15&16

121 3 0
                                    

Chapter15-16

Duk sanda mama rabi ta fi kuwa amra ce ke karbar duk wani aikinta harsai ta dawo sbd haj kareema ce ta shimfida wannan dokar akan cewa Yayan riqo bazasuyi zaman lalaci ba, ita kuwa amra ta gwammace tayi komai kannenta su zauna su huta kamar yanda sauran yaran gidan suma suke rayuwar su babu takura, shiyasa koda haj kareema ta kawo sabon rule dinnan ita kuwa amra dadin haka taji don kuwa ya taimaketa sosai, babu girkin da za ah nuna mata har matan gidan ma kuma bata sangarce ba itakeyin komai nasu a gidan, abu biyu ne kawai batayi musu, na farko bata zuwa part din kowa acikin su sannan kuma bata yi masu wanki kuma bata shiga part din mai gidan wato alhaji Mustapha, yaya awajen ubanta sannan kuma uba awajen su ayanxu ita da kannenta.
Suna nan zaune adaki ita da kanneneta suka fara jin saukan motocin gidan da alamu sun fara dawowa, har akayi sallan ishaï suna zaune ita da kannenta salima tana zanenta while salim kuwa books din shi ya dauko yana assignment,sallamar da akayi ne yasasu dagowa suna kallon kofar don ganin mai yin sallamar, mama rabi ce ta shugo da yar ledar kayanta ahannu fuskarta dauke da murmushi tace "salim na dawo", da gudu kuwa ya tafi wajenta yana mama rabi allah yasa kin kawo min tsarabar raken danace maki,murmushi tayi mashi sannan suka karasa cikin dakin, kallonta amra tayi tare da salima sannan suka gaisheta, anan ta bawa kowa tsarabar shi ''kai salim ga rakenka, ke kuma salima dama goruba kikace min kina so toh ga naki'' washe baki salima tayi sannan tace kaii mama rabi allah ya bar mana ke'', ...murmushi tayi sannan ta kalli amra
tace mutuniyar arziki matar manya ga farar kasar ki nan ke ko gajiya bakyayi duk sati idan zan tafi sai kin bani dari biyar na sayo maki saikace mai ciki ko gajiya bakyayi dashan wannan abar"...dariya amra tayi ta kalleta tace mama rabi ke bakisan kwanakin da nakeyi Ina tattala kudin break dina na school ba duk don na tara na baki ki sayo min farar kasar nan, aykuwa nagode yau naga har yafi na last week yawa, nagode sosai'' karbar ledar amra tayi sannan ta bude ta dauka daya ta fara bantara tana wullawa abakinta, salima kuwa baki ya rufu sai faman gurzar goriba takeyi. Sallama mama rabi tayi masu sannan ta fice ta koma nata dakin dake opposite da nasu. Saida suka gama kusur kusur dinsu tukunna amra ta fita domin zubo masu abinci, anan ta tarar da ishaq, yana ganinta kuwa ya taho, kallonshi tayi sannan tace "bro ishaq yau baku wuni agida ba inata so ka koya min wani assignment da aka bamu a school kasan mun kusa gama exam din second term ni harna kosa wallahi na gama school dinnan wallahi wahalar damu suke yi sosai,'' dariya ishaq yayi sannan yace sis idan kince kin gaji da school to ai kuwa daddy aurar dake zaiyi wallahi karma kiyi fatan ki gama school yanxu'' turo baki tayi sannan tace ay kuwa babu auren da zanyi yanxu nida nake da burin zama babbar likita ay aure ba nawa bane''

kallonta yayi sannan yace "nikam dan allah adama min oat mana dama mun dawo da yunwa naje sama don nayi wanka ina dawowa naga yarannan sun cinye abinci da kikayi kinsan kowa baya resisting abincin ki sis" dariya tayi sannan ta shiga dama mashi oat din sannan ta bashi wucewa yayi yanace mata ''Thanks sis nagaji yanxu gobe idan za ah sauke mu a school zan koya maki'' murmushi kawai tayi aranta tana mamakin mutuncin ishaq sam babu ruwanshi bashida halayyar sauran yaran gidan, juyawa tayi sannan ta fara zuba masu abinci ita da kannenta, daki ta koma saida sukaci abinci sukayi nak ita da kannen ta sannan suka kwanta sbd su tashi da wuri.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now