🙆♂️ *UWATA CE SILA* 🙆♂️
*By S REZA ✍️*
☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
https://youtube.com/channel/UCbdwy4ipF9kQs-yzYtv3i2A
*My you tube channel. 👆 Kubin subscribe. MASOYANA.*
*PAGE 👉1️⃣5️⃣*
..........Nana kuka takeyi tana nuna gurin da Alhaji mudi ya ke tsaye. Meera... Nusee... dakuma likitan da shima shigo warsa kenan yanzunnan, dukkanin suka kai kallon su izuwa gurin da Nana take nunawa. Alhaji mudi ne tsaye yayi mutuwar tsaye har ya saki wayar dake hannunsa, shima kallon ta ya keyi yana son tabbatar wa shin da gaske itace!? Babu ko shakka wannan itace, Alhaji mudi cikin tashin hankali da kuma rashin gaskiya da suka baiyana a fuskarsa ya juya zai bar gurin.
Nusee ta ce "Nana ki nutsu babu abun da zai sameki kiyi shiru ina son duk abun da na tambayeki tom ki bani amsa kinji? NANA kam ta gama tsorata sosai domin kuwa takasa nutsowa d'in. Saida Nusee ta rarrasheta sosai kafin ta nutsu. Nusee ta ce "Shine Abban naki? NANA cikin She-she'kar kuka ta ce "A'a ba shibane.
Nusee ta ce "To waye wancen d'in"
NANA ta sake fashewa da kuka kafin ta ce "Anty shine wallhi shine su biyu ne suka kaini wani guri kuma suka yanka min gabana tana nuna gurin da hannu. Cikin mamaki Dr ya ce "Dame suka wanka miki?
NANA ta ce "Abun fitsarinsu suka sakamin a cikin nawa kuma suka dinga yankani a gurin ina kuka amma basu daina ba, aikuwa Dr najin haka yayi waje cikin sauri. Nusee da Meera kuwa kallon junan su sukayi kafin suka kalli Nana wacce duk tabi ta furgice. Nusee ta ce "Meera ina hoton Uncle da Nana ta gani? fito dashi mutam bayeta ko shi din waye agurin ta domikuw...."Nusee tana dubawa sai taga babu kowa a cikin d'akin daga ita sai Nana.
Dr shida Meera babu in da basu dubaba amma ba Alhaji mudi babu alamar sa, sannan ga motarsa nann, ai kuwa take a ka hana fita da shiga a cikin hospital d'in, a ka kira duk ma aikatan cikin hospital d'in aka ce kowa ya shiga dubashi, ana cikin hakane yansanda da Dr ya kirasu sukazo.
Tafiya takeyi wanda Rabin hankalin ta basa tare da ita, Tabbas itace sila itace silar komai kuma koma meye tasan alhakin sune dole ta je ta nemi yafiyar su tin yanzu sannan ta sanar dasu halin da suke ciki na rashin sanin inda Ameera ta ke. Awani anguwar talakawa ta tsaya tana mai bin gidan da wani irin kallo, kallon da ke 'dauke da nadama, raboton da wannan gidan zatayi shekara a shirin koma tafi.
Gidan nanan a yanda ta sanshi saima 'kara lalacewa da yayi, in ta tuna irin wula'kancin da ta dinga musu a baya sai taji bazata iya shiga gidan ba...
Tana tsaye a gurinne wani ya fito daga gidan yana tafiya yana zabbga masifa kai da ganin sa kaga masifaffe. Tsayawa yayi yana kallon ta itama kallon sa takeyi. Babu shekka ya ganeta Aisha ce matar d'an uwan sa wacce ta rabasu da shi tin yana raye bayan ya mutu kuma ta yi masu iyaka da abun da ya shafeta harda d'iyar cikin ta.
Babu shekka Mom ta gane shi wannan shine abokin rikicin ta shine 'kanin mijin ta wannan masifaffannan amma ta manta sunan sa. D'auke idon sa yayi daga nata sannan ya na 'ko'karin barin gurin. Cikin tsoro da fargaba Mom ta ce "Salamu'a laikum "W slm kawai ya ce yana mai cigaba da tafiyarsa.
Mom ta ce "Dan Allah ka saurareni gurin ku nazu Dan Allah. Cikin masifa baba 'karami ya ce *Wallhi Aisha tin muna cikin ruwan sanyi ki bar 'kofar gidannan in ba hakaba zansa yara su koreki . Duk da kuwa yayi mamakin ganinta a 'kofar gidan nasu. Mom ta ce "Dan Allah ka saurareni Wallhi ha'kuri nazo baku nayi na dama "Baba 'karami ya ce "Mukuma mai kika mana da zaki zo kibamu haguri? Ai mu babu abin da kika mana saboda haka ja motarki ki bar gidannan tin yanzu.
VOCÊ ESTÁ LENDO
UWATA CE SILA. is true life story. Complete
RomanceLabinrin mai cike da abun al'ajabi da tsan-tsar cin amana da soyayya mai zafi. labarin tausaya illar watsi da zuminci, sakacin iyaye ga yaransu. labarin Meeera And Nusee.