Garin kano unguwar lamido cresent GRA.
Gidane babba daga gate din kana shugowa zaka san gida ne na masu arziki, atsakiyar gidan akwai babbar bishiyar guava wadda tayi girma sosai tayi ma compound din rumfa, yara ne gudu suke wasa, duka maza da alamu yan uwane amma kuma kammanin su duk daban ne, biyu acikin yaran farare ne alhalin sauran biyun kuma bakake ne, kyawawa ne yaran bulbul don akalla bazasu wuce shekara bakwai zuwa tara ba kana ganinsu zakasan hutu ya zauna ajikinsu suna sanye da riga da wando na jeans agefe kuwa wani yaro ne zaune gefen wajen famfon wanke motoci yana kallon su da alamu yana son ya shiga cikinsu amma sun hanashi yarone kyakyawa black beauty shima bazai wuce 10yrs ba yana da manyan idanuwa very innocent sannan yana da hancin kamar biro fuskarshi sak irin na Fulani saidai akasin fatar jikinshi chocolate color, daya daga cikin yaranne ya kalli inda yaron yake sannan yace ''kai salim zoka buga ball din", aikuwa kamar jira yake ya taso da gudunshi yana zuwa dab da wanda ya kirashi ji kake bamm anbugo ball din saitin goshin sa nan take ya kwala kara jin zafi agigice ya durkushe kasa, sukuwa yaran me zasu banda dariya, jin kukanshi ya karade duka gidan yasa wata farar mata ta fito daga main entrance din parlour aikuwa tana ganin yaran atsaitsaye suna dariya yasa ta karaso wajensu kallonsu tayi daya bayan daya, fararen yaran ne su biyu suka matso wajenta suna mummy mummy, kallonsu tayi sannan tace Khalil,khamis menene haka banace kuyi wasanku ku kadaiba, wanda aka kira da khamis ne ya kalleta yace ''mummy muna wasane saisu jabir sukazo sukace zasuyi munce masu bazamuyi dasu ba shine jalal yace wai ayi competition muna cikin yi sai jabir ya kira salim wai yaxo ya buga bayan ya taho shine ya buga mashi ball akanshi'', kallon jabir tayi sannan tace ''kai daman baqin hali yayi maka yawa ka godewa Allah ba yarana ka bugama kwallon nan ba da wallahi sainaci uwarka...jan yayanta tayi fuu suka wuce parlor salim kuwa bawan Allah ko kallonshi batayi ba ta wuce cikin gida, jabir da jalal kuwa daukan ball din sukayi suma suka wuce cikin gidan, anan suka bar salim sai matse kwalla yake idanun shi duk sunyi ja goshinsa ya kumbura sosai don ba karamin bugu jabir yayi mashi ba. Yana nan tsaye wata yarinya wadda akalla bazata wuce shekara goma sha biyar ba kyakyawa ce fuskarta sak irin ta salim amma ita ta fishi dogon hanci sannan ita zubinta irin na sirarara ne, hannun ta rike da bucket din kaya da alamu shanya zatayi, juyawa tayi zata wuce hanyar backyard din gida domin anan suke yin shanyar kayansu jin sautin kuka yasa tadan juyo saitin compound din gidan aykuwa karaf idanunta suka sauka kan salim da ya tsugunna yana kwalla, kallonshi tayi da kyau sannan tace '' Salim zonan juyowa yayi jin muryar yayarshi salima, aguje ya taho wajenta, kallonshi tayi sannan tace ''subhanallah salim meya sameka haka? Waye ya dakeka?
Kallonta yayi sannan yace'' ya salima ina zaune wajen famfo ina kallon su jabir suna buga ball shine yace nazo muyi ina zuwa ya buga min ball akaina, kallonshi tayi cikin tausayin kanin nata sannan tace ''Salim na fada maka kadaina wasa dasu bakaji kamanta abinda adda tace mana ko?, kasan ba son zamanmu suke ba acikin gidan nan nasu, kadaina kulasu kaji?'' girgiza mata kai yayi sannan yace'' toh ya salima bazan karaba. Hannunshi taja suka wuce backyard anan ya taimaka mata suna shanya kayansu data wanke, bayan sun gama ta kofar baya wadda take hade da kitchen din gidan suka shiga.
Wata yar budurwa ce ta juyama kofar kitchen din baya da alamu wanke wanke takeyi a sink din kitchen din tana tsaye, sanya take cikin doguwar rigar atampa kalar red da ratsin yellow ajikin rigar wadda ta zauna dass ajikinta, kanta hulace red, tanada diri sosai saboda kana ganinta ta baya zaka hango yanda mazaunan ta wanda suke dan girgizawa sakamakon juyin da takeyi wajen dauraye kayan wanke wanken jikinta irin shape din hour glass ne irinsu ne ake kira da figure 8, tanada hips masha allah har ya rinjaye jikin nata sannan da alamu tana da kiba salim ne ya taho aguje gefenta ya tsaya yace '' adda na sannu da aiki'' juyowa tayi tana kallonshi sannan ta kalli salima data tsaya gefen shi suna mata murmushi itama murmushin tayi masu...ina ganin fuskarta nace masha Allah, yarinya ce kyakyawa itama black beauty ce chocolate color irin wankan tarwada dinnan ita baza ace mata choco ba ita baza ace mata fara ba sbd tafi salim da salima dan haske amma itama din tana cikin category din chocolate colors, hancin ta kuwa kamar har yafi na salim da salima mikewa wanda ya karama fuskarta kyau da annuri, tana da idanu manya manya round afuskarta wul wul dasu suna dauke da eyelashes zara zara tana da cikar gashin gira har yana nema ya hade, bakinta kuwa yana nan oval shape gwanin birgewa, batashafa komai ba a lebanta amma kamar an goga jambaki, ta wajen lip line dinta kuwa yadanyi baki ba sosai ba wanda ya karama bakin nata kyau sosai, itama akalla bazata wuce 19yrs ba tanada boobies manya daidai jikinta sannan batada wani tumbi sosai doguwa ce sharr da ita amma akwai diri......., murmushi kawai take masu saidata kara kallon salim sosai tukunna ta bude baki ta tace '' ya Allah salim what's wrong with your forehead?, shuru yayi sbd yana tsoron kar tayi mashi fada, salima ce tayi charaf tace '' adda Amra wasa yaje zaiyi da wa'enchan mugayen yaran shine suka buga mashi ball ah goshi, na fada mashi ya daina zuwa wajensu yaqi ay gashi nan yajama kanshi",.... Kallonshi wadda aka kira da amra tayi sannan ta tsame hannunta daga wanke wanken sannan tace salim I thought we've talked about this na fada maka kadaina zuwa wajensu sbd duk sanda ka rabe su sai sunyi maka mugunta kuma idan kayi kokarin ramawa kuma iyayensu su huce akanka dan Allah Salim ka rufa mana asiri kadaina zuwa wajensu, ka zauna kayi wasan ka kai kadai kaji ko"? Girgiza mata kai yayi sannan yace insha Allah adda bazan kara ba,murmushi tayi mashi sannan ta jawoshi jikinta tace ''matso nan na gani dakyau'' matsowa yayi sannan ta jawo shi sosai tadan duqa ta fara lailaya mashi goshin nashi, bakinshi ya bude zai fara ihu ganin salima na neman buge mashi bakin nashi yasa yadan runtse idanun shi, ahankali amra ta fara mulmula mashi har saida goshin ya koma, matse kwalla yayi sannan yace adda akwai zafi sosai kaina ya fara ciko, kallon salima tayi sannan tace '' salima kije daki akwai Panadol acikin drawer dressing mirror ki bashi yasha ya kwanta kafin akira sallah dhuhr",..hannunshi salima ta ja suka wuce cikin gidan, ita kuma amra ta cigaba da wanke wanken.
Saida ta tabbatar ta gama wanke duk wani plates da tukwane da akayi using na breakfast din safe tukunna ta share kitchen din, ko'ina saida taga yayi tsaftsaf sannan ta fito da vegetables daga fridge domin daura lunch, wanke vegetables din tayi a sink sannan ta aje su ah kitchen island domin fara yayyankawa, anatse ta fara yanka su red bell pepper dasu carrot anatse cikin qwarewa take yi komai saida ta gama tukunna ta daura tukunya akan gas, saidata fito da tafashen nama dasu blended kayan miya daga fridge tukunna ta fara soyawa, cikin mintuna kadan ta kammala beaf sauce dinta sannan ta juye acikin warmars, bayan ta gama ta daura couscous dayake yanada shi yana da sauqin dahuwa bata wani jima ba ta gama sannan ta fara yankan su salad da cabbage dasu carrot saidata gama tukunna ta faara preparing salad din...cikin nutsuwa ta gama komai ta gyara ko'ina sannan ta fita da warmers din,..ahankali take tafiya har ta iso dining area wanda baida tazara sosai da kitchen din, dining ne babba mai dauke da chair goma sha biyu, kujerun ajare suke colorn black and gold, gefenshi wani babban console ne shima black and gold Sai wata katuwar artificial flowers by the corner wadda ta karama wajen kyau saidan dispenser babba daga gefe,anatse ta fara jera komai tsaftsaf gwanin birgewa, saidata tabbatar ta gama komai tukunna hankalinta ya dawo jikinta sauka tayi daga stairs din dining din ta wuce sitting room, babban parlor ne sosai irin na gidan manyan mutane yasha ado sosai shima yana dauke da kujeru black da ratsin gold tsakiyar parlor kuwa wani qaton carpet ne gold babba sosai sai wani katon center table shima yasha adon kayan alatu na zamani gefen kujerun kuwa wasu shegun side stools ne masu kyan gaske na wood, agaban parlorn kuwa wata tapkekiyar tv ce wadda take akunne an saka tashar nickelodeon da alamu yaran gidan ne suke kallo daga bisani suka tashi suka bar parlorn da tv din akunne , ahankali ta wuce wajen tv station din sannan ta kasha switch din, bayan ta rage hasken chandelier parlor din, komawa tayi hanyar dazai sadaka da kitchen daga gefe akwai wani corridor wucewa tayi harta karasa dakuna biyu ne a wajen suna facing juna, daki daya ta tunkara sannan ta wuce bakinta dauke da sallama, dakine mai dan girma aciki kuwa dan matsa'kaicin gado ne mai dan girma sai karamin carpet atsakiyan daki daga ciki kuwa toilet ne aciki sai yar wardrop a gefen wajen shiga toilet din, anatse ta shiga ciki, juyowa salima tayi wadda take zauna akan kujerar dressing mirror din su mai dauke da dan turare da mai na shafawa da roll on kallonta amra tayi sannan tace ''an fara abinda aka saba ne'',kallonta salima tayi sannan tace '' adda wallahi har allah allah nake Monday tayi mu koma school zaman dakin nan ya ishe ni wallahi donma allah ya taimaka wannan zane zanen da nakeyi yana dauke min hankali,"..kallon book din hannunta amra tayi sannan tace ''our future architect muga yau me kika zana'' ...karban book din hannunta amra tayi sannan ta fara kallon book din.... Zanen gida ne salima tayi wanda ya dauki hankali amra harda nima , murmushi amra tayi sannan tace gaskia salima allah yayi maki basira kina da talent wallahi gidan yayi kyau sosai dan allah kiyi kokari ki maida hankali a karatunki kinji salima inaso mu nunama duniya cewa muma ýaýa ne kuma Allah yana tare damu kuma shi zaiji qan mu, yanxu dai duba kiga ke kadaice kika gado talent din abba yanxu da yana raye zaiyi alfahari dake, Allah ya jiqanshi da umma,, amma dukda haka nima ina alfahari dake kuma insha allah bazakuyi kukan maraici ba zan tsaya maku zan zamo gatanku keda salim insha Allah bazan bari ku wulaqanta ba zanyi duk abinda zanyi don naga kun samu farin ciki..takai karshe tare da share kwallar data zubo mata ita ma dai salima kukan take yi, babu abinda take tunani face rayuwar da sukayi da iyayensu cikin gata da kulawa da soyayyar da iyayen su ke nuna masu rana daya kuwa Allah ya dauke ran su, tunanin wannan kadai yasa suka fashe da kuka acikin su an rasa wanda zai lallashi wani ...dafa su da akayi ne ya dawo dasu daga koke koken nasu, salim ne tsaye yana kallon su da alamu daga barci ya tashi, kallonsu yayi sannan yace adda kukan me kuke yi ne keda salima, goge hawayen suka fara yi da hanzari ganin ya fara nuna damuwa, salim ya fisu rauni sbd yafisu jin mutuwar iyayensu dalili kuwa agaban idonshi iyayensu suka rasu wanda shine ya zama silar kamuwar ciwon zuciya da yake dashi shiyasa koda wasa basa bari damuwa ta fito ah fuskar su har ya gani shima ya fara damuwa wanda dalilin ne yake sashi rashin lapiya sosai gudun haka yasa suke gujewar fadawar shi damuwa. Kallonshi sukayi suna qaqalo murmushi, ''salim ashe ka tashi'' amra ce tayi mashi Magana, murmushi yayi mata sannan yace ''adda na yanxu na tashi'' kallon agogon bangon daki tayi sannan tace an kira salla kaje kayi alwala ka wuce masjid kaji ko, kana dawowa ka dawo daki sai in baka abinci kaci'' murmushi yayi mata sannan yace ''okay adda bari na tafi'' fucewa yayi daga dakin sai alokacin salima ta samu damar yin Magana ''adda ya kamata mu daina koke koken nan ina tsoron kar salim ya gane halin da muke ciki sbd lalurar shi""..girgida mata kai amra tayi sannan tace "hakane salima dole mu kiyaye gaba, ni bari na wuce toilet nayi alwala tunda an kira sallah,''. wucewa toilet din tayi, cikin toilet din tsaftsaf babu kazanta, ko ina kamshi yake sbd basuda kazanta kwata kwata, saidata dauro alwala tukunna ta fito anan ta tarar da salima ta kwanta ta fada tunani, kallonta amra tayi har zatayi mata maganar salla saita tuna cewa batayin sallah, wucewa tayi wajen wardrop din nasu ta jikin bango, hijab ta dauko tare da sallaya, ta fuskanci qibla sannan ta tada sallah, atsanake take ibadarta harta sallame sannan ta fara kwararo adduói neman gafara ma iyayenta awajen Allah sannan ta nema masu ita da 'kannenta kariya daga duk wani sharri na mutun dana aljan da kuma karfe, ta dade tana rokon Allah daga bisani salim ya shugo cikin daki, zama yayi gefen salima yana jiran amra ta shafa yayi mata Magana sbd yunwa yakeji dama shi baya jure yunwa kwata kwata. ..Shafawa tayi sannan ta miqe ta ninke sallayan da hijab din ta maida cikin wardrp... kallonta Salim yayi ya bude baki zaiyi Magana karaf amra ta amshe da ''nasan me zaka ce, muje kitchen na baka daman nasan baka jure yunwa, wucewa tayi ya biyo bayanta itadai salima tana zaune kwata kwata bata cikin annushuwa. Kitchen din suka wuce, bude tukunyan amra tayi sannan ta zuba mashi sauran abincin data rage masu dama sukam basa cikin jerin yan cin abinci a dining , bayan ta zuba mashi sannan ta zuba masu itada salima sannan suka fito bayan ta dauko masu ruwan da suke durawa a bottle daga dispenser domin kuwa shima ruwan bottle water baya cikin ruwan da aka yarda su dinka dauka suna sha, dakin su direct suka wuce sannan suka zauna suka fara cin abinci, santin abinci salim ya fara yi bayan ya cinye lomar karshe sannan ya kalli amra yace '' adda wallahil azeem kin iya girki nidai duk sanda mama rabi tazo ta amshi girki da aiki wallahi bana jin dadin girkinta har sai girkin ya dawo hannunki, wallahi cikina ya koshi amma bakina bai koshi ba beef sauce din tayi dadi sosai''...bayan ya gama ya fara tandar hannun shi kallonshi amra da salima sukayi sannan suka kwashe da dariya, amra ce ta kalleshi sannan tace ''kai salim wallahi ka iya abin dariya har dasu sude hannu'' dariya itama salima tayi sannan tace "wallah adda da gaske yake fah, wallahi babu ranar da zakiyi girki kunne na bai motsa ba anya bazaki shiga gasar kirki ba kuwa'' dariya amra tayi sannan tace kudai kun iya zuzuta abu, dariya dukkansu sukayi sannan suka cigaba da hirarsu.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomanceAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...