🙆♀️ *UWATA CE SILA* 🙆♀️
*(True lef storry)*
*By*
*(SALIS M REZA)*
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* ☀️
*UWATA CE SILA*
*PAGE* 👉1️⃣0️⃣
...............Mom kuwa jin kaman wayar tanayi ne yasa ta d'ago domin dubawa kafin idon ta ya kai gaban wayar saiga kira ya shigo, kallon sunan mai kiran tayi sannan ta kalli Ameera wacce har lokacin kan ta na sunkuye amma jin ringtone d'in wayar tane yasa ta d'ago ta kalli Mom d'in saitaga itama Mom d'in ita take kallo, sai ta mayar da kallonta izuwa kan wayar, Sunan Jibrin ne yake yawo a kan wayar.
Kafin Mom tayi mgn Ameera ta ce "Mom Jibrin ne class ment d'inane ya kirani ne domin yaga tin da muka gama exam ban kirashi ba. Mom ta ce "To daga yau Kar ya sake kiranki in zumunci ne angode in kuma gaisawa ne a tsaya a iya school bana son wannan zancen banzan. Saida Mom ta mata fad'a sosai sannan tace mata babu ruwanta da yin abokai maza a school domin kuwa ba shine ya kaita...
In kuwa har ta sake ta jita da namiji Wai aboki to sai ta sab'a mata. Itakuma Ameera godewa Allah takeyi da yasa Mom bataga film d'in nanba sannan ta na godewa Jibrin da yakira a wannan lokacin amma jin irin fad'an da Mom d'in takeyine yasa ran Ameera b'aci ta ce "Wai Mom ba nace miki babu komai ba ne amma kuma sai gara mai-maitawa kikeyi.
Mom ta ce "Ameera ke yarinya ce bakida wayo kuma baki da hankali karatu shine abun da ya kamata ace kina maidakai amma kuma ke bawannan ne a gaban kiba, inada buri da yawa a kanki domin ganinn na gina rayuwarki amma ke ko a jikin ki "Shin Mom mai yasa kikeson dole sai nayi karatu? ta ci gaba da cewa "Saboda kud'i ko Mom? Mom ta kalleta da kyu sannan tace "Ameera wannan 'kasar tamu in bakada kud'i to kaida kare duk d'aya kuke, kin ga kuwa mai zaisa bazan so kud'i ba?
Ameera ta kalli Mom d'in sai ta sake cewa "Dama sabo da kud'i kenan kikeso nayi karatu? To ai Mom kud'i basai nayi karatu bama zan samo miki Mom namiki Al'kawarin wallhi zan tara miki kud'in da bazaki iya gama cinyesuba har kibar duniya.
Mom tayi dariya sannan ta ce "Ameera kenan shi ilimi ko ba dan kud'i ba ana amfanar sa domin zaman wannan duniyar tamu, sabo da haka bana son nasake jin kince zaki samo min kud'i koda bakiyi karatu ba.
Ameera ta ce "To Mom ni bana son karatun nan wallhi wanda nayima ya isheni nifa Allah Mom kullum in naje school gajiya nakeyi wannan zaman class d'in duk ya ishe ne ni kawai kibarni na zauna a gida tindade na d'an yi karatun kuma sun isheni zaman wannan duniyar d'in.
Cikin jin haushin abun da Ameeran tacene Mon ta ce"Ameera Mai yasa kikeda taurin Kaine yanzu? Yan zu ban isa na ce miki kiyi abu kuma kiyi ba shin wai menene ya mayar da ke hk?
Ameera ta ce "Nifa Mom kece baki fahimtata kawai ni karatunnan ne na gaji da shi kawai ki barni har sai na huta tukunna Ameera tana maganar ne tana kallon wayarda Jibrin yaketa kira tin d'azu. 'Dakagawa tayi had'i da kara wayar a kunnenta sannan tafara magana a gaban Mom d'in.
Cikin tsaninn b'acin rai Mom ta fizge wayar daga hannun Ameera ta bugata da 'kasa sannan ta d'au keta da mari harsau biyu jikake tass tass sannan ta cigaba da cewa...
Daga yau Zan sanar miki tindade bakida hankali... Wannan gidan da kike gani da kuma wannan motocin da kikegani a gidannan duk dalilin karatun bokon da uban ki yayi ne har ya mallakesu, Nima da kikegani duk wannan fariyar da nakeyi duk ta'kamata karatun ne, saboda haka Ameera Kar kiyi karatun daga yau wannan wayar na hanaki amfani da ita sannan kuma na barki har tsawon she kara d'ayan da kikeso Allah ya Baki sa'a, Mom tana kaiwa nan da maganar ta, ta fita daga d'akin ranta a mugun'bace.
YOU ARE READING
UWATA CE SILA. is true life story. Complete
RomanceLabinrin mai cike da abun al'ajabi da tsan-tsar cin amana da soyayya mai zafi. labarin tausaya illar watsi da zuminci, sakacin iyaye ga yaransu. labarin Meeera And Nusee.