11&12

135 3 0
                                    

ganin zata fice yasashi rike hannunta, juyowa tayi zatayi Magana ya katse ta da cewa ''I'm sorry my lady let's begin with the scan,ganin how cool and gentle badaru keyi mata magana sai taji ya burgeta, preparing dinshi tayi bayan ya chanza outfit dinshi zuwa na asibiti anatse ta taimaka mashi ya shiga cikin body scanning machine din, saida ta tabbatar ta duba lafiyarshi tukunna tayi mashi sallama, zata wuce Kenan yace '' right now at this moment I want to be the only man in your life that will love and take care of u'' ita abima har mamaki yake bata shiko wannan daga haduwa da ita bai santa ba bata sanshi ba kallonshi kawai tayi sai tayi murmushi ta fita. Koda badaru ya koma gida hankalinshi sam baya jikinshi tunanin shuwaira kawai yake yi ta tafi da imanin shi yanda take magana da yanda take al'amuranta gaba daya ya tafi dashi, haka dai ya lallaba kullum saiyaje asibitin nan, da farko shuwaira bata amince mashi ba daga baya kuma ta fara tausaya mashi harta fara sonshi. Ganin irin soyayyar dake girma tsakanin shuwaira da badaru yasa iyayenta wanda suke riketa suka zauna da badaru domin yayi masu bayanin asalinshi,koda yayi masu bayanin asalinsa Sai uncle ya aminta dashi kuma yayi alqawarin aura mashi shuwaira tunda itama ta nuna tanaso, dukda anty dinta matar uncle bata soba,bayan Yan watanni uncle ya aura ma badaru shuwaira amma da sharadin bazai koma gida ba zai zauna da ita ah Morocco, nan take badaru ya amince da sharadin su. antyn ta bataso hakan ba sbd tana tsoron gujewa matsala don lokacin da akayi auren babu wanda yazo daga bangaren badaru. Badaru kuwa babu wanda ya fadamawa cewa yayi aure saida suka shafe shekara kunsan biyar alokacin ko batan wata shuwaira bata samu ba suna zaman lpy sosai da ita da badaru dukda maganar danginsa yana damunta sosai, tunda sukayi aure saidai ya shirya ya je Nigeria yayi yan kwanakinsa ya dawo. Lokacin da badaru ya sanar da Mustapha auren da yayi a morocco ba karamin zafi Mustapha yaji ba ayanda ya dauki dan uwan nasa har yayi aure amma bai fada ma kowa ba aciki kuwa harda mahaifiyarshi larai wadda suke zaune anan katsina da ita da binta sai kaninsu  badaru aliyu haidar.
Bayan komawar badaru da wata daya yaji duk zaman morocco ya chanza masa yaji baya qaunar zama ah garin haka yasa ya samu shuwaira da batun komawa Nigeria, duk da shuwaira tana shaáwar ganin dangin badaru amma hakan bai sata jin babu dadi ba zatabar uncle dinta, bayan yan kwanaki badaru ya lallabata suka shirya sukayima su uncle sallama sannan suka taho Nigeria. Dirar su Kenan ah aminu kano international airport kano badaru ya dauki waya don ya kira dan uwansa, nan ya sanar dashi sun iso, minti kadan saiga Mustapha, Mustapha yaji dadi ganin badaru da iyalinshi, direct gidan Mustapha suka wuce inda anan suka huta sannan sukaci abinci aka kaisu dakin da zasu zauna, shuwaira dai taji dadin tarbar da akayi masu amma duk bata cikin natsuwar ta domin tunda suka iso ta fara jin fargaba hankalinta duk ba ajikin ta yake ba amma dai haka ta daure bata nuna ba, bayan yan kwanaki suka shirya harda iyalan Mustapha wato haj kareema da yayanta uku, wahab, Ibrahim da Muhammad.
Koda suka isa katsina ba karamin mamaki Mustapha yayi ba ganin yanda larai batayi ma badaru fadaba akan auren da yayi, abunda baisani ba ashe ya riga da ya fadi ma mahaifiyarshi komai agame da batun aurenshi kuma tasaka mashi albarka sannan ta umarceshi da ya dungo boye duk wani abun alkairinsa da zai faru dashi, bai dauki zancen baba larai da komai ba shiyasa bai nuna damuwa ba kuma shiyasa bai fadama kowa ba ciki kuwa harda dan uwansa Mustapha.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now