Chapter 1

124 8 0
                                    

*WAKE ƊAYA💍*
MomIslam

🆓Page1

Ɗanɗano

A gigice ta durƙusa a gaban, Inna Meramu. tana cewa "dan Allah Inna kiyi haƙuri ki taimakamin karki jefani cikin wannan ruwan wlhi zan iya mutuwa"
Hawaye nabin kumatunta kamar an buɗe famfo.

Cikin rashin tausayi da sanin darajar ran ɗan adam, Inna Meramu ta dagata sama ta waiga taga babu mai kallonta ta wurga Hanan cikin tafkeken kogi.

Inna meramu ta juya a guje tana darara ihun neman agaji, tana isowa ƙofar gida ta zube a gaban malam Junaidu tace "rabona da ganin Hanan tun safe nayi yawo har nagaji, yanzu nan daka ganni daga Kadage nake"
Malam Junaidu ya miƙe tsaye tare da rafka salati yace "nima zama bai ganni ba dole ina shiga gari nemanta"
Sai kuma ya tsaya ya kalli Inna meramu yace "ammafa sai naji kamar Halliru mai shago yace "yaganta da tiran tallar shinkafa?"

Inna meramu ta fara ƙirƙiro kalaman kare kanta kafin tace "uhm malam me kake nufi?"
Bai tsaya jin abinda zatace ba ya bazama gari neman Hanan.

Kowa yagani a hanya sai ya tambayesa yaga Hanan, suce basu ganta ba.

Yayi tafiyar datakai ta d'ari biyar amma bai ko ga d'ankwalin Hanan ɗin ba, zama yayi gindin wata bishiya ya yakice zufar data karyo masa kafin yace "ina yarinyar nan ta shiga?, a iya sanina bata saba yin nisa da gida ba, Allah ka nunamin ta inda zan ganta"

Ya miƙe yaci gaba da tafiya a gajiye.
Yamma liss ya dawo gida ya samu Inna meramu tana alwalar magriba, shima butar ya ɗauka tare da nufar bayi, yana shiga aka kwashe shi aka watsar gefe kamar kayan wanki, ya rafka salati yana cewa "nashiga uku meramu kinajin halin da nake ciki?"
Tana daga bakin murhu tayo kansa da gudu har tana kujewa a jikin bango tace "malam koda ka taka musu ƴaƴan ne?"
Ta fita waje da gudu tana ihun neman agaji,
Cikin sa'a Halliru mai shago ya jiyo kururuwarta ya taho da gudu yana cewa "Inna meramu meke faruwa?"
Tasa hannu akai ta rusa ihu tace "malam ne ya faɗi a banɗaki ka taimaka ka fito dashi"
Halliru ya shiga gidan da sallama ya shiga banɗaki yaga malam a yashe sai wani irin numfarfashi yake,
Cikin azama ya fito dashi, Inna meramu ta shimfiɗa tabarma ta fara yi masa fifita,
"Akira malam mai karatu?"
Halliru ya faɗa yana kallon Inna meramu,
"A'a barshi muga abinda Allah zeyi dan wlhi sisi bana magani bare ince ka kira shi"
Halliru yace "inhar befi ƙarfina ba zan taimaka"
Inna meramu tace "to tunda ka kafe kamar ƙanin ubanka"
Halliru baice mata komai ba ya fice yana jajanta rashin mutunci na matarnan,
Cikin natsuwa ya isa gurin malam mai karatu yace "malam Junaidu ne ya faɗi a banɗaki shine nazo dan Allah ka taimaka masa"
Jinjina kai malam mai karatu yayi kafin yace "bana son shiga gidan nan saboda niƙanmu baya laushi da Meramu"
Halliru ya haɗe hannayensa biyu kamar zeyi kuka yace "dan Allah kai taimaka masa malam ka duba halin da yake ciki"
Malam mai karatu yace " to Allah yasa mu dace, muje yanzu na dawo daga sallahar magriba zan shiga gida"
Suna shigowa suka samu tanata adu'a tana tofa masa, malam mai karatu yace "kull karki sake ta6ashi bare tofa masa gubar bakinki"
Cikin rashin fahimta da dama ba shiri take yi dashi ɗin ba tace "ban gane ba?, ko dole sai kaine idan kayi masa magani zai warke babu wanda Allah yaba sa ni?"
Malam ya girgiza kai tare da fara karantowa malam Junaidu karatun Alkur'ani mai girma, yana yi yana tofa masa, tashi ɗaya ya fara ɗaga hannu amma babu bakin magana,zatayi magana malam mai karatu ya dakatar da ita cikin fushi yace "idan na kaiki Shari'a wlhi bazamu dawo tare ba acan zan barki?"
Inna meramu ta miƙe tsaye tana nuna malam da hannu tace "ƙarya kakeyi wallahi ko an gaya maka niɗin lafiya ce?"
Cikin rashin fahimta Halliru yace "malam wai meke faruwa ne?"
Malam yace "kambun baka ne da ita, sarai tasani inada yaƙinin wlhi akwai kalmar data furta masa muguwa"
Inna meramu ta miƙe rai a 6ace tana share hawayen da suka fara sintiri a fuskarta tace "wlhi yau sai na kaika gidan mai gari"
Malam mai karatu yace "ki kaini gaba da nan ma"
Ta fice.
Wasu irin yaruka malam Junaidu yakeyi wanda babu wanda yasan abinda yake faɗa dagashi sai Allah.

WAKE ƊAYAWhere stories live. Discover now