🙆♂️ *UWATA CE SILA* 🙆
*(True life story)*
*By*
*(SALIS M REZA)*
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
*Naga comment d'inku Yan, group d'in, Assadiya Hausa norvels group, har mutum d'ari uku(345comment) (1klike). Allah yasa mudace.*
*UWATA CE SILA*
*PAGE*👉 0️⃣5️⃣
................ Uncle ne ya ce "Tom Hajiya Allah ya kaimu ranar Monday d'in lafiya" Mom ta amsa masa sannan ya bar gidan cike da kewarta, haka zuciyarsa take ta ayyana masa a bubuwa da dama a game da ita.
Meera kuwa tana shiga d'akinta ta fara rusar kuka, har tayi ta gama babu wanda ya kulata domin Mom ce ta hana kowa zuwa gurin da ta ke. Haka dai ranar Meera ta koma wata iri kamar ba ita ba. Mom ta zo har d'akin na ta rarrashe ta sannan ta ce ma ta Ya kamata a ce izuwa yanzu na daina wannan kukan domin kuwa yanzu fa na gyirma, haka dai har saida ta ga na daina kukan kafun ta barni.
Yau take Litinan tun da sassafe Mom ta bar gida domin kiran gaggawa da ta samu da ga asbitin, zaune muke ni da anty Zainab akan dining table muna breakfast, kallona tayi ganin bana cin abincin, sai ta ce min "Sister lafiya kuwa kike?" Shiru na mata ban amsaba domin kuwa harga Allah ban ji ta ba, "Ameera!!!!! anty Zainab ta fad'a da ihu!! Har sai da na tsorata har ina 'ko'karin tashi na gudu, ai kuwa sai gashi na zubar da abincin da ke gabana, ban tsaya ba sai kawai na tashi da ga gurin gabad'aya na nufi kitchen..
Ina zuwa na shiga dube-dube kamar wacce ta ke neman wani abun da ta ajiye, sai can na hango abun da nazo nema ai kuwa da sauri na nufi gurin da abun ya ke, nan take na ciro na kalli abun sai kawai na runtse idanuna.
Anty Zainab kuwa ganin Ameera ta 'barar da abincin ne yasa ta me'ke, domin abun ya 'bata ma ta rai sosai, ta zauna ta girka abincin amma ta zubar, ga kuma haushin ta mata magana bata amsa ba, duk dai abun ya zamar mata biyu, so take ta je ta kamota ta ci ubanta tun da dai ba ta da hankali. Ta na shiga kitchen d'in ta zaro ido ganin abun da Ameeran ta ke 'ko'karin aikatawa.
Wuk'a ce a hannunta, ta d'aga zata cakawa kanta Allah ya sa sai ga tanan. Da sauri anty Zainab ta kwace wu'kar tana bin Ameeran da ido, "Ameera kina da hankali kuwa? Kin san mai keke shirin ai katawa kuwa Ameera?" Ameera ta ce "Mom bata sona kema haka kullum sai ku barni a gida ni d'aya gashi yanzu babu school kuma na ce muku bana son wannan Uncle d'in amma kuma dukkanku kun 'ki ku kulani shi yasa zan kashe kaina tin da dai ba sona kuke yi ba.
Duk wannan maganar da Ameera ta keyi duk cikin kukane, ita kuwa Anty Zainab sai binta take yi da ido ga kuma wu'ka a hannu sannan tana nazarin maganganun da Ameera ta ke fad'a mata, shiru dukkan su su ka yi ganin hakan ne yasa Ameera fad'awa jikin antyn tata.
Anty Zainab ta kasa magana sai binta da ido ta keyi, sannan ta na 'kara nazarin maganar da Ameeran ta ce. Janyo hannun ta tayi suka bar kichin d'in sannan anty Zainab ta fara magana kamar haka "Shin Ameera me nene yasa baki son karatu? Baki san cewa ilimi shine mutum ba? Yan zu da a ce Mom bata da ilimi zata dinga zuwa aikine? Kuma da ka a ce nima banyi ilimi ba ai ba zan dinga zuwa bautar 'kasar da na ke zuwa ba, kinga kuma saura she kara d'aya na gama kuma ina gamawa sai na fara aiki" Ta ci gaba da cewa... "ke ba ki so ki zama likita ne?" Sai a sannan na ce
"Wallahi anty Zainab in dai haka ilimi ya ke to wallahi dama ke da Mom duk ba ku yi ba", na ci gaba da magana..." bana son wannan karatun na ku please dan Allah ku dawo daga mu zauna tare kin ji?" "To dan ubanki an dai na rarrasheni ki din tin da dai ke baki da kunya ina miki misali amma kina cemin wai babu amfani" Ta na fad'in haka ta tashi ta barni a palorn a zaune.
YOU ARE READING
UWATA CE SILA. is true life story. Complete
RomanceLabinrin mai cike da abun al'ajabi da tsan-tsar cin amana da soyayya mai zafi. labarin tausaya illar watsi da zuminci, sakacin iyaye ga yaransu. labarin Meeera And Nusee.