Chptar 23

4 1 0
                                    

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA* 🙆‍♂️

      *(By S REZA* )



☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

 *KASHI NA ASHIRIN DA UKU*

       *PAGE* 👉2️⃣3️⃣

.............. *AL'KALI* ya buga gudumar sa take kotun kowa yayi tsit, kana ya ce "Ko lauyan Wanda a ke 'kara yana magana? Barista Sani ya me'ke tsaye sannan ya ce "Bani da abun cewa ya mai shari'a. Al'kali ya kalli Barista Muhureez ya ce "Kotu tana sauraron ka. Barista Muhureez cikin tsananin farinci da jin dad'in ganinn ya samu nasara ya je gurin Alhaji Bashir ya ce "Shin wannan record d'in da kowa ya saurara shin dagas ke muryar kane? Alhaji Bashir yayi shiru yana tinanin yaufa asirin sa ya gama tonuwa bashida wata hanya da ta rage masa. Ya ce "Eh muryata ce. Barista Muhureez ya ce "Kenan da gaske ne kune kuka yiwa Nana fyad'e?

Alhaji mudi ya harari Alhaji Bashir yana masa a lama da ido a kan kar ya fad'a, shi kuwa Alhaji Bashir ya kalli gurin da Nana take tsaye sannan ya kalli gurin da Mom take kana ya kai kallon sa izuwa gurin da Kabir da Nusee da Meera suka, take yaji hawaye suna bin kumatun sa. Ya ce "Eh mune muka mata.

Take kotu ta sake kacamewa da surutai kowa na tofa albarkacin bakinsa, shikuwa Daddy wani irin dad'in yaji ganinn cewar yaude gaskiya ta baiyana, ya kai kallon sa izuwa gurin da Mom take, ai kuwa yaga ta had'e fuskarta tamkar taga wanda ya kashe mata miji. Kabir kuwa duk abin da Meera ta ke cewa acikin kunnuwansa amma tsananin tashin hnkali da yake ciki ya kasa maga, sai ma yanzu da yaji Daddy d'in ya ce sune suka yi fyad'e sai yaji lokaci d'aya ma ya tsani Daddy d'in nasa.

Barista Muhureez ya ce "Ko zaka iya sanar wa da kotu gaskiyar lamarin da kuma kai da waye? Cikin kuka Alhaji Bashir ya ce "Eh zan iya. Nann take Uncle ya fara basu labarin tin daga lokacin da sukaje gurin BOKA har zuwa lokacin da BOKAN ya basu tabbacin samo maniyin karuwa wacce bazata huce shekara 16 zuwa ashirin 20 ba, da kuma jaririya da yarin ya yar shekara goma 10 zuwa sha biyu ba.

Zuwa lokacin da suka kai masa komai zuwa kwanciyar da sukayi da ita, zuwa mutuwar da tayi, zuwa d'auko ta da sukayi a motarsu zuwa jefarta da sukayi, zuwa burin su da ya cika, zuwa had'uwa da yarinyar a asbiti zuwa kawosu kotu da a kayi zuwa yanzu zuwa zuwa zuwa.

Kotu tayi shiru domin kuwa kowa yana tsoran karyayi magana shima hukunci ya shafeshi. Barista Muhureez ya kalli Alhaji mudi ya ce "Alhaji mudi ko kada abun cewa gameda labarin da abokinka ya bayar? Alhaji mudi yayi shiru ya sun kuyar da kai yana mai jin wata irinyar kunya wacce bai ta'ba jin taba, Barista Muhureez ya ce "Kotu kai take sauraro Alhaji mudi.

Alhaji mudi ya ce "Gaskiyane mune mukayi amma wallhi ni ban "Ya isa haka bama son jin komai tin dade har ka fad'i gaskiya da bakin ka.

Barista Muhureez ya ce "Ya Mai girma mai shari'a duba da yanda masu laifi suka wahalar da shari'a sannan suka kashe rai na jinjiri da kuma 'bata rayuwar yarinya 'karama, Muna so wannan kotu mai a dalci da ta yankewa wad'annan bayin Allah hukunci dai-dai da abun da suka aikata. 

Kotu tayi tsit Al'kali ya shiga rubuce-rubuce har zuwa wani lokaci kafin ya d'ago kai ya kalli ilahiran jama'ar da ke cikin kotun kafin ya bud'e baki ya ce "Abisa kwararan hujjoji da aka bayar da kuma amsa laifi daga gurin masu laifi kotu tayi duba da niyar kashe rai da masu laifi sukayi har guda uku amma Allah bai yiba saboda haka, s tsarin hukunci na addinin muslinci ya ce duk wanda ya kashe to a kashe shi. Dawannan koyarwa ta addinin muslinci wannan kotu mai a dalci ta yankewa Alhaji mudi da Alhaji Bashir hukuncin kisa ta hanyar rataya, da kuma tararr kud'i kimanin miliyon bibiyu kowannansu izuwa gurin iyayan jinjirar da a ka kashe, sannan kotu da bada umarni a nemo iyayan jinjirar acin kwana biyu.

UWATA CE SILA. is true life story. CompleteDove le storie prendono vita. Scoprilo ora