Chptar 31

1 0 0
                                    

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA*🙆‍♂️

       *By S REZA*


☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

https://youtube.com/channel/UCbdwy4ipF9kQs-yzYtv3i2A

 *Please kumin subscribe d'in YouTube channel d'in mu domin samun dad'an littatafai🖕* 

 *KASHI NA TALATIN DA D'AYA*

       *PAGE* 👉3️⃣1️⃣

..........kallon fuskar ta yakeyi yaga ita ko a jikinta saima cigaba da tayi da ninke kayan da takeyi, ganinn yayi shiru ne yasa ta ce "Umhum ci gaba mana ina sauraron ka? Kabir kuwa tsabar mamaki ya hanashi magana sai binta yayi da kallo kamar idanunsa zasu zubo. Mommy ta ce "To bari kaji in sanar maka... "Ni dama nasan yarinyar karuwa ce amma ada, banda yanzu, lokacin da tazo gidannan ta bani labarin rayuwarsu tsaffff, kuma wannan gidan da kaji sun koma to sun tubane daga abun da sukayi, nima na mata wa'a zi sosai akan taje tanemi ya fiyar iyayen ta ta kuma samu miji tayi aure kuma ta ce in sha Allah zatayi, to a haka muka rabu. Bayann nann kuma ina wannan yaron da sukazo har sukace shine zai auri d'aya yarinyar? Kabir ya ce...

"Ok Sulaiman kenann ko? "Mommy Ta ce "Eh shi, to yazo gidanan bayan wata d'aya da suka huce ya sanar min da komai akan cikin datayi, abun da yasa kaga ban maka maganaba kawai ina son naga gudun ruwan kane, saboda haka yanzu kabari sai ta aihu sai kawai aje ayi magana domin kuwa kaima nasan kana son ta sosai. Ai da wani irin sauri Kabir ya run gumeta kammar zai shige cikinta ya ce "nagode Mommy Allah ya saka da alkairi, kafin ya bar gidan cike da jin dad'i.

Bayan ya fitane Mommy ta ce "Kabir kenann!! Ai wanda ya soka alokacin da kowa ya gujeka to tabbas soyayyar gaskiya yakemaka, kaima kuma karka gujeshi aduk irin halin da zai shiga, kai Allah dai ya sau 'keta lfy. Shi kuwa Kabir kaman yanda Mommy ta ce ya bari har sai ta aihu kafin ya kirata kuma haka akaiyi, har yanzu bai kirataba amma kullum yana lissafin lokacin da zata sihu. Har ga Allah shima yana sonta domin yanzu yana jin koda aihuwa goma tayi to tabbas zai iya auran ta.

 *BAYAN WATA UKU*. *HAJIYA FATIMA* Kallon kayan da Sulaiman ya had'a a matsayin kayan lefen karuwa takeyi, cikin tsawa ta ce "To wallhi wannan yarinyar bata da darajar da za'a kaimata wannan kayan saboda haka tin kafin ranka ya 'baci ka rage komai yanzu kuma a gabana. Sulaiman yayi shiru yana kallon ta kafin ya ce "Hajiya please dan Allah kinsafa wan..."Nasan ubanka? Na ce nasan ubanka? Banza solo'biyo wanda ya rako maza duniya, in banda tsabar rashin hankali ace karuwa d'ana zai aura!! Sai kawai ta fashe da kuka ganinn haka yasa Sulaiman ya fita, a zuciyaraa kuma yana cewa ai tindade kin ha'kura ayi auran ai shikenan.

Saida tasa aka rage komai na cikin akwatin kafin masu kaiwa suka d'auka. Ana jibi d'aurin aure ne Ameera ta samu Sulaiman akan maganar Nusaiba. Nann take ya sanar mata da yanda sukayi da Mommy lokacin da ya je Nasarawa ai kuwa taji dad'i ta ce "To yanzu kaima baka gano gidan da suka koma bako? 

"Eh Nima nayi iya nemana amma ban sani ba.

Ameera ta ce "Nikuma gashi Mommy ta bani phone d'ina amma ta goge komai na ciki harda numbers d'in da suke ciki... Kuma nasan yanzu koma tana inane to lokacin aihuwar ta yayi. Haka dai suka cigaba da hira duk akan Yaya zasu samo gidan su Nusaiba.

 *NUSAIBA* Yau tun safe da ta tashi take jin jikin ta ya mata nauyi, ga ciyon da mararr ta keyi, tin bata damuwa har abun yafi 'karfin juriyar ta, kawai sai tafara ihu. Dama Maman tasan ta shiga lokacin aihuwar ta hakanne yasa take an kare da ita, ko aiki bata sakata ko nann da cen, saide ta ci ta sha takuma kwanta, dukda haka kuwa baisa ta futa daga damuwar da take ciki ba. Tin maman nata bata jin kukan har ta juyo ihun nata, ai kuwa da gudu ta shigo d'akin tana mai kiran sunann ta...

UWATA CE SILA. is true life story. CompleteWo Geschichten leben. Entdecke jetzt