27&28

126 3 0
                                    

Ta bangaren wahab kuwa ya tsorata muraran, sbd ya tuna akwai wani lokaci da lalurarta ta tashi ya kirata dakinsa da niyar lalata da ita lokacin ma ko qirgen dangi bata fara ba aikuwa duk kankantarta tayi mashi dan banzan duka gashi shedanun basu da Imani basaso abata mata rai tunda ga ranar bai kara shiga harkarta ba har ya koma kasar waje, toh yauma gashi an tapka abin kunya... abinda abdul wahab bai saniba shine, tun lokacin da hakan ta faru tsakaninsu bata kara yin lalurar ba dalili kuwa shine akwai lokacin da kaka larai tazo ganinsu, a lokacin ne ta kawo mata wani magani wanda tunda tayi amfani dashi bata kara rashin lapiyar ba.
Da kyar ya fito daga toilet din yana leqe leqe, saida ya tabbatar bata dakin sannan ya futo ya kulle dakin ya kwanta hankali a tashe.

Washe gari kuwa normal ta tashi suka shirya da kannenta da wuri domin yau zasu fara CA test sannan kuma asatin ne zasu fara rehearsal na wani competition da za suyi da Turkish international school wanda shima kafin azabi school dinsu saida akayi yi competitions tsakanin schools din dake jahar gaba daya kuma alhamdlh an zabi school dinsu da wasu makarantu biyu wanda zasu kara da Turkish international school din, kuma duk wanda yaci acikin student din any of the school yana da gagarumar kyauta wadda sai alokacin competition din za ah fada. Amra nada kwazo sosai domin duk class dinsu itace ke zuwa ta biyu, inda zatafi burgeka shine kwakwalwar ta tafi ja wajen karatun addinin musulunci, idon tana karatu bazaka so ta daina ba. Yau test hudu kawai sukayi sannan aka tashe su, koda suka koma gida yau ma kamar kullum babu abinda sukayi suna zaune adakinsu ganin ma zaman bazai yuwu ba yasa suka fito backyard domin yin wankin kayan su,

Zama sukay a bakin fanfo ita da salima, ita ke wankewa salim yana daurayewa, salima kuma tana shanyawa, suna cikin wankin sukaji saukar motorn dady da tasu Ibrahim.

Bayan sun gama wankin suna cikin tattara buckets din da sukayi wankin dashi saiga khady ta biyo ta kitchen, tsayawa tayi tana kallonsu, wani tunani ne ya fado mata ta koma cikin gida sannan ta fito hannunta dauke da undies dinta, tana zuwa dab dasu ta watso masu undies din,

kallonta salima tayi afusace tace ''malama meye haka kika watso mana kayanki''...ko kallonta khady batayi ba ta kalli amra sannan tace "ku wanke min su yanxu, sannan kijama wannan mara kunyar qanwar taki kunne niba sa'ar tsarar ta bace ko kema kinmin kadan ke hatta uwarku ma'' ...jin haka yasa salima daukan ragowar ruwan da suka tsane kayan datti zasu zubar ta watsa ma khady ajiki, a qule ta fara magana ''idan zaki zagemu ko zaki ci mutunci mu kiyi amma karki kuskura karki sake kice zaki zagi iyayen mu'' kallonta kawai khady tayi sannan tace ''ayau yau dinnan ba gobe ba saina ci ubanki sannan saina nuna maki cewa ku ba komai bane face yayan riqo'' aguje khady ta tafi bakin bishiyar tsakiyar backyard din gaban gidan ta buga Ma kanta sau biyu har saida jinni ya tsatso sannan ta wuce ta gabansu tana kecewa da dariya ganin haka yasa hankalin amra yayi matuqar Tashi ta maida kallonta ga salima ta fara Magana ''yau mun shiga uku salima kin jawo mana bala'i innalillahi, salima na fada maki kome zasuyi mana ki daina tankawa amma ke bakyaji yanxu allah kadai yasan mai zataje tace Munyi mata..'' jikin salima ne yyi sanyi tabbas tayi nadamar biyewa khady, yanxu watan cin ubansu ya kama ganin haka yasa amra kwasar undies din ta fara wankewa saidata wanke tass har an kira sallar ishaï sannan suka dunguma suka shiga ciki basu tadda kowa ba aparlor hakan yadan kwantar masu da hankali, daki suka wuce direct sukayi sallah sannan suka zauna kowannen su ya zabga tagumi, suna nan zaune sukaji saukar motorn daddy dasu iya Ibrahim da wahab, ganin haka yasa hankali amra ya sake tashi.

Suna nan zaune har salim yayi baccin wahala tsabar yunwar da yakeji amma yana tsoran fita ya karba wajen mama rabi ita kuma yau tun bayan sallar magrib ta kwanta sbd wani irin zazzabi daya rufeta.
Hayaniya suka fara jiyowa a parlour hakan yasa hankalinsu ya tashi matuka, tashin hankalin da ba'a sa mashi rana, suna nan zauna aka banko kofar salim agigice ya tashi, ya Ibrahim ne ya shigo idon nan nashi babu kyan gani, fadowa yayi dakin gadan gadan sannan ya damko hijab din salima ay kuwa me zasu yi banda innalillhi, babu abinda amra ke fada sai "dan Allah kuyi hkuri nice na nayi musayar yawu da yaya khady don darajar Allah kuyi hkuri'' ..baiko saurareta ba yaja salima har tsakiyar parlor inda su dady da mama kareema da khady sai wahab suke atsaye kowannen su fuskarnan babu annuri Sai faman furzar da huci suke kamar sunje yaqi,

khady kuwa tana lafe akan kujera tana nishi kamar wadda keyin naquda, ganin anja salima waje yasa amra kallon salim sannan tace duk abinda zai faru karka sake ka fito kaji salim" amsa mata yayi da toh sannan ta saka kai ta fice.
Karasowa tayi daidai inda aka wanchakalar da salima wanda idonta ya cuko tab ta kwalla kallonsu daddy yayi sannan yace "don ubanki badaru me Khadija tayi maki kika fasa mata kai? ''shuru sukayi chan amra tace daddy wallahi bamu fasa mata kai ba itace ta.... Karaf kareema ta tari nunfashinta tace "don ubanku karya zata maku inace taje ta sameku kuna wanki tace ku taimaka ku wanke mata undies dinta shine kuka zagi ubanta kukace bashida Imani sannan kuka buga mata kanta iye?' jin irin karyar da aka shirya masu yasa salima cewa ''mai karya dai dan wuta ne'' kallonta daddy yayi sannan yace "dan ubanki badarun matsiyaci waye yake maki karya iye, toh kuwa yau zaki gane kuskurenki.. kai ibahim ka kaita storage room karka fito saika tambatar da ka balle hannun mara kunya kafin ka fito'''jin haka yasa azafafe Ibrahim ya dunga janta kamar dabba har storage room, hankalin amra fa ba karamin tashi yayi ba za'a illata yar uwarta ay kuwa aguje ta bishi kafin ta karasa ma ya rufe kofar storage room din, babu abinda yake sai jibgar salima tun tana rokonshi da Allah ya kyaleta harta sume, saida ya tabbatar ta jigatu sannan ya fito ya rufo kafar yasa key din a aljihun sa, kuka dai amra tayi kuka harta godema Allah, su kuwa kowannen su wucewa part dinshi yayi hankali kwance.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now