19&20

128 3 0
                                    


Free page....

Chapter 19-20

Kallon salim amra tayi sannan tace kaje wajen mama rabi ka jira yanxu zanzo nima, fita yayi sannan ya jawo kofar ya fice, kallon salima amra tayi sannan tace ''salima da alamu bakida hankali ko, mekike shirin yi ne salima so kike ki jefamu cikin masifa kinsan yanda zaman mu yake acikin gidan yanxu mene amfanin mayar ma da dady Magana dakikayi, salima barikiji baki fini jin zafin abinda akeyi mana agidan ba don tun kafin ki mallaki hankalinki na fuskanci wulaqanci iri iri amma duk na koyi shanyewa kuma na hadiye, ina baki shawara ki yi kokari ki dunga danne wannan zafin zuciyar naki inba haka ba da ranki da nawa duk baci zaiyi.
kukan da salima ke hadiyewa ne ta fashe, sheshekar kuka kawai takeyi sannan ta dago ta kalli amra tace '' adda na gaji da wulaqancin da ake mana, na gaji da zagin iyayenmu ta akeyi, yau shekara bakwai Kenan da rasuwar su amma har yau ba adaina zaginsu ba mai sukayi da suka chanchanci wannan wulaqanci da rashin mutunci...mutuminnan ada yafi kowa qaunar mu lokacin da iayeyn mu suna raye amman ayanxu da kasa ta rufe masu ido shine yake wulaqanta mu".., tana kaiwa karshe ta fashe da kuka,..zama kusa da ita amra tayi ta rungumota jikinta tana lallashinta, saida taga tadaina kukan sannan tace salima ''I'm so sorry dan Allah kidaina bari damuwar ahalin gidan nan tana damunki baki ganni ba harna saba, duk rintsi duk wuya allah yana tare damu kinji shine zai kawo mana sassauci yanxu ki share hawayanki kizo muyi game ah yar nokia ta kinji"... dariya salima tayi tana kallon yar uwarta cikin so qauna tace ''thank you big sis, adda na, wallahi adda bansan ya zanyi ba idan babu ke",

kallon ta amra tayi sannan tace ''salima ina nan tare daku babu inda zanje zamuyi rayuwa atare insha Allah kinji small sis''.. dariya salima tayi daga bisani salim ya shugo cikin dakin, anan suka zauna suka sha hiransu su kadai sannan suka kwanta asuba ta gari.......

Haka kwanaki suka dinga tafiya har suka fara exam din second term ayau kuma Friday zasuyi last paper sannan ayi masu hutun term din, dadi sosai su salima sukeji sbd wahalar bulalar latti ta kare.
Bayan an taso su daga school gida direct suka wuce domin su shirya don washe gari za ah tafi katsina gaba daya gidan domin aje agaida kakannin wato kaka larai da kaka binta sai kawu aliyu.
Sammako sukayi don tafiyar hanya zasuyi daddy ne agaban sienna sai driver habu akujerar baya kuma hajiya kareema ce da Khadija azaune, chan quryar baya kuwa ishaq ne sai Muhammad sannan sai jabir da jalal motar bayansu kuwa itama sienna ce irin ta gaba, hajiya labiba ce abaya sai halim agefenta chan kuryar  baya kuwa Khalil ne da khamis sai amra da salima, a gaba kuwa driver haladu ne wanda ke tuqawa tare da salim, tafiyar awa uku sukayi suka iso katsina suna parking kuwa kowa ya fito, gidane dan matsakaici amma kuma anyi mashi gyara dan kuwa ginin bulo ne akayi part biyu acikin gidan daya yafi daya sosai nesa ba kusa ba, direct babban part din duk suka wuce hardasu salima suna shiga wata tsohuwa ce tukuf zaune akan tabarma daga gefe wata yarinya da bazata wuce shekaru goma sha takwas ba tana yi mata tausa, ganin masu shugowa yasa kaka binta Shewa tana fadin '' lale lale maraba yau manya manyan baki nayi acikin gida Mustapha na kaine yau agidan ...ke tsigai tashi kwaso tabarmu ashimfida kowa ya zauna,'' wucewa yarinyar tayi uwar daka sannan  ta fito da tabarmu ta fara shimfidawa, zama kowa yayi akasan sannan suka fara gaggaisawa, kareema ce ta kalli kaka larai sannan tace "inna mun sameku lafiya?", kallonta kaka larai tayi sannan tace aikuwa muna nan kalau tunda gashi kin ganni garau, ina waccar farar kishiyar taki?"
kallon labiba kaka tayi sannan tace au ashe gaki nan ko ni zan fara gaisheki ne?'' kallonta Haj labiba tayi sannan ta yatsine fuska tace sannu kaka mun sameku lafiya?"
ko amsata kaka batayi ba ta maida hankalinta ta kalli jikokin nata tace, "jikokin kaka babu ko gaisuwa"? , gaisheta sukayi gaba dayan su anan ne ta kalli su amra sannan tace, ke Aisha haka kike kiba saikace balan balan lallai Mustapha kana kokari ince suke cinye maka shinkafar gida har sunfi yayan ka qiba ma'' ..
dariya Mustapha yayi sannan yace ''inna ai ina kokari kam, ya muka sameku kuwa, kwanaki na bama aliyu sako ya kawo maki fatan dai an sayo maki komai da kike buqata ragowar wanda ba ah cinye ba kuma kin aikama uwar badaru ko ?,... kallonshi kaka binta tayi sannan tace "eei ankai mata sauran sannan aliyu ya kawo min sabbin buhunhuna allah yayi maka albarka dannan,'' kowa ya amsa da ameen... nan ne tsigai ta kawo masu lemu da ruwa daga firjin dakin mama binta, ganin an faara salla yasa kowa ya shiga daga cikin domin yin salla, dakuna hudu ne acikin dakin kaka binta, daya dakinta sauran kuma nasu ne idan sunzo, wanda daya kareema da yayanta ne ke shiga shikuma dayan labiba da nata sannan dayan kuma su ishaq ne suke kwana daddy kuma hotel yake zuwa ya kwana har su koma gida kano.

QueenMarh✍️
08032542629

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now