Alhaji Badaru gambo, alhaji badaru haifanfan dan garin katsina ne, anan ya taso agaban iyayenshi da kaninshi alhaji sammani, alhaji badaru mutun ne mai mutunci mai hakuri da sanin yakamata kuma mai son yan uwanshi, su kadai ne awajen mahaifinsu, anan katsina ya hadu da larai wadda ta kasan mace mai hakuri da juriya, shekarar su goma da alhaji badaru allah bai basu haihuwa ba, alhaji badaru bai damu ba sbd haihuwa daga Allah ce, suna zaman lafiya shida matarshi bashida wata damuwa inda alhaji sammani kuwa kanin badaru ya koma kano domin yin kasuwanci anan katsina yabar dan uwanshi badaru, badaru shike kula da mahaifinshi sbd tun bayan haihuwar sammani mahaifiyarsa ta rasu allah ya karbi abarshi, akwana atashi babu wuya shekara wajen goma sha biyar larai babu ciki babu goyo at this point abin ya dan fara damun badaru dukda baya nuna mata cewa ya damu, ana haka har sammani yayi aure ya aure amaryarsa talatuwa inda ashekarar da sukayi aure ta haifi danta santalele inda yaci sunansa Mustapha, Mustapha nada shekara uku allah yayi mashi rasuwa,sammani yaji mutuwar danshi sosai harda yayan shi Mustapha sbd yaso yaron nan kamar dan cikinshi dukda sbd Mustapha sammani ya dawo katsina tare da matarshi talatu ana haka kuwa kanwar talatu wadda take mabiyar ta tazo katsina domin zama tare da yar uwarta anan ne asalin true color din talatu ya fito ganin kasuwancin badaru har yaso yafi na minjinta sammani, gashi bashida da balle jika, ganin haka saita fara kwadaituwa ta gidan badaru asannu cikin ruwan sanyi ta fara zuga sammani akan ya tilastawa dan uwanshi ya kara aure wataqila rashin haihuwarshi daga matarshi ne ba daga shi ba, aikuwa sammani ya samu dan uwanshi da maganar, shidai badaru har yanxu baida wani raayin aure sbd haka ya nuna bai amince ba, ganin badaru bashida niyar kara aure yasa talatu shiga malamai don ganin qanwarta ta samu shiga cikin gidan badaru gashi har lokacin arzikin da badaru yake yi har yaci uwar na sammani nesa ba kusa ba, anan ne Allah yayi ma mahaifinsu rasuwa, bayan rasuwar mahaifinsu badaru ya shiga damuwa sosai ba kadan ba, baya cikin walwala ko kadan daga nan ne kuma ya fara bullo da sabbin halaye na wulakanci, haka dai larai ta daure ta hadiya suna zaman dukda babu dadi, ana haka badaru ya bullo da zancen kara aure, anan ya shaidawa sammani cewa shifa yaji ya gani yana son qanwar matarshi binta, sammani kuwa yaji dadi sosai da kanshi ya nemawa dan uwansa auren kanwar matarshi kuma aka bashi aurenta. Bayan wata biyu aka daura auren badaru da binta kanwar talatuwa, ansha budiri kuwa, duk wannan abun akan idon larai amma bata taba tankawa ba shima kuwa baice mata komai ba, acikin dan zamansu larai ta fuskanci cewa makirci talatu da kanwarta suke shirya wa wadda kanwar talatu har taci uwar talatu ah iya mugunta da wulaqanci ana haka saiga ciki ya bullowa binta, murna farinciki babu wanda badaru baiyiba har Allah ya sauke binta ta haifi santalelen danta inda badaru yayi alkawarin maida sunan marigayi dan gidan sammani Mustapha, anyi suna an kashe kudi sosai ah katsina.,
Yaro ya taso cikin soyayyar ubansa da kawun sa sannan kuma ya taso da mugunta irin ta uwarsa don akan idonsa uwar ke shiryawa larai mugunta iri iri, haka ya taso dai tun baisan me ake nufi da kyamatar mutun ba har ya fara kyamatar larai wato kishiyar mahaifiyarsa, bayan shekarun Mustapha goma aduniya kwanci tashi yau da gobe sai Allah, Allah ya azurta larai da ciki, tayi murna ta godema allah ba kadan ba, daga nan ne ta fara neman tsari daga mugunji da mugun gani tana addua akan allah ya tsareta da abinda ke cikinta da mijinta, har larai takai wata takwas wata rana ta tashi domin kuwa ranar girkinta ne bayan ta gama shirya abinci ta zuba nasu itada badaru ta koma ta aje nata adaki sannan ta fita domin karban ruwan adduar naquda bayan fitarta kuwa saiga Mustapha ya shugo dakin innarsa rai abace dama itake zugashi akan cewa idan har yana kallo larai ta haihu to shikenan gatan da ake mashi yakare, aikuwa ranar ya dawo gida saboda babansa badaru wanda yayi mashi fada akan abokanan banza da yake tara wa,dakin innarsa ya fada nan ya taddata tana shirin fita hannunta rike da wani qulli da alamu batasan ya shugo cikin dakin ba, ganin ya shugo rai abace nan ta shiga tambayar sa me akayi mashi nan take ya zayyane mata komai dagana ta dora mashi da cewa ''ay matsiyaciyar matarshin chan ce ta zuga sa sbd haka yau zamu dauka fansa, kaga wannan kullin kaje uwar dakanta nasan yanxu malam ya wuce sallar magariba kaje ka zuba cikin kwanan abincinta dazarar taci nan take zata mutu kowa ya huta, ay kuwa yana karba ya wuce dakin yana zuwa ya tarar da kwanon larai anan ya zazzage duka maganin sannan ya juya miyar kukan datayi, ya fice daga dakin yana dariya,fitarsa keda wuya saiga malam ya dawo daga masallaci yana shiga daki baiga larai ba daman ta fada mashi zata je gidan malam liman domin karbo ruwan adduar naquda.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomanceAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...