NURUL-AAYN

11 0 0
                                    

[11/10, 11:34 AM] Ayush💞: *NURUL-AAYN*
_[Hasken idaniya ta]_

_Story&written by_
*_AYUSH💞_*

_Elegant Online Writers_

*_FREE-BOOK_*

_I dedicated this page to Our leader *#Nimcyluv* Allah ya baki lafiya, Allah ya tashi kafaɗunki yasa kaffara ne. Pls sisters duk wanda yaga page ɗin nan kuyi mata addu'a da wanda suka santa da wanda basu santa ba. Allah ya ba kowa lafiya. Ameen_

_Page 3&4_

*_Thirty minutes later_*

_____Ƙarar cokula ne kawai yake tashi a dinning ɗin, can Ayush ta miƙe tare da ɗaukar wayar ta, sannan ta dube su tace "Sai da safen ku".

Duk suka amsa mata da Allah ya tashe mu lafiya,daga nan tayi gaba.

Daddy ne ya dubi Sadeek yace mai. "Sadeek idan ka ƙarasa ina son ganin ka".

Sadeek yace "to Daddy". Daga nan Daddy ya nufi stairs domin yayi shiri bacci.

Khalil yace " Mommy yau Autar ki rigima take ji da ita".

Mommy tace "Ita ta sani, da kanta zata sauko daga wannan fushin nata". 

Sadeek yace "A'a Mommy Autar a dai bata haƙuri".

Mommy tace "to shike nan".

*_Ten(10) minutes later_*

Zaune yake a parlour yana jan carbi sai ga Sadeek ya shigo bakin shi ɗauke da sallama, Daddy ya amsa mai sannan ya bashi umarnin zama.

Bayan ya zauna yace "Daddy barka da hutawa".

Daddy yace "Yauwa Sadeek, ya hanya? Ya kuma mutanen gidan? ".

Sadeek yace "Alhamdulillah, suna gaishe ku".

Daddy yace "Masha Allah, abinda yasa nace kazo nan shine munyi waya da Daddyn ka shine yake sanar dani abinda zai kawo ka nan, sannan yayi min magana akan kana son ƴar uwarka(Ayush) toh nidai abinda zance a nan Allah ya taimka yasa Alkhairi sannan ka nemi yardar ta shike nan,in Allah ya kaimu gobe da safe hada ni za'aje ma'aikatar taka  domin naga aikin".

Sadeek yace "Toh shike nan Daddy nagode Allah ya ƙara girma".

Daddy ya amsa daga nan sukayi sallama.

Sadeek yana fita bai zarce ko ina ba sai wajen Khalil inda ya same shi a  compound, yana ƙarasa yace mai "Kai Yaro Daddy yace na nemi yardar Noor bai san mun daɗe da wuce wannan wajen ba, ya ƙarasa yana dariya".

Khalil yace " Eh lallai dole kace min yaro tinda ka fara maganar Aure, toh bari kaji daga yau Yaya zaka riƙa kira na dashi if not.... ".

Sadeek yace " da ka ƙarasa mana ai na girmeka fa kawai dai zan riƙa maka biyayya saboda Matsayin Noor a wajena".

Khalil yace "kaji dashi ni wuce mu shiga ciki dan yau bacci nake ji".

Sadeek yace "ohk amma kafin nan ya za'ayi naga Noor? "

Khalil yace "muje wajen Ummi". Daga nan suka shiga parlour bakunan su ɗauke da sallama, Ummi ce zaune tana kallo ta amsa musu sannan suka ƙarasa wajenta suka zauna.

Khalil ne yace "Ummi kin leƙa Ayush kuwa?".

Ummi tace "eh na leƙata har tayi bacci".

Daga jin haka Sadeek yaji bai ji daɗi ba saboda shi a target ɗin shi idan yazo gidan nan soyayya zasu sha sosai kafin ya gama abinda ya kawo shi ya tafi, amma yanzu sam bai ji daɗi ba.

Ummi ce ta katse mai zancen zucin daya ke tace "Sadeek ya jikin Daddyn ka dafatan bai sake kwanciya ba?".

Sadeek yace "eh Ummi yaji sauƙi sosai kullum yana fita office ma kuma sai dare yake dawowa".

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 10, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

[11/10, 11:34 AM] Ayush💞: *NURUL-AAYN* _[Hasken idaniya ta]_    _Story&written Where stories live. Discover now