*BILLIONAIRE BILKISU.. 💅🏻*
( _Hamshaƙiya_)
_@Mrsbalarabe_
*Fatima Batula*_1&2_
_SADAUKARWA; ga my SA'AD my lovely boy Allah y rayamin kai rayuwa mai albarka ya saka ka zamto mahadacin al'qur'ani mai girma_
_TSOKACI; zaku ga canjin labari da wancan wanda na fara yi da wannan,wani ikon Allah ne ina zaune naji wannan lbrn ya fado cikin raina, sai na yanke na maida mishi sunan wancan,ku yarda da ni wannan lbrn zai nishadantar da ku sannan zai wa'azantar, na kasa tsaida kaina ga suburbudo muku shi cikin gaggawa, ina fatan zaku bi ni sannu a hankali duk da labarin ba mai tsawo ba ne, amma tafiyar mai cike da kasaita ce._
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*Da sunan Allah mai rahama mai jin kai dukkan yabo da godiya su tabbata ga ubangijin Al'arshe tsira da aminci su kara tabbata ga shugaban mu manzon mu (S A W) . Allah ka dau rayuwar mu da soyayyar ma'aikinka, barka da ranar Juma'a . Amin.*
ABUJA.
MADDALA.
"Ina son *SA'AD* Maryam ke kinsan ina sonshi, soyayya mai tsantsar karfi amma.. amma....",shiru tayi tare da zare hannuwanta daga cikin na Maryam ɗin ta goge yan hawayen da suka fito mata.
"Amma me *Bilkisu* ? wani irin tunani ne kike da shi haka? yau fa aka kawo kayan saka ranar ku da shi amma naga kina kuka , kuma kuka bawai na farinciki ba" .
Tashi tsaye BILKISUn tayi ta juyawa Maryam din ba, kalle jikinta ta shiga yi tana juyawa gaba da baya, "Kalle ni Maryam ki kalle ni, sam ban dace da Saad ba kalli irin zubin da Allah yayi min, taya ma SAAD zai riƙe ni taya zai iya bani kulawa bashi da komai ke kin sani SAAD bai da komai mai yaci balle yaban kina ganin wayar duba dari da hamsin bai iya siyamin, taya kenan zai iya ciki min burina na zama HAMSHAƘIYA, taya? bayan ke kinsan banda wani buri da ya wuce wannan, gaskiya Saad bai dace da rayuwata ba....."cikin dan kukan ta na ƙunci ta kai karshen zancen.Ganin Maryam din bata ce da ita komai ba ne yasa ta daura da fadin," Anya kuwa zuciyata ba so take da cuce ni ba, anya kuwa bazan iya nadamar auren Saad ba, dan ban dace da shi ba ni babbar yarinyar ce sai n kare akan shi, shi kenan duk wannan kyawun, diri zati, kwarjini, izzza, kasaita, sun tafi a karkashin shi taya zai iya kulawa da ko lafiya ta ma balle kyau n d izzata anya kuwa....
"To ki barshi mana", Maryam din tai saurin tare da dan faɗan ta.
Juyowa tayi wanda ni sai yanzun ma na samu ikon kallon ta, Dukkan yabo su tabbata ga ubangijin wannan halittar na fada a zuci d baki, lallai wannan halittar karshe ce gurin kyau duk abunda ta fada to duk ta fi haka ma kyau izza kasaita kwarjini duk sun wuce tunanin mutum sai ga wanda yayi arba da ita zai fahimta.
Dawowa tayi ta zauna kan gadon da Maryam din take wanda gadon yake karami ne.
"Ina son Sa'ad shi ma samunshi Burina na ne, kuma mafarki na SAAD mafarki na ne, shi ne burina ina sonshi my Final choice my favorite my Destiny idan zan yi aure a wannan duniyar to shi ne irin mijin da ya cancanci samu na, shi ne mijin da ya dace da ni shi ne mijin da zan kalla na kira shi da miji na wanda zai amsa sunan mijina to Sa'ad ne, Saad yayi y hadu komai da ake son namiji a duniya yana da shi ba tsaran maza ba ne shi maza zasu rufe bakin amsa sunan su n maza agaban shi, SAAD Burina ne".
Cike da chan mamakin BILKISU Maryam tai ajiyar zuciya sannan ta ce, "To meye matsalar".
Dan rausana kai tayi, "Baki sani ba ne Sa'ad baida kudi taya zan rayu da shi, dan ina sonshi hakan ba yana nufin zan rayu da soyayya ba ne kawai".