BABI NA GOMA SHA BIYAR

138 3 0
                                    

Page__15.

*FATHIYYA*

Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*

*LAST FREE PAGE*

Washe gari tun da safe Mami ke faman doka mishi kira tana nemanshi akan zancen da suka yi da mahaifiyar Sameera jiya duk da jiya da daddare da suka yi waya dashi ta ce tana son ganinshi yace mata zai zo idan ya tashi daga office amma hakan bai hanata kiran shi tana sake tunatar dashi lallai-lallai fa yana tashi daga office ɗin ya wuto don tana son ganin shi urgently.

Kai tsaye yana tashi daga office ɗin gidansu ya wuce duk da yaso biyawa ta wajen Sameera ya ganta saboda bai samu da safe ya je ba kamar yadda ya saba mata da hakan kullum, sai dai kiran na Mami yasa dole ta haƙura ya fara zuwa yaji neman da take yi mishi tunda bata faɗa mishi komai ba tafi so suyi ido da ido dashi tukuna.

A ɗakin Mamin ya tarar da ita ne tare da 'yammatan ƙannen shi dasu Bushriya da Zainab. Yana shigowa Bushriya da ta kasance sakuwar shi ta hau guɗa tana cewa "kaga angon Sameera, irin wannan ƙyallin goshi haka tun ma baka angwance ba".

Tsaki yayi yana zama akan gadon Mamin yace "ke dai ba'a rabaki da shirme sai kace yarinya ƙarama, zan faɗawa Fathiyya kina cikin partyn ƴan adawa".

Dariya tayi tace "daga faɗar gaskiya Ya Farouq? Ai ita ma kanta tasan bama tare da ita Sameera ce tamu da zata zo ta haifa mana ƴan dugui-dugui ko ba haka ba Zainab?".

Dariya Zainab ɗin tayi duk da bata irin wannan wasan dashi ta ce "haka ne wallahi mu muna bayan amarya dama". Tayi maganar a takaice don bai fiye bata fuskar da zasu yi irin wannan wasan da shi ba, ita ma Bushriya don tare suka taso saboda tsiran su babu yawa yasa bata shayin yi mishi wasa.

"Mami ina yini" ya russuna yana gaida mahaifiyar tashi.

"Lafiya lau, tun ɗazu da nake kiranka sai yanzu kaga damar zuwa" ta ƙarashe zancen nata da ƙorafi.

"Kiyi haƙuri Mami wallahi ayyuka ne suka tsareni sai yanzu na samu kaina".

"Um-hm" tace "dama batun inda zaka aje Sameera ne.." yayi saurin katseta ta hanyar cewa, "Sai me ya faru Mami?" Don sai da gabanshi yayi wata irin muguwar faɗuwa don a tunaninshi wani kisannm kuɗin ne zasu sa ya sake yiwa gidan.

"Ba ayi komai ba, kawai so nake yi ka haɗesu waje ɗaya".

"Amma Mami gidan zai matsesu, asali ma tsarin mace ɗaya ne sai wajen saukar baƙi dake nan ƙasa, taya zai ishesu zama?"

"Na dai faɗa maka haka nake buƙatar kayi, sannan Sameera ce zata zauna sama ita kuma matarka ta dawo ƙasa".

"Amma Mami..." Kafin yace wani abu ta ɗaga mishi hannu haɗe da cewa

"Umurni ne nake baka ba shawara ba, don haka idan kaga dama kabi ko kuma ka fasa". Tana gama maganar ta miƙe ta bar ɗakin fuskar nan tata a murtuƙe.

"Menene Ya Farouq, gidan ka ne fa sai yadda kace ayi za ayi, banga abun damuwa ba cikin lamarin nan, in dai ba baƙin ciki ba shekaru nawa tana a saman nan, don ance ki sauko sai ya zama damuwa? Kuma ai anan ƙasa akwai wani ɗaki na gani ciki da parlour banda ɗakin baƙi dake can corridor, sai ka gyara mata ta dawo nan". Bushriya ta faɗa tana ɓata rai, shiru ya ɗan yi kafin can shawarar Bushriya ta kama kan shi, tabbas zai iya yin hakan in yaso ɗakin baƙin zai iya  ɗibar shi yayi wa Fathiyya kitchen sauran ya ƙara haɗe mata shi ta can cikin parlourn ta saboda ya ƙara girma don set biyu na kujeru take dashi, nan take shawarar Bushriya ta kama kan shi ya gama tsara yadda za'a fitar mishi da tsarin, ajiyar zuciya ya sauke tare da kallonta ya ce "eh ina ga hakan za ayi Bushriya, shawarar kin nan tayi sosai".

Murmushi tayi irin na samun nasarar nan haɗe da cewa "Ah to shine ai, naga zaka fara dogon tunani da damuwa kana fresh angonka". Suka sa dariyar tare yana nuna ta da key ɗin motar hannunsa, "Ke ko? Baki da dama Bushriya, ni zan tafi sai an jima".

FATHIYYAWhere stories live. Discover now