saida ta dauka kusan 1hour before ta fara dawo wa daidai, amma har yanxu tanajin ciwon marar nan, amar kuwa wanda ya lumshe ido babu abinda yake tunawa sai fadan da sukayi da dan uwansa, har yana ikirarin sai ya zama karshensa,runtse ido yayi yana jin zafin irin qiyayyar da aman yake mashi, wani irin huci mai zafi ya furzar, zuciyarci babu abinda take sai tafarfasa, yana cikin tunanin nan ya fara jin shesheqar kuka daga gefenshi, mamaki ma ya gama hanashi tantace mace ke kukan ko namiji, ya dauka almost 10 minutes sannan ya fara jin kukan nata yana kara gaba, wani irin bal balin zafi ya dunga ji babu abinda kukan nan ke tuna mashi sai Amma, baya qaunar kukan mace ko yayane baya so ko kadan, ahankali ya bude idanunshi wanda sukayi jaa sosai bacin rai karara ya bayyana afuskarshi, kallon gefenshi yayi adurkushe yaga mutun, tun daga tsakiyar kanta wanda ta durkushe har gwiwarta, kallo daya yayi mata ya dauke kanshi, ganin kukan bamai karewa bane kuma babu alamun zatayi shiru yasashi saka airpod ya toshe kunnen shi ya kunna karatun qur'an , anatse yake sauraro har ya fara bin karatun, yana lumshe idonshi....
Jin melodious muryar dazu ya sanya ta tsagaita kukan anan take zuciyarta ta fara sassauta mata daman ciwon ciki ne ke nuqurqusar ta ga tunanin su salima duk shi yasata kukan nan, anatse take sauraron yanda yake karatu har yanxu bata dago baa haka har barci ya dauke ta a wahalce..... shima barcin ne ya dauke shi....sun dauki almost 2 hours suna bacci chan yaji dan nauyi akafadar shi, ahankali ya fara bude idanunshi da suka rine tsabar jin baccin bai ishesa ba, jin hannunshi yayi tsami yasa ya fara yatsine fuska,ahankali ya bude idonshi tarr akan ta, kwance take akan kafadar shi mayafin jikinta ya rufe mata fuskarta lokaci guda ranshi ya baci amai ya fara neman kakaro mashi, hankadeta yayi wanda yasa ta buge da gefen hannun kujerar, ahankali cikin barci tace ouchhh wayyo oum, tashi yayi a zafafe ya wuce bathroom, saida ya wanke fuskarshi sannan yadan samu nutsuwa, babu abinda yake ayyanawa aranchi face tunanin wacce mara hankali ce wannan zata kwanto jikinshi, babu abinda ya tsana irin mata mara aji, kwata kwata bai kawo cewa ba da saninta tayi hakan ba, amra kuwa baiwar allah, dalilin farkawarta ya dawo mata da matsanancin ciwon mara tun tana daurewa har kukanta ya fara fitowa sosai, jin haka yasa crews sukayo kanta, tambayarta suka farayi amma kwata kwata ta kasa Magana saidai nuni da take masu da cikinta, ganin nunfashinta na neman daukewa yasa suka firgice, wata crew ce ta wuce wajen announcement ta fara announcing emergency idan akwai doctor yaxo yayi taimakon gaggawa, allah ya taimaka kuwa an samu wani shahararren likita, dr Benjamin, har gaban amra ya karaso koda ya tabata yaji taba motsi yace akawo mashi ruwa domin ta suma, amar kuwa yana toilet saida yakai almost 10mins kafin ya fito ko kallon inda yarinyar take baiyi ba yadaiga mutane cirko cirko agabanta, kawar dakai yayi ya zauna yana lunshe ido,...saida aka dauko first aid akayi mata allurer bacci tukunna ta samu dan sauqi, oga amar kuwa tunda ya lumshe ido bai ko bude ba, koda akazo raba abinci kamar yanda ya umarta bayason special treatment babu wanda ya kawo masa, da akazo raba na yan economie kuwa ko kallon crew dinda ke tambaya mai za ah bashi baiyi ba.... 1hr later jirgin ya tsaya transit, bayan waenda zasu sauka suka sauka, saida aka gyara mashi inda ya buqata tun farko sannan aka sanar dashi, mac laptop dinshi kawai ya dauka sai wayar shi sannan ya bada umurnin adauko mashi baggage dinshi da brief case dinshi, sannan ya kara gaba ko kallon gefenshi baiyi ba daman duk atakure yake, first class ya wuce inda wajen yake nan kamar daki cikin nutsuwa yake komai nashi, saida ya rufe bangarenshi for privacy sannan ya zauna yana yan latse latse cikin laptop dinshi, tunda ya kafa kai yana danne danne har akayi landing, daman sai yan first class sun sauka tukunna Sai yan business sai yan eceonomie, anatse ya fita cikin isa, har gaban wata lexus bayan ya shiga aka fita dashi daga harabar jirgin. Amra kuwa ana chan ana shakar bacci saida kowa ya sauka ita kadai ta rage yasa wata crew ta tashe ta, ahankali ta bude idanunta, ganin anyi landing yasa ta mike, mamaki ne ya cika ta jin garau tajita babu ciwon cikin saidai dan blood flow data fara ji chan kasan ta, anatse ta fito har cikin airport din, owww wow, saida ta shaki iskar garin taji wani irin sanyi a zuciyarta, addua tayi yanda ta taka kasar garin Allah yasa ta tako da alkairi, anatse take tafiya har ta fito exit lokacin har safiya tayi wajen karfe bakwai da rabi na safe, garin is so peaceful,
Kiran airport taxi tayi sannan ta fada mashi inda zai kai ta wato Elvira apartment deira, anan ya shaida bata free ride ne sbd yau anniversary din sarkin garin na cika shekara arba'in da zama a kujerar sarki sbd haka yau komai free ne indai har na government ne.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomanceAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...