Page__10.
*FATHIYYA*
Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*"Hmm! Mahmoud kaifa ka ƙyale Zinnira shi yasa take yi maka irin wannan tsiyatakun, mata da kake gani sam basu da hankali, burin su kawai su saka maka hawan jini ka mutu kabar musu gado suyi yadda suke so, amma wallahi da nine kai da tuni na ƙaro aure ko na sallami Zinnira don ba zan iya da wannan guntun iskanci da wulaƙancin nata ba, haka fa Fathiyya jiya tayi mini ƙarfe kusan goma da wani abu na dare ina yi mata magana tayi banza dani akan na bata shawara taje ta nemawa kanta magani kada nazo na ƙara auren nan tazo tana ganin laifina, shikenan ta hau bakin ɗabiar da sam ba tata ba tayi ta faffaɗa mini magana, wallahi sai ta gane kurenta akan hakan!"
Farouq ya faɗa yana kallon Mahmoud daya gani wani birkice kamar ba shi ba, don kai tsaye yana fitowa wajen shi ya nufa ya taddashi cikin nashi ɓaci ran shima, daga nan kuma ya ɗauke shi suka nufi Blue Cabana suka ci abinci don kowanen su yunwar cikin shi ta ishe shi, shine bayan sun gama yake labartawa Farouq abinda ya faru tsakanin shi da Zinnira don basa ɓoyewa juna matsalolin gidajen su da matan su.
Ajiyar zuciya Mahmoud ya sauke yana kallon Farouq dake goge hannun shi da tissue yace "Farouq matsalar Fathiyya mai sauƙi ce kuma ya kamata ka duba mata kayi mata adalci, kai da kanka yanzu kace bata taɓa yi maka abinda ya faru tsakaninku jiya ba, to me zaisa baza kayi mata uzuri ba? Ita fa tana son haihuwar nan da kai, tana yi maka ladabi, tana kyautata maka komai tana yi maka, don wannan damuwar ai yaci ace ka shanye duba da yanayin da take ciki na zancen wannan ƙarin auren naka da take ganin don ta kasa baka ƴaƴa zaka yi shi, Nira fa?"
"Kai ka ƙyaleta na faɗa maka, ni yanzu ma nake ganin Mami gata tayi mini ashe ban sani ba, jiya naje mun haɗu da Sameera kuma mun daidaita kanmu, don haka ka shirya nan da sati biyu don bazan yarda a ɗau lokaci ba, na fahimci itace cikar farin cikina, don idan Fathiyya ta ɓata mun tabbas zata gyara mun, tun jiya na fara ganin hakan, gata da iya tsara kalami cikin wata irin sassanyar murya da duk tabi ta kashe mini jiki, ai wallahi abokina ba zan iya jiran tsawon lokaci ba da wurwuri za'a yi abun nan ko na samu hankali na ya kwanta".
"To kadai ji tsoron ALLAH, yadda kake faɗar halayen Fathiyya bai ci ka wulaƙantata ba, komai zata yi maka a wannan lokacin kayi haƙuri kayi mata uzuri, akwai so akwai kuma kishi, sune zasu taru su haifar da hakan, a gefe kuma ga sheɗan da muguwar zuciya, sai kun yi da gaske daga kai har ita musamman kai, don haka ka lallaɓata har ALLAH yasa komai ya daidaita".
"Ba zaka gane ba Mahmoud, mata sai da wuta, yadda na ɗaure mata a yau na tabbata dole zata zubar da makaman ta wanda ba don nayi hakan ba ALLAH kaɗai yasan tsiyar da zata yi don haka ba taga komai ba ma wallahi."
"Subhanallahi, matar taka Farouq, wai kodai jiya sameera ta baka ka shanye daga zuwa shi yasa kake neman birkicewa yarinyar mutane". Ya ƙare maganar cikin sigar tsokana suna dariya suka tafa haɗe da miƙewa Farouq na jaddadawa Mahmoud ya ƙara aure shima hakan zai sa ya rabu da matsalar Zinnira, dariya yayi lokacin da suka iso bakin motocinsu yana kallon shi yace
"Ai Ni mijin mace ɗaya ne Farouq idan ba wata ƙaddara daga ALLAH ba, ana aure ne idan mutum zai iya adalci ni kuma da kake gani nan na tabbata bazan iya adalci ba don duk duniya yanzu babu wacce nake so kamar Nira, ina yi mata kallon uwa, uba, mata kuma ƴan uwa domin ita ce asusun sirrina a yanzu, ita tafi kusanci dani fiye da kowa, ita kaɗai nake da ita da zan bugi ƙirji nace tawa ce duk da tarin matsaltsalunta, soyayyarta ba zata bani damar yiwa duk wata mace da zan haɗa da ita kishi adalci ba, kaga kuwa maganin a bari kar a fara, na sani Nira nada matsala tana kuma bani ciwon kai, amma a randa na sake ɗauko wata matar na aura gani nakebyi na ƙarowa kaina matsala, gara na bari na fara gyara wacce nake tare da ita tukuna, na canza mata hali ko kuma na saba da matsaltsalunta ta yadda bazan riƙa kallonsu a matsayin matsala ba sannan in har ta kama dole sai nabƙaro wani auren, but for now na bar maka abokina ALLAH ya tabbatar muku da alkhairi".
STAI LEGGENDO
FATHIYYA
Storie d'amoreFathiyya! Labari akan wasu abokai kuma aminai guda biyu wato FAROUQ da MAHMOUD, inda ƙaddara tayi wa rayuwarsu ƙullin goro akan mace ɗaya mai suna FATHIYYA. FAROUQ shine masoyinta kuma mijinta da take jin cewa mutuwa ce kaɗai zata iya rabasu, kwats...