Ganin hankali kowa yayi gaba yasa su amra da kannenta fitowa suka wuce dakin mahaifiyar babansu wato kaka larai, koda suka shiga baiwar allah tana bakin murhu duk tsufanta wanda akalla zata bama binta shekaru kusan bakwai amma ita da kanta take komai,...suna shigo wa tsakar gidan da gudu sukaje suka rungume kakar tasu, allah sarki farin ciki ya cika kaka larai ganin jikokinta saida suka gaggaisa sannan ta jasu har dakinta wanda dakuna biyu ne kawai aciki,sallah kawai sukayi bayan sun kammala ta zuba masu abinci sukaci suka koshi, hira sukayi sosai da jikokin nata wanda idan ta kallesu take tunawa da badarun ta bawan Allah. Da daddare kuwa amra ce ta dafa masu taliya jollof sukaci suka koshi sannan sukayi kwanciyarsu, kwanan su goma chur suka tattara suka dawo kano. Kwanci tashi abin babu wuya awurin Allah hutun makaranta ya kare har sun koma school, su amra kuma
an fara preparation na waec da neco, amra dadi kamar zai kasheta amma kuma tana baqin cikin rabuwa da kanneneta idan ta kammala school, sbd zasu sha wahala sosai daman itace ke karba masu duk wani punishment da za ayi masu na lattin makaranta.
Akwai wata ranar laraba da suka je makaranta
bayan an tashi sun zauna jiran habu driver kusan awa biyu suna zaune shuru babu habu ga yunwa na nuqurqusar su har aka fara kiraye kirayen sallar magrib suna zaune ganin haka yasa hankalinsu ya tashi sosai gashi babu kudi ajikinsu balle su nemi abin hawa, ganin har kusan karfe takwas yasa hankalin amra tashi ga salim yanata murqususun yunwa haka yasa ta yanke shawarar su fita bakin titi dama a gate din school suka tsaya don babu kowa acikin makarantar duk an tafi sai mai gadin school din wanda ko naira goma baza su samu awajen shi ba, tafiya suka danyi mai nisa lokacin Har garin ya soma duhu sosai don ko abin hawa ma ya gagara sbd titin makaranta kamar waje wajen gari take, ganin sun galabaita sosai yasa suka tsaya bakin titin,suna nan tsaye wani mai mota yazo ya gifta ta gaban su, Har yayi gaba sai kuma yayi reverse ya dawo, ganin tsayuwar moto a gaban su yasa suka dan tsorata sbd rayuwa babu tabbas, fitowa matuqin yayi daga moto ya zo har gabansu, kallon Shi sukayi gaba dayansu hannayensu sarqe dana juna kamar za'a raba su.
Saurayi ne dogo akalla zaikai sa'an ya Ibrahim amma shi wannan fari ne, shima ganin su awaje kamar haka ya bashi mamaki shiyasa ya tsaya don yaji ko taimako suke nema gashi ya gansu da uniform. Kallon da yaga suna mashi ne ya sanyashi murmushi yace,'' hey boy me kukeyi anan kaida sisters dinka'' ...kallonshi salim yayi sannan yace '' driver ne ya manta mu baizo ya dauke mu ba'' .. tausayi suka bashi ganin yanda suke tsayuwa da kyar... anatse ya soma magana yana kallon amra ''idan ba matsala kuzo na sauke ku agida", da sauri salim yace "zamu bika''.. bude masu motor yayi sannan suka shiga duk sun takure suna qanqame da juna,saurayin kuwa daya dauko su idonshi nakan amra wadda ta lumshe idanunta kamar mai bacci,,haka kawai yaji ta burgeshi yarinyar domin yaga alamun nutsuwa atare da ita, ahankali suke tafiya har suka iso gida wanda duk salim ne ke yi mashi kwatancen gidan, koda suka iso gidan godiya sukayi mashi sannan suka fara fitowa daga cikin motor din, dai dai nan wata haddaiyar honda ta kunno kai har gaban gate din, habu driver ne ke tukawa sai wani abayan motor wanda ba ah ganin fuskarshi sbd motor akwai tint ta baya, horn Habu yayi sannan mai gadi ya wangale gate din, parking yayi ah wajen da suke parking motocin gidan, su amra kuwa basu tsaya ganin wanda ke cikin motorn ba suka wuce hanyar da zai sadaka da main door, jin muryar ya abdul
-wahab yasa suka tsaya ''kai kuzo nan,'' ahankali suka fara takowa har gaban motorn wajen inda yake zaune ya bude kofa ya zuro kafanshi dake sanye da loafers baqaqe kasa, kallonsu yayi daya baya daya, sannan ya sauke idonshi akan amra yace '' ke uban waye ya sauke ku yanxu nan, kuma maisa sai yanxu kuke dawowa daga school?" Shuru sukayi suna sunkuyar da kansu, ganin sun tsaya suna mashi zuru zuru da ido yasa ya daka masu tsawa, a furgice gaba dayan su suka kalleshi, amra ce tayi kokarin tattara natsuwarta sannan tace ya wahab ba'azo daukan mu bane muna zaune har akayi sallar magrib,'' shuru yayi chan kuma yace "shikuma wanchan daya kawoku fah?" ..da sauri salima tace yaya ya ganmu ne akan hanya shine ya taimake mu ya kawo mu gida" ..girgiza kai kawai yayi sannan yace "kuje",... da sauri suka wuce cikin gida, shi kuma yaa juya ya kalli habu yace "kai wake dauko yaran nan?" Atsorace habu yace "nine yallabai", .... "meysa baka dauko su ba yau?" Kallonsa habu yayi yace ''bayan na sauke su ishaq da rana shine hajiya tace wai na wuce airport na jiraka sbd bakason jira"
Murmushin gefen baki yayi sannan yace "good" fitowa yayi daga motor ya nufi cikin gidan direct yah hau sama part dinsu, dakinshi ya wuce dake cikin part din mamansu ko zuwa gaisheta tsaya yayi ba saida ya wuce toilet ya sakarma kanshi shower sannan ya fito ya sanya jallabiya dama already sunyi sallah ah masallaci akan hanyansu na dawowa daga airport, fitowa yayi ya wuce dakin mummyn su inda ya sameta tana zaune gefen gadonta tana waya, waje ya samu ya zauna akan kujerar dake gefen gadonta, saidata kai karshe wayan sannan tace, "hajiya madina bari na kiraki anjima kadan" sannan ta aje wayan, tana fuskantar shi, ''mummy ina wuni na sameku lpy" ya fada yana kallonta, murmushi tayi sannan ta ce "ya hanya kai iso lpy wahab?" amsa mata yayi da alhamdlh,
...kusan minti biyar shuru babu wanda yayi magana sbd akwai dan kunya tsakanin su ta dan fari, sun dauka kusan five minutes sannan ya kalleta yace ''mummy naga yaran uncle sai magrib suka dawo yau meysa ba'asa dayan driver ya dauko suba?'' tabe baki tayi sannan tace ''dazu danasa habu ya dauko ka saina manta ma da sha'anin su Akwai matsala ne?"...sunkuyar dakai yayi sannan yace ''okay mum'' sannan ya tashi yayi mata sallama, direct hanyar kitchen ya nufa lokacin around 10 na dare, koda ya shiga ciki domin daukan ruwa sai yayi kicibus da mutun,amra ce sanye da doguwar riga ta barci, rigar ta dan zauna ajikin ta, kallonta yayi da gefen ido sannn ya kauda kanshi gefe, jin motsin mutun akitchen din yasa ta juyo domin ganin waye koda ta ganshi tsaye yasa tasha jinin jikinta har yau idon ta kalleshi babu abinda take tunawa da abubuwa da dama, Akwai wani lokaci daya dawo nigeria ya umarci da takai kai mashi abinci bedroom dinshi anan ne tsautsayi yasa ta zubar mashi da abincin sakamakon ayaba dayaci ya yar ta taka, sulbin ayaban yasa ta fadi ta zubar da abuncin shikuwa yayi mata dukan tsiya dukan da bai taba yima kowa agidan ba aranar ne ta tabbatar da yayan mama kareema bazasu taba sonsu ba, bayan ita ma ya taba gaurawa salim mari akan wani laifi da bai taka kara ya take ba. Koda taganshi ya tsaya wajen fridge saita dan rissina ta gaisheshi, atakaice ya amsa mata sannan ya fice.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomanceAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...