39-41

145 4 0
                                    

Koda ta tashi da safe da ciwon ciki ta tashi kadan kadan kuma yau ta kasance ranar tafiya, anatse take yin komai don duk jikinta yayi sanyi, karfe bakwai daidai ta wuce toilet, tayi wanka sannan tazo ta zauna gefen su salima wanda bancin su kawai suke, zuba masu ido tayi sannan tace ''kannena banida kamar ku duk duniyar nan, zanyi kokari nayima kaina alkawari zan kula daku kuma insha Allahu zanyi ilimi na fitar daku daga qangin rayuwar nan insha Allah, salima wadda tashinta Kenan ta bude idununta ta kalli yayar ta wadda qwalla shar akan fuskarta tace ''adda dan Allah ya kamata ace kin daina koke koken nan saikace mutuwa zamuyi idan kika tafi, nayi maki alkwari wallahil azeem bazan taba yin abinda zaisa ki damu ba idan kika tafi, zan kula da salim zan zama uwa agaresa zan kula dashi kinji adda kidaina damuwa dan Allah"... dakyar salima ta lallashe ta sannan itama ta wuce don tayi wanka.

Bayan salima ta fito,kimtsawa itama tayi sannan suka wuce kitchen, a tare sukayi breakfast da mama rabi inda tayi ma amra fada akan ta kula da kanta da mutuncin ta sannan tayi Ma amra alkwari kula dasu salima.

Daki suka koma nan salima ta tashi salim ya shiga wanka ita kuma amra ta dauko sabuwar wayar ta sannan tayi exchanging number da sabon sim din data sayama su salima, ganin karfe sha daya saura yasa ta saka sabuwar abayar ta sannan ta wuce sama domin yima masu gidan sallama, koda taje part din haj kareema batama tsaya ta saurare ta ba ta koreta, fitowa tayi ta wuce part din Haj labiba, koda taje bangaren haj labiba kuwa, ba laifi tadan kulata hardasu Allah ya kiyaye,...direct kasa ta sakko abinta sannan ta koma wajen salima koda ta shiga dakin azaune ta ganta, hannunta dafe da cikinta, karasowa tayi tana tambayarta ko bata da lafiya, ganin hankalin yar uwarta zai tashi yasa salima saurin yin yaqen wahala tace ''laa adda dan period pain ne yama daina''....magani amra ta bata tasha sannan itama ta shirya cikin atampa yellow doguwar riga. Wardrop dinsu amra ta bude nan taga envelop din da dady ya bata, daukar envelop din tayi sannan ta bude, kudi ne aciki dollars wanda akalla zaikai 5k dollars ajiyewa tayi aciki yar chain handbag dinta sannan ta dawo daki ta zauna, suna nan zaune ishaq yazo suka dan taba hira bayan kiran sallar zhuhr ya wuce masjid su kuma suka tada kabbarar sallah, saida suka idar sannan sukayi addua ita da kannenta, salim kuma ya fara kiciniyar fitar mata da akwatinta, lokacin it's about 2pm batason tayi latti shiyasa ta shirya futa da wuri sbd flight din Karfe uku ne. Koda suka fito bayan sunyi sallama da mama rabi harda yan hawayenta sannan ta bata farar kasar data saya mata don kartayi kewa sannan suka karasa wajen haladu driver, shiga cikin napep din sukayi saiga ishq, shima shiga yayi domin yin rakiya.
Direct Aminu kano international airport suka wuce inda anan suka hadu da mrs abida wadda zata bata passpost dinta da visa dinta da komai na school, godiya tayima mrs abida sosai saboda tayi mata qoqari sosai sannan ta juya wajen kanneneta, salim wanda idonshi ya ciko da kwalla ya kalleta yace ''addana yanxu tafiya zakiyi ki barni ko'' kallonsa tayi cike da kauna da kewarsa sannan tace '' my salim karkayi kukakaji ko I promise to buy you a big army jet toy and I will come back soon so that I can bring you and salima kaji ko ''... dariya yayi jin tace zata dawo ta tafi dashi, kallon salima tayi sannan tace ''salima dan allah ki kula kinji, ku dinga kirana idan kuna buqatar wani abu sannan ga ishaq nan zai kula daku kinji sannan duk wani abu dake damunku ga mrs abida ga mama rabi ga ishq na tabbatar zasu kula daku''... rungume kannenta tayi sannan ta sakesu ta wuce da sauri cikin airport din sbd hawayen dake shirin zubo mata don idan Har ta tsaya suka fara koke koken nan toh fa tafiyar nan bazata yiwu ba ganin kusan Karfe uku ta kusa yasa suma suka wuce gida kowannan su dauke da kewar ta,... ita kuwa amra kuka sosai takeyi harta iso counter din emirates, anatse ta gama komai ta wuce da luggage dinta, abinma yazo mata da sauqi sbd sun taba tafiya lokacin iyayensu na raye lokacin sunje morocco wajen uncle din mamansu. Koda ta wuce ciki wuri ta samu ta zauna domin jiran jirginsu, ko five minutes batayi ba da zama aka kira jirginsu nan kowa ya Tashi domin yin boarding saida suka gama tukunna suka wuce harabar jirgi, anatse take tafiya sanye da abayarta wadda suka sayo black, tayi mata tsam gata dama akwai diri sai tabi shape dinta tayi irin A shape dinnan tayi mata kyau sosai sannann tayi rolling kanta da mayafin abayar sai yar chain hand bag dunta akafada har suka iso cikin jirgi, seat dinta atsakiya yake nan ta samu waje ta zauna while gefenta is empty by right sannan left dinta kuma wani bayarabe ne.....Bayan Yan mintuna kadan jirginsu ya daga zuwa abuja domin transit zasu fara yi daga abuja su wuce uae.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now