Chptar 9

8 0 0
                                    

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA* 🙆‍♀️

     ( *True lef storry)* 

          By

      ( *SALIS M REZA)*




☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO..☀️*



 *UWATA CE SILA* 

          *PAGE* 👉0️⃣9️⃣

...............Kallonsu ta tsaya yi cikin mamaki ganin Nusee d'in itama harda kai mata naushi, take taji duk ba'kin cikin da tazo da shi yana tafiya dalilin wannan dramar tasu. Saida tayi gyaran murya sannan suka kula da ita. Nusee ta kwace jikinta daga ru'kon da Rakiya tamata ta nufi gurin Meera tana murmishii. Da sauri Rakiya ta sake cafko mata hannu had'i da cewa "Baki isa kibar gurinnan ba sai kin bani kud'i na ko kuma muje na mayar dake gurin da na ganki".

Nusee ta ce "Ki sakarmin hannu kafin na soma shinfid'a miki rashin mutun ci! kuma kud'ine bani da su bazan bayarba. Rakiya ta bud'e baki da niyar yin magana Meera ta ce "Anty Rakiya kiyi haguri bari na baki kud'in amma ki sakar mata hannu tukunna. Rakiya kuwa ganin Ameera tana ciro kud'in da ga Jakarta ne yasa ta sakar mata hannu tana hararar ta. 

Itama Nusee d'in hararata takeyi. Meera ta ce "Nawane kud'in"? 

Kafin Nusaiba tayi magana Rakiya ta ce... "Dubu takwas ne" dama ina bin ta dubu uku gakuma na yau dubu biyar, shine suka zama dubu takwas(8K). Nusee cikin mamaki ta kalli Rakiya sannan ta ce "Ban tan uba!! Ai kuwa baza ma a Baki ko naira ba tindade ke macuciyace. Nusee ta ja hannun Meera daniyar tafiya.

Ameera ta mi'kawa Rakiya kud'in tana cewa Ni bani da kud'i kiyi haguri da wad'an nann, kafin tayi magana, Nusee ta jata cikin d'akin ta. Suna jin irin zagin da Rakiya take bin su dashi domin kuwa dubu uku Ameera ta bata. Ameera ta ce "Wai dama haka kukeyi da uwar taki? kaman wasu sa'anye? 

"Nusee ta ce "lallai kam su uwata anji jiki, wannan matar da kike gani wallhi batada kunya, itafa ko a gaban waye zata iya kamani da dambe, ke itafa in dai zata samu abu a gurina walhi har zagin ta in dai nayi baya damun ta, kedai mubar maganar wannan matar muyi abun da yake gaban mu. Nusee ta ce "daddy ya tsoratani jiya fa.

Ameera ta ce "Nusee Mom ta sallami Uncle kuma yanzu kona kira number sa bata ta fiya. Take Nusaiba ta zaro ido waje ta na ri'ke girjinta ta ce "Ban gane ba? Nan take Ameera kwashe komai da yafaru ta sanar wa da Nusaiba, sannan ta had'a da maganar zuwa England. Nusee ta ce "Kema kin san Uncle naiman hanyan guduwa yakeyi, bayason ya tafi bada daliliba ne mu tona masa asiri, yanzu kuwa gashi ya samu dalili kinga kuwa bazai sake yarda ki ganshi ba.

Ameera ta ce "Nifa duk bama wannan ba, yanzu shikenan ya gama cin moriyata kenan? Ya tafi yabarni da ciwon zuciya!? kye Nusaiba wallahi Uncle bai ci ban zaba sai na rama duk abin da yamin kuma shida kansa zai zo har gabana ya na neman yafiyata lokacin ni kuma na gama dashi. Nusee ta ce "Ban gane ba? Me zaki masa keda baki sanshi ba? Ameera ta ce "Uncle yanada aure harda yara kuma a cikin garinnan suke, kuma harda d'a namiji a cikin yaran nasa, domin bana mantawa watarana zai je gida ya ce yaran sa bashi da lfy. Shin kina ganin mai zai biyo baya?

Nusee ta ce "thank you so much for this information, yanzu kika kawo shawara mai kyu, to amma yanzu kin san gidanne? "Ameera ta ce "mune zamu nemo karki damu komai zai warware very very soon. Nan dai suka cigaba da shirya abin da suke ganin zasu yi wa Uncle kafin Meera ta bargidan akan sai sun had'u a school.

Uncle Bala kuwa yana shiga gidan yafara surfawa Mom masifa ta in da yashiga ba tanan yake fitaba, ya ce mata karta sake zancen kaiwa Ameera wata 'kasar domin yin karatu. Haka Mom tayi shiru haryagama bata tanka masa ba har ya tafi ba tace komai ba, jira takeyi Ameera ta dawo domin kuwa tasan itace zata sanar masa.

UWATA CE SILA. is true life story. CompleteTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang