Chptar 24

6 1 0
                                    

🙆 *UWATA CE SILA*🙆‍♂️

*(BY S REZA)*



☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*




*KASHI NA ASHIRIN DA HUD'U*

*PAGE* 👉2️⃣4️⃣

............... *Daddy* ya ce "Amin in sha Allah shima Sulaiman d'in zai sota tin dade yar uwar sace, Mom dai bata saike cewa komaiba har suka bar cikin garin Nasarawa. Kabir kuwa bayan an kammala shari'a ne ya fito daga cikin kotun ya nufi gida cikin yanayin damuwa, yana tafe yana tinanin rayuwa, yanzu yasan shikenan kuma Daddy da Najib sun gama 'bata musu suna a idon jama'ar gari. Ai kuwa kaman yasani tin kafin ya shiga gida 'yan unguwar su suka fara nunashi, tin basa magana har suka fara zagin Daddy da masu irin halin su, haka dai Kabir ya isa gida bai ko kallesu ba. Yana shiga gidan kuwa ya taranr da wani sabon tashin hankalin da yafi wanda ya ke ciki.

Hotel d'in da suka kama suka je, bayan sun shigane cikin mamaki S M ya ce "Ban gane ba shin mai kukeyi a nann? Nusee ta ce "D'akin da muka kama kenann. Meera ta kalli Nusee ta ce "Kin ga manta da wannan zancen muyi abun da ya kawomu, domin kuwa ita Meera gaba d'aya ma ta rikice.

Meera ta ce "SM kace Nana 'kanwar ka ce ko?

SM ya ce "Eh 'Kanwa ta ce baban mu d'aya da ita.

Ta sake cewa "Kana nufin dai Alhaji lawan Shine mahaifin Nana kuma mahaifin ka?

SM ya ce "Dama kin san shi ne?

Cikin sauri Meera ta ce "A'a nima a Kotu naji Sunan sa. Ya ce "okay, sannan ya sake tam bayar su ..

SM ya ce "Ameera mai kuka zoyi a Nasarawa tsawan wannan lokacin kun sa ana ta neman ku, har gidan kufa na je amma a ka cemin wai kin b'ata wai an saceki, please dan Allah ku dawo gida kubar wannan yawon ban zan.

Nusee ta ce "Tom SM in Sha Allah zamu koma amma dan Allah menene tsakanin Abbanku da kuma wannan matar da mukaga sun shiga mota d'azu a Kotu? (wato tana nufin Mom) Kafin SM yayi magana cikin sauri Meera ta ce "Ina ruwanki da su please dan Allah ba wannan ba, yanzu SM gida zaka tafi daga nann ko?. Tayi wannan tambayar ne domin kawar da maganar da Nusee d'in tayi.

Ita kuwa Nusee mamaki tayi ganinn ai wannan abun ne ya kamata a ce sun fara tam baya kafin komai amma ita ko a jikin ta, amma bari dai taga Ameera d'in mai take nufin domin kuwa tasan ta da 'karami tinani yanzu sai ta had'a wata sabuwar masifar bayan wacce suke ciki. SM ya ce "Eh amma yanzu nafasa tare da ku zamu tafi saboda haka kawai ku shirya sai mu tafi. Cikin sauri Meera ta ce "Eh zamu tafi tare amma fa ba yauba sai de gobe Saboda bamu gama aikin da ya kawomu ba. Itama Nusee ta ce "Nidai ko goben ma saide ku tafi ku barni.

SM ya ce "Okay Allah ya kaimu. Suka amsa da amin sannan ya tashi ya bar d'akin yana mai jin wani farin ciki yau Meera ta saki jiki da shi. ( *NI KUWA S REZA NA CE "KAIDE KABI MEERA A HAM KALI🥰)*

Bayan ya fita Nusee cikin sun saninn wani irin abu Meera take 'kullawane ta ce "Wai ke Meera anya kinada hankali kuwa? Bazaki duba abu. "Ya isa Mera ta katseta cikin sauri.

Meera ta ce "Shin ke a naki d'an 'karamin tinanin mai kika hango gameda maganar da SM yayi? Nusee cikin tsananin jin haushin 'kawar tata ta ce "To me zan hango bayan baki bari ya sanar damu abun da ya kamata mu sani ba, kin san Allah Meera wallhi jikina ya na bani wani abun zai faru da mu.

Cikin tsananin jin haushi Itama Meera ta ce "To in ke kin manta da abun da Alhaji lawan ya mana Bari na tina miki. Kin manta shine kad'ay ya ci amanar mu, bayan ya kwanta da ni kema ya baki magani a rashin sani ya kwanta da ke, kuma kin manta da cewa munce muna son d'au kar fansa? To bari kiji ni dai na samo hanya guda d'aya wacce zata min maganin matsala guda biyu.

UWATA CE SILA. is true life story. CompleteTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang