Chptar 30

1 1 0
                                    

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA*🙆‍♂️

       *By S REZA*


☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

https://youtube.com/channel/UCbdwy4ipF9kQs-yzYtv3i2A

 *Ina kuke masoyan littatafen S REZA? 🖕 kumana subscribe a YouTube channel d'in mu domin samun dad'an littatafai* 🖕🖕🖕🖕.


 *KASHI NA TALATIN*

       *PAGE* 👉3️⃣0️⃣

..........kallon wayar tayi taga dagaske ya katse kiran kawai sai ta fashe da wani irin kuka mai ta'ba zuciya, du'kawa tayi a gurin ta dinga kuka tana ta'ba cikinta har Rakiya ta ji. "Lafiya kikazo kikacika mana gida da kuka kamar anyi mutuwa? Cewar Rakiya tana shigowa d'akin. Ai ko kallonta batayiba saima cigaba da tayi da kukanta tamkar bata jitaba.

Rakiya kuwa dama cike take da haushin ta ganin tinda tadawo ko magana ma ta'ki yarda suyi kuma tanason ko wani abu ta bata amma sai wani shareta takeyi Rakiya. Cikin tsananin b'acin rai ta ce "Ke dan uwarki badake nake mgn bane? Meye ya samu cikin naki? Aikuwa in dai fankan da ke cikin d'akin ya amsa mata to itama Nusaiba ta amsa. Ganin hakane yasa Rakiya ta kamo hannuta tana mai juyowa da ita ta ce...

"Nusaiba wallhi kud'i nakeso ki d'an aramin zan yi... "Kafin ta 'karasa Nusaiba ta tureta had'i da cewa "Wallhi in baki fita a harkataba zan miki abun da bazaki ta'ba mantawa ba. Ai kuwa dama Rakiya abun da take nema kenann sai kawai ta fara masifa had'i da zage-zage. "Yo dama ina wani mutunci a gurin yarinyar da tabar gidan iyayenta tabi duniya, ai dama in bakimin ba ai baki cika cikakkiyar yar duniya ba, babu mamaki ma cikine kika kwaso daga can gurin yawon tazubar d'in muna fika.

Haka Rakiya ta cigaba da zaginta tamkar an aikota, ita kuwa Nusee tana jinta amma masifar da take cike yafi ta tsaya tana biye mata, amma har cikin zuciyar ta tana jin zafin maganganun da take fad'a a kanta, ganinn hakane yasa ta hau gado ta rufe kanta da bargo har tagaji da zagin kafin ta bar d'akin tana mai cigaba da zagin harda kiran mahai fiyar Nusaiba din ta zaga.

 *ABBAN NUSAIBA* Yana zuwa bayan an masa sallama da ita tafito, cikin tsananin b'acin rai ya ce "Tom gashi nann burinki ya ciki tin dade ke baki damu da itaba, yanzu wa gari ya waya? Cikin rashin fahimta ta ce "ban ganeba me kake nufine?

Ya ce "Nusaiba na d'auke da ciki, Saboda haka saikisan ya zakiyi da ita, yana kaiwa nann ya shiga motarsa yabar gidan cikin 'bacin rai. Mommy ta tsaya tana mai-maita maganar ciki!². Sannan ta ce ai kuwa wannan karan saide duk Abu da zai faru ya faru amma sai ta kawo yarta gidannan koda mijin ta bayaso to saide in rabuwa zai da ita surabu. Haka ta shiga gidan tana mamaki yaushe Nusaiba d'in tadawo kuma dama yawon bin maza taje!!! Ai kuwa dole yanzu ta rungumi yarinyarta domin kuwa dik laifin tane amma in Allah ya yarda zata gyara komai, wata zuciyar kuma ta ce bayan komai ya b'aci mai kuma zaki gyara!?.

 *AMEERA* Kuka takeyi sosai domin kuwa Nusaiba ta kirata ta sanar mata da cewa Kabir ya 'ki d'aga mata waya, yanzu in takirama bata shiga tasan blocked d'inta yayi. Ita kuma gashi yanzu babu damar fita Mom ta ce bazata sake fita ko inaba har sai ta gama istubura'i tukun, harta wayar ta an kwace wannan ma wayar Mom ne da tadameta da kuka shine ta ce zata kirata sau d'ay she kenann kuma ta yarda. Yanzu ita damuwar ta wani hali take ciki. Tana mutu'karr tausayawa Nusaiba domin kuwa yanzu abar tausayi ce, amm in sha Allah zata san yadda zatayi.

 *KABIR* Shi duk a tinanisa Nusaiba ba karuwa bace domin shi yayi tinanin Ameer ce kawai karuwa ganinn yanda take da saukin Kai, amma wai ace harda ciki!! Inana lillahi wainana ilaihi raju'n. Ace 'yarda nakeson zan aurane da ciki!! kai ina gaskiya bazai iyaba, hakanne yasa yayi blokend number d'in ta harda number Ameera domin kar ta kira ta number, duk da irin sonda ya kemata amma gaskiya yana da kishi sosai, bazai iyaba.

UWATA CE SILA. is true life story. CompleteWhere stories live. Discover now