙆♂️*Story by S.REZA
True life story
*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
Kaman yanda na sanar daku cewa wannan littafin ya faru da gaske ne, sai dai wasu gurare da na gyara domin ka'wata labarin, sannan labarin gajere ne bashi da tsayi, Ina son ku bini a hankalin don ji abin da ya k'unsa.
Ya Allah kasa yan da nafara libarin nann cikin farin ciki da kwarin gyiwa ya Allah kasa na gama shi lafi amin amin 🙏
*BISMILLAHI RAHAMANUN RAHIM!*
*🙆♂️_U'WATA CE SILA_🙆♂️*
*PAGE* 0️⃣1️⃣
Mom shin dama ashe duk irin yan da kike ikirarin cewa kina son kud'i a'she ba haka bane? Shin wai yan zu menene ya rage miki a duniya? Kin ce kud'i kike so kuma ga shi nan har gida suke zuwa su sameki amma kuma Mom bazaki dai na kukaba?
Cikin kuka wacce a kakira da Mom ta ce "Amera kiji tsoran Allah kitina cewa duk wannan abun da kikeyi yana kallon ki kuma"
"Shin da gaske Allah yana kallona?" Amera ta katse Mom d'in cikin sauri. Da kallon mamaki Mom tabita tace "au Ameera?"
D'an tab'a baki tayi kafin ta mik'e ta kalli Mom sannan ta ce "Mom zan fita kuma ba lallai na kwana a gidaba sabo da haka in kikaga tara tayi ban dawoba to bazan kwana a gidaba kawai ku rufe gida. Tana gama fad'in haka ta mi'ke tsaye sannan ta rataya jakar da take kusa da ita sannan ta ce "Mom wannan kud'in da kike gani wallahi sun fiye min komai yanzu domin kuwa sune dalilin komawata wannan rayuwar... Kar kibar kud'innan a'nann kwara kije ki adana su domin kuwa inde kud'ine yanzu kika fara gani, zan tara miki su kamar yan da kike so. Tana zuwa nan da magar ta ta ta fice ta bar gidan tana taunar cingon ta irin tantiran yan barikin nan.
Inalilahi wa Ina ilaihi raju'n shine abin da Mom take furtawa a zuciyarta. Kallon kud'in tayi wanda yar tata guda d'aya tilo ta ajiye mata, kud'in da take musu kallon masifa kallo kud'in takeyi kai kace bata san menene ba, kasa tab'asu tayi sai kukan zuci tayi wanda ya fito fili, tashi tayi tabar kud'in a gurin ko kallon sama bata sakeyi ba domin ji takeyi wannan kud'in tamkar tsiyace ko kuma ta ce masifa.
D'aki ta shiga ta d'auki waya ta kira uncle Bale, yana d'agawa ta fashe da kuka.
Amera tana fitowa daga gurin Mom motar ta tashiga fara sool har wani d'au kar ido takeyi, bayan mai gadi ya bud'e mata ne sannan ta tsaya saitin mai gadin ta bud'e glass din ta ce masa... Iro tin daga kan Anty Zainab tuk wanda kaka ya shigo gidan nan to in na dawo ka sanar dani, cikin sauri Iro ya ce "Angama ranki ya dad'e ai itama hajiya Zainab d'in d'azunnan tafita kuma nasan yanzu zata dawo" "Na sani ni dai ga abin da na sakaka nan" inji Amira tana jifa masa dubu biyar sannan taja motar ta tabar gidan.
Shi kuwa Iro babu abin da ya keyi sai godiya da kirari dama shi Iro haka yake irin muta nannan ne masu shegen surutu sannan kuma Iro ya kai she kara ashirin (20)yana gadi a gidan, dama kuma tashi tazo d'aya da Ameera domin kuwa tana masa ihi sani sosai sannan yana ta kaicin irin rayuwar da yarin yar tafad'a duk da dai bai san komai a kai ba amma dai yasan mahaifiyar ta ce sila.
*TIRGA BAR* Wani babban gurin Sha k'atawa ne da yake cikin garin Benue starte wanda sai kakai babban shige zaka shiga gurin domin kuwa duk wanda kagani a gurin tofa ya isa da kansa, haka ma mata sai kin kai kafin kishiga gurin.
Gurin ya had'a arna da musilmai kuma maza da mata, cikin shiga irin ta marasa sanin ciwon kansu.
Da sauri itama ta shigo gurin bayan masu gadin gurin sungama sarcihng d'in ta, wani taiburi taje ta zauna tana ajiye jakar hannun ta sannan ta ciro wayar ta tayi dailing wani number ta kara a kunne ok kawai ta ce sannan ta kashe wayar tana bin fad'in gurin da kallo wan da ita har ga Allah bata son zuwa gurin nan domin ita kwata-kwata gurin baya burgeta kwara duk abin da za suyi da mutum to suje hotel kokuma gidan sa yafi mata.
YOU ARE READING
UWATA CE SILA. is true life story. Complete
RomanceLabinrin mai cike da abun al'ajabi da tsan-tsar cin amana da soyayya mai zafi. labarin tausaya illar watsi da zuminci, sakacin iyaye ga yaransu. labarin Meeera And Nusee.