29&30

133 4 2
                                    

Bangaren salima kuma sumewa tayi dalilin bugun cikinta da ya Ibrahim yayi tun daga lokacin ta fita hayyacinta. Amra kuwa annan zaune bakin kofar ta zauna zaman dirshen tana kuka tana rokon Allah akan ya tsare mata yar uwarta, gashi storage room din ana dadewa ba ayi amfani dashi ba don babu komai aciki sai karafunan motoci da tsofaffin gas cylinders da aka gama amfani dashida ake ajewa idan sun tsufa. Anan suka kwana har safiya amra bata samu damar koda rufe ido ne ba babu abinda take sai kiran salima amma shuru, tsoronta kada ace kashe mata kanwarta sukayi, karshe dai dakin mama rabi mai aiki ta wuce lokacin tana kan sallaya tana lazimi batasan wainar da ake toyawa ba, ganin amra ta fado dakinta kamar wadda ta susuce idonta yayi rudu rudu tsabar kuka yasa ta mikewa tace ''ke amra lapiya meya faru?'' hankali atashe amra ta labarta mata komai sannan tace mama rabi sun kashe ta sun kashe min yar uwata na shiga uku.

Saida mama rabi ta kwantar mata da hankali sannan tace inada extra key wanda ake barmin sbd ijewar kayan da suka lalace bari na dauko muje mu bude ta, cikin sauri mama rabi ta lalubo key din suka wuce direct dakin, suna budewa kuwa hankali atashe suka ciccibi salima wadda har yanxu bata farfado ba,jikinta duk ya kumbura hawayen fuskarta harya bushe, daki suka wuce da ita anan mama rabi ta dakko ruwa ta yayyafa mata aikuwa tana bude idonta ta fara kuka muryarta adishe ta fara sammabatu "adda wannan wace irin masifa ce maysa baku bari na mutu ba, adda kashemu mutanen nan zasuyi basa son mu innalillahi''

Rungume ta amra tayi, hawaye sharr afuskarta, dakyarta lallashi kanta sannan daga salima da taimakon mama rabi  ta wuce da ita toilet saidata gaggasa ta sannan suka fito daki, kaya ta dauko ta saka mata sannan ta kwantar da ita, kitchen ta wuce ta hado mata tea me dan kauri ta bata saidata tabbatar ya shanye sannan ta dauko pain killer da suke ajewa a locker sannan ta bata. kallon salim tayi wanda ya gama takurewa da alamun da yunwa ya kwanta yasa taji tausayi yan uwanta duk ya rufeta, Har lokacin hawaye bai daina saukowa daga idanun ta ba,saidata taimakawa salima tayi sallah sannan ta kwantar da ita, ta jawo mata bargo. Tashin  salim tayi wanda duk ya takure agefe guda tayi domin suyi sallah koda suka idar shima tea din ta hado ta bashi yasha, kwanciya sukayi basu tashi ba sai wajen nine saboda rashin baccin da basu samu sunyi ba, ganin lokacin school ya kure yasa suka fasa kawai daman taso salim shi yaje school din ita kuma ta zauna ta kula da salima.
Wunin ranar adaki sukayi tsabar mugunta babu wanda yabi ta kansu, tunawa da kayan wankinsu yasa amra ta tashi inda tabar salima na barci salim kuma yana home work sannan ta wuce backyard. Tana karasowa ganin kayansu akasa yasa ta fara kwashewa tana cikin kwashewa kuwa khady tazo har inda take sannan ta fara kecewa da dariya, kallonta kawai amra tayi irin kallon ina tausayawa karshen ku.

Kallonta khady tayi sannan tace ''ai na fada maku niba tsarar yinku bace, kalli dai dan buga kaina da ni da kaina nayi ya janyo kun kusa salwantar da kanku, hahaha ina tausaya maku amra haka zakuyi ta wahala agidannan har karshenku, sannan zan kara warning dinki akan kiyima mara kunyar kanwarki magana don wallahi idan har tayi wasa zaman gidan nan zai gagareta, yanda na tsaneku haka na tsani mutuwa ta, bakuyi min komi ba amma bana qaunarku samm" tsaki taja sannan ta kara gaba, amra kuwa kallonta kawai tayi sannan ta cigaba da abinda take ta wuce dakinsu .

Jikin salima kuwa ya warke har sun koma school saidai kullum saitayi kukan ciwon ciki ana haka har suka fara exam din waec Sukuma su salima har sun gama exam sun fara hutu, haka kullum zata shirya ita daya ta tafi school tana gama exam kuma ta dawo gidan abinta, yanxu kam ta tsaya sosai akan kannenta, bata bari su shiga damuwa sannan ta tsaya masu sosai. A kwana a tashi babu wuya yau saura kwana biyu su gama paper, yau da gobe Tuesday da Wednesday Kenan sai on Saturday kuma zasuyi grand competition next week kuma za ayi walimar saukar yan ss3 wato su kenan, abubuwan sunyi ma amra yawa ga karatun waec ga preparation na competition, haka dai ta dukufa da karatu.
Yau Wednesday suka shiga last paper duk yan class dinsu kowa farin ciki yake za ah gama exam, bayan sun gama first paper amra ta fara jin ciwon baya kadan kadan, chan anjima kafanta ya rike jin haka ya tabbatar mata da period zatayi dama a day before ta fara alamun haka ke bayyana ajikinta, lallabawa tayi ta koma class har suka fara second paper wanda shine last one, gaba daya ta takure ahaka dai tayi managing kanta har suka gama sannan ta fito ta wuce gida, koda ta iso har zazzabi ya fara rufeta daki kawai ta wuce tayi wanka ta chanza zuwa simple riga da skirt, tana nan zaune salima ta kawo mata abinci taci sannan sukayi sallah.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now