BABI NA UKU

83 9 0
                                    

Page__3.

*FATHIYYA*

Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*

________________________________
    Mahmoud kuwa ya jima a wajen zaune har cook ɗin dake haɗa abinci a gidan ya fito tare da russunawa a gaban shi yace "Sir! Breakfast is ready".

Mahmoud daya buɗe idanuwanshi a hankali tare da sauke ajiyar zuciya yana tashi zaune daidai ya ce "ok". Sannan ya miƙe ya koma sama, yana shiga ya tadda wayarshi na haske, ko daya duba kiran babban aminin shi ne da basa rabuwa wato Farouq kusan missed calls biyar, yana ƙoƙarin kiranshi message ɗinshi ya shigo

    _"We need to talk abokina, a ina zamu haɗu?"_

     _"In my Office, let's say by three o'clock"_

Ya tura mishi amsa tare da ajiye wayar gefen gadon, yana ƙoƙarin miƙewa kiran Zinnira dake gab da shiga kamfanin nasu ya shigo wayarshi tana son faɗa mishi cewa kada ya manta ya fito da wuri saboda ana buƙatarshi shima a wajen meeting ɗin, yana ganin ita ce ya yi tsaki tare da kashe wayarshi gaba ɗaya ya mayar ya ajiye, toilet ya shiga yayi wanka ya shirya cikin wani haɗaɗɗen voile kalar Royal blue ɗinkin half jumper, ya taje kanannaɗaɗiyar sumar kanshi baƙa siɗik irinta fulanin asali haɗe da sajenshi dake ƙara fito da cikar kyawun fuskar shi da kwarjinin shi na cikakken namijin da ya amsa sunan shi ya shafa mai sai kyalli suke yi, hula ya ɗauko kalar royal blue itama ya ɗora akai yana kallon kanshi ta madubi haɗe da murza ƴan madaidaitan laɓɓansa da suke pink colour tamkar ya shafa jambaki sannan ya ɗauki turarukan savage(dior) da kuma eros(versace) ya fesa tare da ɗaura silver agogonshi na pierre cardin a tsintsiyar hannunshi, baƙaƙen eye glasses ɗinshi da suka kasance na ƙara ƙarfin gani ya saka, abun tubarkallah masha ALLAH don Mahmoud kam badai kyau ba, gwargwado shima ALLAH ya kyautata surarshi don mutane har kasa banbancewa suke yi tsakanin shi da amininshi Farouq wanda yafi kyau, amma yadda mata ke matowa a kanshi yasa wasu ke ganin ya ɗara Farouq kyau nesa ba kusa ba, duk da kuwa rashin fara'ar da yake fama da ita in ba can baka rasa ba, shima ɗin hakan tafi faruwa idan yana tare da abokanan kasuwancinshi ko kuma mai girma Zinnira.

A hankali yake saukowa daga upstairs ɗin har ya ƙaraso ƙasa ya nufi wajen dining, kaɗan ya tsakuri breakfast ɗin ya mike don sam ba tayi mishi daɗi a baki, cike da girmamawa ya shiga amsa gaisuwar masu aikin dake harabar gidan da yake faman ratsowa ta wajensu yana wucewa, wasu bayin ruwa suke yiwa fulawoyi, wasu kuma share-share, wasu wankin motoci wasu kuma masu yin cefane ne da sauran masu kulawa da aikace-aikacen gidan.

Sai daya tambayi kowannen su  idan yana da wata matsala suka amsa mishi da babu haɗe da yi mishi fatan ALLAH ya kiyaye sannan ya shiga motarshi da kanshi ya tayar ya bar gidan, kai tsaye office ɗin shi ya nufa dake ɓangaren kamfanin da yake kula dashi ba tare daya damu da zuwa wajen meeting ɗin da za a gudanar a can ɗayan kamfanin ba wato head office ɗin su yana jiran isowar abokinshi Farouq don yau ya sha alwashin sai ya baƙanta ran Zinnira kamar yadda ta baƙanta mishi shi yasa ba zai tafi wajen taron ba, duk da ya san cewa zuwan nashi a wajen nada matukar muhimmanci sosai don shi suka fi sani ba ita ba...

*****.    *****.     *****.   
   A ɓangaren Faruq kuwa sai da suka yi sallar azahar ya samu ya lallaɓata ta sha tea rabin mug ya ɓallo paracetamol ya bata ta sha sai faman narkewa take yi tana zuba mishi shagwaba, kukan da ta yini tana yi ne ya saukar mata da zazzaɓi, kwanciya ya sata tayi, cikin lokaci ƙalilan kuwa bacci ya ɗauketa yana zaune yana riritata kamar wata jaririya.

Sai da ya lura baccin nata yayi nisa sosai kafin ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka a gurguje ya fito ya shirya yana kallon ɗan karamin agogon dake ajiye akan bedside drawer, bai da buri yanzu irin ya ganshi wajen Mahmoud daya ce mishi su haɗu a Office ɗinshi, ya tabbata bazai rasa samun mafita ba a wurin shi don shi a daidai wannan lokacin ya rasa abun yi gaba ɗaya.

FATHIYYADove le storie prendono vita. Scoprilo ora