🙆♂️ *UWATA CE SILA🙆♂️*
( *By S REZA)*
*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION....*
*KASHI NA ASHIRIN DA BIYU*
*PAGE 👉2️⃣2️⃣*
............. Kallonta ya keyi yana son tabbatar wa shin da gaske ita d'in ce ko dai gizo take masa, lumshe idon sa yayi a hankali kafin ya bud'e, ai kuwa ya sake sau'ke su a kanta. Ita kuwa Meera tana had'a ido da shi saida gabanta ya fad'i ganinn wani irin 'kwarjini da yama, take ta d'auke idon ta daga nasa tana jin wani migun tsanar sa, glass d'in idonta ta mayar sannan ta mai da hankalin ta izuwa wajan al'kali. Shima Kabir kawar da kansa yayi daga kallonta izuwa gurin da mahaifin nasa ke tsaye. Ita kuwa Nusee sai bin sa takeyi da kallo tamkar ta rungumshi takeji amma kaahiii!!! Badama.
Mom suna gaba-gaba yayin da su Nusee kuwa suke baya, tin da Mom ta shigo cikin kotun takejin gaban ta na fad'uwa hakanne yasa ta kasa sakewa sai karanta innalillahi wa inna ilahi raju'n takeyi a zuciyarta.
Bayan mai gabatar wa ya gama gabatar wanne, Lauyan su Alhaji mudi ya tashi cikin kwarin gyiwa ya ce "ya mai girma mai shari'a ina son kotu ta bani dama domin yiwa Nana lawan wasu tambayoyi?
Al'kali ya ce "Kotu ta baka dama. Ya ce "Na gode had'i da d'an sunkuyawa alamar girmamawa kamar yanda lauyoyin sukeyi.
Ya je har gurin da Nana ta ke sannan ya ce "Nana lawan ko zaki iya tabbatar wa da kotu suwaye suka shirya miki wannan 'karyar domin ganin cewa ke yarinya ce hukunci bazai hau kankiba? Nana cikin kuka ta ce 'Ba kowa ni ban sanme kake cewaba nidai tsoro na keji. Barista Sani ya ce "To in dai kina jin tsoro ki sanar min da komai sai nasa a sakeki kin ga babu wanda zai miki komai? Kafin Nana tayi wata magana barista Muhureez tashi ya ce
"Up jok shon my load bai kamata a ce yana sakawa yarin ya 'kama zance abakiba.
Al'kali ya ce "Lauyan mai kare wanda a ke 'kara a kiyaye. "Na gode.
Barista Sani ya ce "To Nana yanzu dai kin ce Baki San komai ba ko? Nana ta 'kyad'a masa kai a lamar eh. Sannan yayi dariya ya ce "Ya mai girma mai shari'a iya wannan hujjar ta isa tayi nuni da cewa Nana lawan wasu mutanane sukayi amfani da abun da a ka mata domin ganin an 'bata sunann bayin Allah, sabo da haka mukeso wannan kotu mai adalci da ta kori wannan 'kararr sannan a sa Nana ta sanar mata da suwaye suka sakata wannan aikin. Barista Sani yana kaiwa nann ya sun kuya alamar girmamawa ga alkalin kafin ya harari gurin da Barista Muhureez ke zaune.
Al'kali yayi yan rubuce-rubucen sa kafin ya ce "ko Lauyan wanda ke 'kara yanada abun cewa? Barista Sani kuwa cikin ransa yana jin cewa ai yanzu babu wata hanya da ta ragewa barista Muhureez da zai biyu domin kuwa yasan yayi wening wannan kess d'in. Sunyi shari'ar sau hud'u da shi yayinda Barista Muhureez yayi nasar cin guda uku shikuwa Barista Sani ya ci d'aya, hakanne yasa suke ta'kun sa'ka a tsakanin su duk da ba gari d'aya sukeba.
Barista Muhureez ya ce "Inada abun cewa ya mai girma mai shari'a. Yaje gurin da su Alhaji mudi suke ya ce "Alhaji Bashir shekaran jiya misalin qarfe uku na yamma yaron ka yazo police station gurin ka ko zaka iya sanar wa da kotu wani abu kuka tattauna?
Dai-dai lokacin da Alhaji Bashir ya ce "Ni ni ai ba jiya bane yazo ba ba kuma bai zoba ma. Ya kasa ma yin maga sai in-i'na yakeyi alamar dai ya rikecw. Dai-dai lokacin ita kuma Mom ta d'ago da niyar kallon gurin da maiyin wannan alamar rashin gaskiyar ya ke. Aikuwa caraff Mom ta had'a ido dashi amma shi bai gan taba.
Cikin tsananin tashin hnkali Mom har ma ta manta da cewa a kotu take ta mi'ke tsaye ta ce "professor Kamal!! Yayin da shikuwa Alhaji Bashir yana jin wannan sunan sai ya kai kallon sa izuwa gurin da Mom take. Aikuwa caraff suka had'a ido lokaci d'aya ya ganeta take yaji wani sabon salon tashin hankalin ya sake riskarsa, aikuwa cikin rikicewa ya fara 'ko'karin ja baya amma ina babu dama.
YOU ARE READING
UWATA CE SILA. is true life story. Complete
RomanceLabinrin mai cike da abun al'ajabi da tsan-tsar cin amana da soyayya mai zafi. labarin tausaya illar watsi da zuminci, sakacin iyaye ga yaransu. labarin Meeera And Nusee.