*UWATA CE SILA* 🙆♂️
( *BY S REZA)*
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀️
*KASHI NA ASHIRIN DA SHIDA*
*PAGE* 👉2️⃣6️⃣
............ Dasauri Nusee ta kawar da kanta daga kallon sa tanajin kamar taje gareshi ta ce masa tana sonsa zata aureshi bazata iya rayuwa ba tare da shiba. Kamar daga sama taji muryar sa yana cewa "To mungode Allah yasaka miki da Allah kairi kicewa kwar taki muna mai bata ha'kuri akan abun da aka mata, munsan duk wannan abun hak'kinta ne yake bibiyar mu amma in har ta yafemana munsan zamu samu sau'ki in sha Allah.
Nusee ta mi'ke daga zaunan da take ta matsa kusa da Mommy sannan ta ce "ai ita ta dad'e da yafewa dama itace 'karfin zuwana gidannan akan naje na nemi yafiyarku in kun yarda sai tazo itama ta naimi ya fiyarku. Mommy ta ce "Allah sarki ai babu komai wallhi mun yafe mata itama tazo sai ta yafe mana.
Sun d'an jima suna hira da mommy kafin ta ce "To Mommy bari naje ana jirana domin yau zamu tafi gida dama mu yan Benue makurdi ne, Ta d'ora da cewa zamu biyo tananan da ita sai muyi sallama. Mommy ta ce "Tom sai kunzo Allah ya kiyaye hanya.
Nusee ta kalli gurin da Kabir ke zaune ta ce "Yaya Kabir rakani bakin get mana? Kafin yayi magana Mommy ta ce "Tashi ka rakata har bakin titi ta samu abun hawa kaji? Haka suka jero suna tafiya abun sha'awa kamar wasu masoya, tafiya sukeyi har suka bar gidan babu wanda yayi magana. Ita kuwa Nusee sai takejin ta tamkar ba'a wannan duniyar takeba. Wani 'bangaran na zuciyar ta na sanar da ita cewar wannan dama ce ta samu kar tayi wasa da ita ta fito fili ta sanar dashi abun da ke ranta.
"Me kukazo yi garin mu naji kin ce ku ba 'yan Nasarawa bane? Tamkar daga sama taji tambayar, hakane yasa ta rikece domin kuwa bata shiryawa tambayar tasa ba. "Amm amm dama dama kawai munnnn... Sai kuma tayi shiru, kafin tayi magana sukaji wasu yan zaman majalisa suna cewa...
"Ai wallhi anyi abun kunya yarin ya 'karama amma suka danneta har su biyu saboda tsinannune marasa mutunci. Na kusa dashi ya kar'ba da cewa "Ai ni Walhi naji dad'in wannan hukuncin da a ka musu saboda masu irin halin su shegu marasa mutunci. Wanima ya ce "Wai an ratayesu d'in ne kodai za'a musu halin girma afitar dasu kaman yanda a kasaba a wannan 'kasar tamu? Wanima ya cigaba da cewa "Ai wallahi mutu'karr suka saki mutanann idona idonsu saina hallakasu saide nima a kasheni.
Haka dai suka cigaba da hirarr tasu, wacce Kabir da Nusee d'in duk sunaji. Nusee ce ta kalli fuskar sa domin ganinn yazaiyi aikuwa taga yana kuka lokaci d'aya taji tausayin sa, sai kawai itama ta fara hawaye ganin shima hawayen ya keyi. Ta ce "Please ka daina kuka wannan itace taku gaddarrar kowa da irin tasa kaide kayi haguri wataran sai labari. Kabir ya ce "Dole nayi kuka domin kuwa Daddy ya mana tabon da bazai ta'ba goguwaba, yasa kowa ya gujemu hatta yarinyar da nakeso kuma mukayi Al'kawarin aurema iyayenta sunsa ta gujeni...
Dik in da na shiga nunani a keyi ana cewa, yayana yayiwa qanwar mu fyad'e ta mutu, babana kuma sun yiwa yarin ya qarama fyad'e had'i da kashe jinjira 'karama saboda duniya. To in banyi kukaba mai zanyi?
Lokaci d'aya kukan Nusee ya tsaya jin cewar budurwar sa ta gujeshi, sai kawai taji wani abu yazo mata mai kama da dariya amma ta danne, take wani kwarin gyiwa yazo mata ta ce "Kabir kana sona zaka iya aurena?.
' *BAN GARAN MEERA* Ganin har yanzu Nusee bata dawo bane yasa Meera fara tinanin ko dai an samu matsala ne, ta kasa sukuni ganin kamar hankalinta baya tare dashi ne yasa SM ya tam baye ta.
Take ta sanar masa da komai akan Nusee taje gurin Kabir ne. Cikin mamaki SM ya ce "Gaskiya tashi mubi bayanta kar muje ko matsala a ka samu, ai kuwa take Meera ta had'a musu duk kayan su domin kuwa bazasu biyo ta nann ba sai de suhuce gida ta can.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
UWATA CE SILA. is true life story. Complete
RomantizmLabinrin mai cike da abun al'ajabi da tsan-tsar cin amana da soyayya mai zafi. labarin tausaya illar watsi da zuminci, sakacin iyaye ga yaransu. labarin Meeera And Nusee.