9&10

143 3 0
                                    

badaru na shiga dakin kuwa ya tarar da flask din data aje abinci dama da yunwarsa ya dawo, zama yayi ya zubama kanshi sannan yayi bismillah yaci ya koshi yayi dam daga bisani yayi sallar isha í sannan ya kishingida yayi kwanciyarsa, koda larai ta dawo ganin mijin nata yana barci yasa bata tashe sa ba, sallah itama tayi sannan tayi kwanciyarta already daman dataje gidan malam liman taci alala da matar liman tayi wadda ta bata sha'awa dama matar lima inno kawarta ce kut da kut, gab da asuba ta farka ganin badaru dai baccin shi yake hankali kwance yasa itama ta koma barcin ta, binta kuwa ganin malam bai fito ba kuma bataji sakamakon abinda take jira ba kawai saita wuce bangaren larai, tana zuwa kuwa ta fara doka masu sallama, larai ce kawai ke iya amsawa sannan ta fito ta sameta, ganin lafiya kalau larai ta fito yasa hankalin binta tashi sosai, gyara nutsuwar ta tayi sannan tace ''kicema badaru inason ganinshi'' wucewa ciki larai tayi sannan ta fara tashin badaru, ganin ko matsi bayayi yasa hankalinta ya tashi, daga karshe dai ta dunga kwala mashi kira ganin baya nunfashi yasa larai kwala ihu nan take ta fadi assume, jin ihun larai yasa binta shugowa da hanzari koda ta shugo taga badaru babu rai saita fara ihu anan take kuwa gidan ya cika da mutane anan aka gane cewa badaru ya mutu cikin barcinshi itakuwa larai doguwar suma tayi bayan an taimaka mata ta farfado nan hankalinta ya tashi ganin badaru ya tafi ya barta tapiya ta har abada, tayi kuka tayi kuka ta godema Allah daga karshe ganin za ah kai badaru makwanci sa yasa larai nagudar dole anan matar liman inno ta taimaka ta kaita wani dakin kaya extra agida, anan aka kira wata nurse makwapciyarsu tazo domin taimakon gaggawa, matar bata ida zuwaba kuwa larai ta haifi santalelen danta kyakyawan gaske gashi black beauty.
Bayan kwana bakwai yaro yaci sunan mahaifinshi marigayi wanda ya rasu aranar da aka haifeshi wato Badaru...binta kuwa ashe tana dauke da sabon ciki wanda sai bayan mutuwar malam ya baiyyana, binta tayi rainon cikinta har wata tara sannan ta haife danta inda yaci sunan sa Aliyu haidar koda sammani yaso yasama yaron suna sai binta ta nuna tanason ta sawa danta suna da kanta aikuwa ya barta da abinta.
Badaru ya taso cikin koshin lapiya da son dan uwanshi Mustapha wanda shima haka Mustapha ya nuna mashi qauna sosai sun taso tare inda badaru keda shekara goma shi kuma Mustapha yanada shekara ashirin dama shekaru goma ne tsakanin su in badan an fada maka ba bazaka taba sani cewa ba uwa daya ce ta haifesu ba, suna kaunar junan su sosai inda aliyu haidar kuwa yakeda shekaru tara aduniya don kuwa badaru ya girmeshi da shekara daya, yanda Mustapha keson badaru kwata kwata baya yima aliyu wannan soyayar, dama gashi shi aliyu bashida hayaniya kuma bai damu da sha'aninsu ba, lokacin da badaru ya kammala secondary school dinshi alokacin shikuma Mustapha ya aje bokon ya shiga kasuwanci inda allah ya buda mashi lokaci guda ya zama tambatsentsen dan kasuwa mai shegen kudi ganin haka yasa badaru ya bishi zuwa kano anan ne ya samu admission ah BUK inda ya fara karanta architecture,Mustapha kuwa anan kano ya hadu da kareema awajen wani taron yan kasuwa tazo tare da baban ta nan kuwa taji itama Mustapha ya zauna mata bayan yan watanni akayi aurensu. badaru yaro ne mai basira da son mutane cikin kankanin lokaci BUK tasan da zaman badaru inda yana kammala karatunshi yayi bautar kasa anan ne wani company suka daukeshi aiki ya zama babban mutun sbd irin kwazon da yake dashi wajen iya zane, har competition akayi na architects cikin ikon Allah shine ya zama gwarzo afadin Nigeria anan ne duniya tasan da badaru daukaka tazo mashi har Allah ya daga shi ya fara tafiye tafiye,alokaci yana da shekaru ashirin da biyar aduniya anan ne yayi tafiya izuwa morocco domin yin wani project anan ne allah ya hadashi da shuwaira, shuwaira marainiyace batada iyaye sun rasu amma tana tare da kanin mahaifinta da matarshi waenda Allah bai taba basu haihuwa ba, shuwaira haifaffiyar yar morocco ce irin black beauties din morocco's tana aiki ah wani private hospital, amatsayi nurse, ranar da suka fara haduwa da badaru kuwa ranar yaje overall body check up domin office din da zaiyi aiki dasu ah morocco ba a fara aiki dasu saika kawo health history dinka, aranar kuwa ta kasance duty din shuwaira, bayan ta shigo patient scanning room kanta akasa tana karanta information dinshi, muryarta ce ta dawo dashi daga danne dannen wayan da yake yi, wani irin melodious voice yaji akunnan shi '' hey mr badaru how are you today? I will be the nurse to check you up today'', da sauri ya dago kanshi domin jin me daddaden muryar nan, ya shagala da kallonta saidatayi gyaran murya bayan itama ta gama kallonshi sannan tace ''sorry i'm i in a wrong room?'' cikin inda inda da kuma shauqin ganinta yasa badaru cewa ''no noo you're in the right room, right close to my heart, ganin yanda badaru ya lalace da kallonta yasa tayi dariya tace ''kallon ya isa haka karkasa na kasa aikina mana'' aikuwa kunya ta lullube badaru baisan lokacin dayace mata ''mss na kasa daina kallon ki don allah ki bani magani ko zan iya cire idanuna akanki, ganin badaru na neman zaucewa yasata cewa "lallai kana da enough time yau dinnan don inaga kwana zamuyi ahaka you're not ready for the full body scanning, ganin zata fice yasashi rike hannunta,

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now