Chptar 6

8 3 0
                                    

     *(True life story)* 

          *By* 

      *(SALIS M REZA)*



☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

  

 *YAU BANI DA LFY, TYPING D'IN BABU YAWA, INA BARAR ADDU'AR KU MASOYANA🤲🤲🤲. SAI KUMA NA SAMU LFY ZAMU CIGABA. 

 

  _Salisuadamu115@gmail.Com_ 


 *UWATA CE SILA* 

  *PAGE*👉 0️⃣ 6️⃣ *NOT*EDITING❌* 

................Dr Lurwan ya ce "Hajiya wannan wani irin sakaci ne haka? Yarin ya 'karama amma kunsa rayuwarta a cikin hatsari? "Shin wai menene kakeson sanar danine Dr? Inji Mom wanda izuwa yanzu hartafara kuka "Ameera tana d'auke da "Ya isa likita kar ka 'karasa bana son jin koma menene, Mom ta katseshi dominn kowa sam bata yarda da abun da zaice d'in ba. Tin kafin ya fa'da ma tasan 'karyane.

Zan kaita asbitin mu zan dubata da kaina basai ka sanar dani ba, in ji Mom kenan ta na me'kewa zata bar asbitin. Dr Lurwan ya ce "Tom hajiya kafin kitafi ina so ki 'kar'bi wannan takarda ki tafi da ita in yaso in kin kwadata duk abun da kika gani sai ki had'a da wannan ki gani mai zai baki. Mom ta sa hannu ta Kar'bi takarda sannan ta koma ta zau ta ce...

"Shin Dr me yake damun ta? Dr ya ce "Gaskiya Hajiya kunyi sakaci da rayuwar wannan yarinyar domin kuwa abubuwa biyu ne yanzu suke damun ta. "Please Dr sanar dani wad'anne kallan ciwone? Dr Lurwan ya ce "Nafarko olsar sanadiyar rashin cin abinci da batayi, sannan abun har ya bi jikin ta, sannan kuma hakan a rayuwar gidan ki abun tam bayane?

Na biyu kuma shine... Yaza a ce yarin ya mai shekara takwas (8) ace wai tasan wani abu wai shi damuwa? Shin me nene kuke mata da haryasa kata a damuwa? "Shuru Mom tayi tana son tina wani abu amma ta kasa, sai cen ta ce "Shikenan abun da yake damun ta? "Da sauri Dr Lurwan ya d'ago kansa yana kallon Mom jin abun da ta ce "Wai iya, wato ita a gurinta wannan ciwon shine ma zata ce wai iya.

"Tashi Mom tayi ta bar ofees d'in Dr Lurwan ranta a mugun 'bace, domin kuwa tasan cewa Ameera duk wannan abun a kan rashin son karatu ne kuma wallahi in dai a kan karatu ne to wallahi zan ta kawar da idonta daga kanta kuma sai tayi karatunnan, a haka har Mom ta 'karaso d'akin da a ka kwantar da Ameera d'in.

Kwance ta ke ana 'kara mata ruwa itakuma Anty Zainab ta na zaune kusa da ita, Mom ta ce "Ki kula da ita gobe za a baku sallama sannan kuma ki tabbatar ta na shen ma ganin da za a bata, haka zaliki abin ci, karki bari ta dinga zama da yunwa? Sannan kuma duk abun da ke faruwa ki din ga sanar dani, kuma bayan ta samu sau 'ki ki tabbatar ta cigaba da zuwa gurin uncle domin cigaba da karatun ta. 

Mom tana kaiwa nan ta fita had'e da cewa "Ni na koma gurin ai ki, kuma bazan dawo ba sai bayan wa sati uku wato ( *3 week's)*. Anty Zainab kuwa sai bin ta take da ido, da kuma to to to. Domin kuwa Mom d'in ta had'e fuskarta babu a lamar wasa a tattare da ita, har ta fita bata iya magana ba.

Anya kuwa Mom lfy ta ke? To me ya faru? Shine tam bayar da ta ke yiwa kanta. Bayan Ameera ta farka daga barcin ne ta ke tam bayar anty Zainab ina Mom? "Ta koma gurin ai ki, shine abun da anty Zainab ta ce mata, ita kuwa Ameera sai kukan ta ya 'kara 'karuwa.

Ameera tin da ta farka ta ji ciwon kan ya daina ta shin zuciyar shima ya daina, sannan gurin ma ya daina mata ciwo, to amma mai yasa Mom ta tafi bata bari mun 'kara had'uwa ba!!? Tam bayar da ta sake ma anty Zainab kenan ita ma ta ce "Wallahi ban saniba, inaga dai waini kiran gaggawanne daga cen asbitin nasu, ita dai Ameera bata yardaba domin kuwa tasan halin Mom d'in ta, idai ba Ni da

UWATA CE SILA. is true life story. CompleteDonde viven las historias. Descúbrelo ahora