Page__7.
*FATHIYYA*
Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*________________________________
A ɓangaren fathiyya kuwa tana zaune a parlourn ƙasa taci kwalliya cikin straight skirt kalar ja da riga body hug baƙa, bata jima da dawowa daga wajen aiki ba, a gurguje ta ɗora masu girki tayi wanka don kar ya dawo ya isketa ba a yadda take so ba duk da tarin gajiyar dake tattare da ita, sosai kayan suka yi mata kyau don sun bi jikinta sun kwanta sun bayyana duk wani lungu da saƙo na jikinta daya fitar da kyakkyawar surarta ta ɗiya mace, kallo ɗaya zaka yi mata kasan tun daga tsarin matar gidan har gidan sun dace da zama a muhallin, gaba ɗaya gidan sai tashin daddaɗan ƙamshin turaren fatar jikinta da wanda ta turare gidan dashi yake yi, haɗuwar ƙamshin da sanyin a.c ba ƙaramin daɗi yayi ba don ya bada wani kalar sihirtaccen ƙamshi da yanayi mai daɗi dake cike da natsuwa da kuma sanyaya zuciya.Duk da ƙarar tv dake a kunne hakan bai hanata tattara hankalin ta gaba ɗaya ta maida a waje ba tana dakon dawowar masoyin nata kuma mijinta, ƙarar tsayuwar motar mai gidan nata data ji ya saka ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwa haɗe da buɗe wa tana jiran tsammanin shigowar shi, wucewar wasu mintoci da a ƙalla zasu iya kaiwa takwas zuwa goma bai shigo ba ya saka ta miƙewa tsaye ta nufi ƙofa da zummar isa wajenshi ta gani ko lafiya?
Alamun taɓa ƙofar data ji ne yasa ta ɗan ja da baya tana bayyanar da murmushi akan fuskarta tare da buɗe hannuwa, murmushin ya saki duk da akwai ƴar damuwa dasƙare a zuciyarshi tare da hugging nata shima lokacin daya shigo, dama abinda take jira kenan ta shige jikinshi sosai haɗe da cewa "welcome home darling, tun ɗazu nake zaman jiranka, gaba ɗaya har hankalina ya soma tashi da naji ka daɗe da shigowa gidan baka ƙaraso ciki ba".
Yadda tayi maganar a shagwaɓe ya saka shi ɗan sakin murmushin shima ba wai don yana jin hakan ba haɗe da cewa "ayya, am sorry sweetheart, abu na ɗan tsaya yi cikin motar shi yasa ban shigo da wuri ba, muje ki bani abinci naci don yau na kwaso yunwa sosai".
Breaking hug ɗin tayi ta karɓi kayan dake hannun shi da suka haɗa da wayar shi da kuma i-pad ɗin shi ta ajiye akan centre table sannan suka wuce wajen dining table, sai da ta janyo mishi kujera ya zauna kafin ta ɗauki Plate ta saka mishi abincin ta tsiyaya mishi haɗaɗɗen zobo drink ɗin dake tashin kamshin mint leaves da strawberry a cikin tumbler ta ajiye mishi a gaban shi kafin taja kujerar dake gefen shi ta zauna ita ma tana son karantar yanayin da zuciyarshi ke ciki da fuskarshi ke ƙoƙarin bayyanarwa, ganin haka ya saka shi saukar da kanshi ƙasa sosai ya cigaba da cin abincinshi ba tare daya bari ta fahimci komai ba, duk da bata buƙatar cin abincin don babu yunwa a tare da ita hakan bai hanata ɗaukar plate ba ta ɗebi abincin daidai cikinta itama ta fara ci. A hankali suke cin abincin tana ɗan jan shi da hira kaɗan kaɗan amma sai taga kamar hankalinshi kwata-kwata baya kanta, saɓanin sauran ranaku da yake bata dukkannin attention ɗin shi, ta lura tsaf dashi sai tafaɗi magana sau biyu sau uku kafin ya bata amsa, shima ɗin da eh ko kuma a'a, daga haka kuma baya ƙara cewa komai, wanda hakan ya tabbatar mata da akwai abinda ke damun shi don ba haka ya saba yi mata ba.
Kafin ta fito wannan tunanin da take sai kuma ga mamakinta taga ya ajiye spoon ɗin ba tare dako rabin abincin yaci ba ya ture plate ɗin gefe, kofin zoɓon data tsiyaya mishi taga ya mika hannu ya ɗauka ya shanye tas sannan ya ajiye cup ɗin tare da miƙewa tsaye ya bar wurin.
Da kallo kawai ta bi shi har ya haye sama, to meke faruwa dashi ne? Ko zancen auren da Mami keso yayi ne ke damunshi? Wani irin zafi da kishi taji sun rufe mata zuciya ta ture abincin itama don sai taji duk ya fita daga ranta.
Tashi tayi ta tattare wurin ta maida kayan kitchen ta wanke ta maida komai wajen zamanshi sannan ta ɗebi wayoyin shi da tab ɗin data ajiye akan centre table ta bishi saman.
YOU ARE READING
FATHIYYA
RomanceFathiyya! Labari akan wasu abokai kuma aminai guda biyu wato FAROUQ da MAHMOUD, inda ƙaddara tayi wa rayuwarsu ƙullin goro akan mace ɗaya mai suna FATHIYYA. FAROUQ shine masoyinta kuma mijinta da take jin cewa mutuwa ce kaɗai zata iya rabasu, kwats...