Page__1.
*FATHIYYA*
Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR**YAN TAGWAYE.....*✍️
*PAID BOOK....*#400GA MASU BUKATAR ƳAN BIYU DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA DAYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
A tura shaidar biya zuwa ga
+44 7894 142004
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
________________________________
Tun tashin ta sallar asuba bata samu ta koma ba kasancewar daga ita har maigidan masu fitar sassafe ne, tana gama azkar ɗinta ta wuce kitchen don haɗa musu abinda zasu yi breakfast, duk da cewa tana da wadatattun ma'aikatan dasu ke taya ta aiki amma tafi son ta ciyar da maigidan ta daga abinda ta sarrafa da hannunta.Yam fritters ta soya wato doya mai kwai sai tayi soup din kayan cikin rago, black tea ta dafa haɗe da kayan kamshi da ɗan flavour na strawberry da ta zuba a ciki.
Sai da ta tabbatar komai ya kammala ta shirya a kan table kafin ta wuce zuwa bedroom don ta shirya, har wannan lokacin maigidan ta Farouq na naɗe a kan gado yana bacci.
Girgiza kai tayi ta wuce Bathroom tana murmushi "shi dai sweetheart baya gajiya da bacci" ta faɗi hakan cikin zuciyarta, fitowar ta daga banɗakin yayi daidai da tashin shi daga bacci.
"Good morning sweetheart, gara kayi ƙoƙari ka tashi ka shirya kada fa muyi latti" ta faɗa tana ƙarasawa gaban dressing mirror tana mai tsane jiƙaƙƙen gashin kanta da ta wanke da ɗan karamin towel.
"Mtss... Wallahi baccin nan bai isheni ba" ya ce yana ƙara ƙudundunewa cikin duvet.
Har ta gama shiryawa cikin atampar Julius Holland dinkin A shaped doguwar riga yana kwance bai motsa ba, kan gadon ta hawo haɗe da cewa, "Sweetheart ka tashi haka, ALLAH za muyi latti idan baka tashi ka shirya ba". Ta ƙare zancen tare da kai hannunta ta shafo fuskarshi, fuskarta ɗauke da murmushi, riƙe hannun yayi haɗe da kissing ɗin 'yan yatsunta kafin ya janyota gaba ɗaya cikin bargon ita ma ya rungume, kissing ɗinta ya shiga yi ta ko ina, kafin ta samu da kyar ya tashi ya shiga wankan ita kuma ta hau tattare ɗakin ta gyara. Bayan fitowar shi ma da taimakon ta ya shirya cikin Navy blue suit ɗin kamfanin dolce and gabana, shirt ɗin ciki kuma kalar sky blue.
Sosai yayi mata kyau a ido har ta kasa kau da kai daga kallon shi har sai da ya hura mata iska a fuska, kawar da kanta tayi tana murmushi cikin jin kunya don ba yau suka fara hakan ba dama.
Duk da yadda mutane ke yawan faɗin kyawun ta, a karan kanta kuma ta san ita ɗin mai kyau ce amma har kullum ta kalli Farouq sai ta raina kyaun da take da shi domin kuwa shi ɗin kyakkyawa ne irin kyaun da idan yana yawa zata iya cewa har yayi mishi yawa, saboda tun daga saman shi har kasan shi Allah ya wadata shi da kyakkyawar ƙira, babu ta inda aka rage halittar shi komai na shi kamar shi ya zabawa kan shi.
Yana gaba tana biye da shi a baya hannunta ɗauke da hand bag ɗin ta da kuma jakar laptop ɗin shi sai mayafin da zata yafa da ta saƙala a kafaɗarta.
Saukowarsu kenan suka ji ƙarar door bell, a tare suka kai duban su ga bakin ƙofar suna tunanin wane baƙi suka yi haka yanzu da sassafe, ajiye kayan hannunta tayi akan kujera jin ana cigaba da danna ƙararrawar babu ƙaƙautawa, ta warware mayafin ta yafa tunda bata san wa zata tarar a bakin ƙofar ba ta tafi don ganin waye.
STAI LEGGENDO
FATHIYYA
Storie d'amoreFathiyya! Labari akan wasu abokai kuma aminai guda biyu wato FAROUQ da MAHMOUD, inda ƙaddara tayi wa rayuwarsu ƙullin goro akan mace ɗaya mai suna FATHIYYA. FAROUQ shine masoyinta kuma mijinta da take jin cewa mutuwa ce kaɗai zata iya rabasu, kwats...