35-38

120 4 0
                                    

Washe gari Monday da kyar salima tasa amra ta amince domin zuwa school ta karbo kyaututtukanta dukda tace bazata karba scholarship ba.
Futowa tayi haladu ya dauketa har school dinsu, ba laifi da akwai mutane a school din wanda rabi teachers ne, wucewa tayi wajen head office bayan tayi sallama, kallonta mrs abida tayi fuskarta dauke da murmushi sannan tace ''my beautiful student, I'm so proud of you my dear zoki zauna kinji''... samun guri amra tayi sannan ta gaisheta sannan ta fara mata bayannin cewa bazata karba scholarship ba, tambayrta mrs abida tayi dalilinta, nan ta shaida mata cewa bazata iya tapiya tabar kanneneta ba, sanin irin rayuwar da su amra keyi ah gidan ruqonsu yasa mrs abida ta gane  inda zancen amra ya nufa,

nunfasawa kawai tayi sannan ta fara Magana '' amra inason kisan cewa karatunki yana da matukar amfani bake kadai bama harda kannenki, kece uwarsu kece ubansu yanxu idan baki nemi ilimi ba dame zaki taimaki kannenki harsu dogara dakai, shawara zan baki kamar yanda uwa zata bama yarta, idan har kinason cire kannenki daga rayuwar da kuke ciki to ya zama dole ki tattara courage dinki ki natsu ki kwantar da hankalinki, ki karba scholarship dinnan, dama ce kike samu don wallahi idan kika bari ta kufce maki bazaki kara samun kamarta ba, shawara ce na baki, sannan if you're worried about siblings dinki, Allah yana tare dasu koda kina nan ko baki nan idan har abu zai samesu toh duk isarki duk karfinki bazaki iya hanawa ba, sannan nima zan taimaka maki wajen kula da kannenki da harkar iliminsu kinji ko''
girgida mata kai tayi alamun gamsuwa sannan tace to shikenan ma''..
sundan tattauna daga bisani ta bata check dinta na 2m da cash sai latest iphone xmax dinta, godiya amra tayi sosai, daga bisani mrs abida tace ''kije kiyi shawara sannan ki fada ma mai riqonku duk yanda kika yanke saiki dawo koki kirani awaya sai mu fara processing komai kinji ko'' godiya amra tayi mata sannan ta wuce ta koma gida.

Wunin ranar da tunani batun scholarship dinta ta wuni daga karshe ta yanke shawarar tunkarar daddy tukunna idan ya amince fine idan ya hana babu yanda zatayi don shi ne wanda kawai zaiyi sponsoring upkeep dinta.

Dare nayi wajen karfe tara bayan ta daidaici lokacin hutawarsa sannan ta wuce sama domin ganin daddy, ahankali tayi sallama yana zaune sitting room dinshi shi kadai yana cin dambun nama yana kallon news, ahankali ta kutsa kai ciki, bayan ta gaisheshi sannan tadan nunfasa ta fara Magana '' daddy daman munyi end of the year competition a school dinmu kuma nice na zo gwarzuwar shekara sannan na samu scholarship da kyaututuka''... kallonta yayi sannan yace ''okay''... shuru ta danyi sannan tace ''daddy daman naga tunda wannan opportunity ne mai kyau yasa nace bari naji ta bakinka ''... kallonta yayi sannan yace ''are you planning on accepting the schorlaship?"girzigiza mashi kai tayi sannan yace ''okay to naji harda accommodation ko? To shi kuma expenses dinki kuma fah da upkeep waye zai baki ko kudin da suka baki zai Isheki shekarun da zakiyi? Shuru tayi sannan tace ''daddy daman ina neman taimakon wannan awajen ka''... kecewa yayi da dariya sannan yace zan iya taimakon ki yar badaru amma bashi zan baki,saboda dawainiya da nayi daku kawo yanxu nayi na Allah yanxu kuma lokacin biyan bashi yazo'' shuru tayi hawaye na bulbulowa afuskarta wai wannan wan mahaifinta ne mafi soyuwar babanta'' shuru tayi daga nan kuma wata jarumta tazo mata lokaci guda ta kalleshi har cikin idonshi tace ''na amince duk abinda kayi mana zan biyaka koda kuwa zai zama karshe nunfashina, saidai alfarma daya inason kannena su kasance kamar kowa agidan nan". Tana kaiwa nan ta fuce, kwata dady yayi aranshi yana Kara jin tsanar yaran.

Amra kuwa Daki ta dawo inda ta samu salima nacin goruba anatse amra tayi mata bayanin amincewar ta wanda hakan ba karamin dadi yayima salima ba saidai bata gaya mata yanda sukai da daddy ba.
The next day,
Tana tashi ta kira mrs abida a yar wayarta ta shaida mata komai, mrs abida taji dadi sosai da amra ta yarda, nan mrs abida ta shaida mata cewa zasu fara processing passport dinta inda ta umarceta data zo school on Monday don ta kaita ayi mata passport, godiya tayi mata sannan sukayi sallama.

Komai dai yana tafiya daidai don har anyi ma amra passport yanxu visa ake jira saidai hankalinta atashe yake jin anytime visa ya fito za'a saya mata ticket daman already an shigo new year.

Yau visa amra ya fito sannan ayau ta fara processing komai na makarantar da zataje wato Middlesex university dubai inda zata karanta nursing, an shirya mata komai harda accommodation tana isa chan school kawai zataje tayi registrating sannan sai lectures.

Allah sarki amra za'a shiga sabuwar rayuwa........😭

Something is waiting for amra, this is just the beginning, Amra is approaching her destiny.........................✍️



Yau saura kwana biyu tafiyar amraa,tana kwance agadon su babu abinda take sai tunanin tafiya, yanxu shikenan haka zata tafi tabar kannenta, wazai tsaya masu, waye zai kula mata da su, kuka ne ya kufce mata, jin sallamar ishaq yasa ta saurin goge hawayen daya zubo mata,
kallonta yayi sannan ya shugo fuskarshi dauke da murmushi yace '' sis nazo nayi congratulating dinki daxu nakejin salima da mama rabi suna hirar ah kitchen, yanxu sis ni baki daukeni dan uwanki bane banida darajar da za ah fada min wannan kyakkyawan labarin na tafiyar ki school, gaskia banji dadi ba sis'', mumushin yaqe amra tayi sannan tace
''I'm so sorry bro, wallahi duk na shaáfa ne duk tafiyar ya fita kaina, ishaq bansan ya zanyi ba inajin tsoron barinsu salima su kadai, ishaq dan Allah ina neman alfarma awajen ka don Allah idan bana nan ka kula min da kanne na nasan kai kadai ka damu da walwalar mu''

takai karshe hawaye na zubowa akan fuskarta, lallashinta ishaq yayi sannan yayi mata alqawarin zaiyi kokari wajen kula da kannenta, sallama yayi mata sannan ya fuce.

Shugowa dakin salima tayi da sallama sannan tace adda ki tashi mu shirya mu tafi domin ki samu ki bude account din sannan mu wuce kasuwan. Kasuwa sukaje inda anan amra ta sayama kanta kayan barci sabbi dasu bra da panties daidai kudin su masu arha sannan tayi ma su salima yan kananun sayayya wanda zaiyi masu amfani koda ace batanan, duk wannan hidimar da kudinda ta samu sukayi, wucewa sukayi wajen masu abayas, anan ta saya kala biyar masu kyau daidai kudinta, sannan suka wuce bank domin bude account, daganan suka tsaya shagon wayoyi na zamani anan ta bada karamar nokia ta cika da kudi suka musanya da android mai kyau domin tanason ta barma su salima domin jin lafiyar,wunin ranar awaje sukayi shi.

Bayan sun koma gida sai alokacin ta tuna da sabuwar wayarta wadda tundo tazo da ita ta aje while kudin da ta samu wanda aka bata cheque dinshi ta bama mrs abida ta aje mata
ko zata buqata nan gaba ko kuma idan kannenta zasu buqata dukda an diba kusan rabi wajen yi mata visa da flight ticket.

Yau thurday gobe Friday jirginsu zai daga wajen karfe uku na rana, kwata kwata bata cikin nutsuwarta lafewa tayi akan gado zazzabi yana neman lullubeta, salima kuma tana zaune tana shirya mata kayanta ah cikin akwati, saida ta hada mata komai duka yan kayayyakin ta sai yar jakar da ta saya mai chain guda biyu masu kyau da abayoyin da ta sayo, bata wani kwasa wasu kaya masu yawa ba.
Suna nan zaune taji shugowar daddy saida ta tabbatar ya huta sannan ta wuce sama part dinshi, kodata shiga yana nan zaune kamar kullum yana waya, karasawa tayi saida ta bari ya gama sannan suka gaisa nan ya miqa mata wasu papers yace tayi signing, karba tayi ya fara signing bayan ta gama ta miqa masa,
Karban papers din yayi yana murmushi ya bata wani envelop yace '' first upkeep dinki ne wannan na rubutashi acikin contract da kikayi signing yanxu sannan duk sanda kika buqaci kudi zan baki idan har kika gama makaranta baki biyani ba acikin gadon ku Zan dauka wato gidan ubanku wanda yake Abuja a maitama''

kallonshi amra tayi afurgice sannan tace ''amma daddy ba haka mukayi dakai ba, baka cemin zaka musanya yarjejeniya da gidan gadon mu ba shi kadai muka mallaka ni da qannena ,''  baiko kalleta ba yace zaki iya tafiya

kuka ne ya kufce mata kawai ta fice daga dakin.
Koda ta koma daki saita fara dana sanin amincewa da batun biyan bashi da dady yace zatayi ashe tun farko manufarshi Kenan abinda yakeso, shiyasa yayi sauri ya amince da tayi mashi maganar school din, kuka kawai take yi koda salima ta shugo ta ganta saitayi tunanin kukan tafiyar da zatayi ne gobe, zama tayi gefenta tausayi yayarta ya gama lullubeta, rugume juna sukayi sai kuka, jin alamun shugowar salim yasa suka tsagaita don kar ya gane me suke ciki gudun karya shiga damuwa sbd ciwon zuciyar shi, Haka suka kwanta rungume da juna.
Cikin dare kuwa amra kamar an tsikareta ta fara jn wannan ciwon bayan nata dai alamun zata fara period dinta, tashi tayi ta nema Panadol kawai tasha, cikin ikon Allah barci ya dauketa.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now