Chptar 19

4 0 0
                                    


          *By S REZA*




☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

 *SADAU KARWA A GAREKI👉ANTY FATIMA* 


       *PAGE* 👉1️⃣9️⃣

..................... *BABBAN GIDA* Cike yake da dangi takota ina wasuma har sun manta da wasu tsabar rashin d'aukar zumin cin da muhimmanci. Babu shakka wannan family d'in ba'karamin family ba ne amma rashin zumunci yasa wasu sun manta da wasu, kowa kallon juna sukayi ganinn cewa yau dai an had'u. Hajjo tsohuwa mai ran'karfe ce ta fara magana, dukda cewa Hajjo ta tsoufa amma in ka ganta bazakace itace ta hafi mazan gidan ba....Hajjo ta ce "Ina Lawand'in ya ke? Yanzu lawan a ce kananann a raye amma babu ruwanka da iyayenka haba lawan mai muka maka haka. MLM Sani ne ya katse hajjo da cewa "Haba Hajjo kibari muyi abun da ya kawomu tukun in mun gama sai kiyi Masa fad'an ai zaifi. 

Cikin masifa Hajjo ta ce "In kuma banyi shirun bafa?... Ace mutum yayi watsi da 'yan uwan sa saboda duyi kace wai nayi shiru, to Koda a ce ma haifiyar sa bata raye ai yanada 'kanne. Hakade Hajjo ta wanke Daddy da fad'a wato Alhaji lawan saida tayi har da gaji kafin tayi shiru.

Alhaji lawan kuwa tin lokacin da Hajjo ta fara fad'a yake tinanin abubuwa da yawa, Babu shkka d'an uwan sa ya rasu kuma yanada mata d'aya harda ciki tin a wancen lokacin to shin ina take!!! Itace tambayar da yakeson yiwa Hajjo amma ya kasa, sai jin muryar mlm Sani yayi yana magana kamar haka...

Tom muna sake godewa Allah da ya sa muka gane gaskiya tun kafin lokaci ya 'kuremana, babu shekka munyi kuskure wajan watsi da zumuncin bayan Allah subuhanahu wata'ala shi da kansa ya ce muyu zumunci Sannan kuma shugaban mu Annabi Muhammad sallalahu a laihi wa sallama ya u'mar cemu da mu ri'ke zumunci, amma kuma mu munyi watsi da namu, to amma yanzu lokaci bai 'kureba ba sai mu 'kyara. Duka d'akin kowa ya amsa da cewa hakane kuma in sha Allah komai yazo 'karshe in Sha Allah. 

Nann take kowa ya shiga gabatar da kansa agurin wanda ya manta da shi, saida kowa yayi ya gama sannan mlm Uba shima ya ce "Tom Daddy wannan itace matar marigayi Salisu wacce ya rasu ya bari da ciki a jikin ta kuma ta aihu lafiya yanzu haka itama yarin yar bata tare da ita an nemeta an rasa. Lokaci d'aya Daddy da Mom suka d'ago kai suka kalli juna...Saida gaban kowa acikin su ya buga, barinma Daddy da ya had'a ido da ita. Babu shkka tin da ya shigo yake binta da kallo yasan wannan fuskar to amma a ina!!? Sai yanzu ya tabbatar da itace domin kuwa ya tina fuskar ta.

'Ban garan Mom kuwa tin lokacin da ya shigo ta ganeshi kaaan cewar ita bata manta da fuskar saba. Nann dai a ka tambayi Mom komai game da Ameera ta bada amsa. Sai a Lokacin Daddy ya yi magana ya ce "Yanzu ina ita yarinyar? Mom ta ce "Kaman yanda kaji mlm Sani ya fad'a d'azu cewa ba'a San in da takeba to hakane. Yace "To a gari yaya har kikayi sakaci 'yarki ta bar gida baki sani ba? 

Mon ta ce "Wallhi duk laifinane nice silar komai da ya faru kokuma na ce da yake faruwa, take Mom ta kwashe komai abun da yafaru da Ameera ta sanar musu tin daga lokacin da Mijin ta ya rasu har zuwa rashin ganinn Ameera da a kayi. Kasan cewar dama ta sanar wa da su baba 'karami, sauran dangin ne kawai basu jiba da kuma Daddy. 

Ai kuwa lokacin da ta kammala basu labarin saida kowa yayi mata fad'a a kan abun da tayi d'in. Kadija ce ta ce "Innalillahi wa inna ilahi raju'n!! Yanzude kice kin 'bata rayuwar Ameera ta 'karasa maganar tana kuka tana cewa wallahi Aisha kin cucemu yanzu ita kad'ai Yaya Salisu ya bari a duniya amma kin rabata da kowa nata yanzu ga irin halin da tashiga.

MLM Sani ya ce "Ameera ba 'bata tayiba ni a nawa tinanin kenan fa mu barta har lokacin da ta ga dama zata dawo. Baba 'karami ma ya ce "Nima dai gani nakeyi kaman ta gudu ta bar gida ne saboda zafin abunda mahaifiyar tata ta mata, kuma dama gashi ta ce lokacin da Ameera ta gudu fishi ta keyi da ita. Hakade 'yan d'akin kowa yayi a'manna da maganar da baba 'karami yayi. Kadija ta ce "To ni yanzu inason kibani hoton ta koda zan ganta a ABUJA ba sai na sha wa halaba. Haka kuwa a kayi Mom ta turawa kadija hoton Ameera. Lokacin da kadija ta ga hoton Ameera wani irin sone taji ya shigeta na yarinyar abun ka da had'uwar jini sai take ganin kamar ma tana kama da ita.

UWATA CE SILA. is true life story. CompleteTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang