MEYE ILLATA?
Wannan littafin yay daban da saura. So idan da hali ki samu ki karanta zai miki amfani😊
بسم الله الرحمن الرحيم
Episode: 1
Duk wanda ya ɗaga kai ya kalli IDREES MUHAMMAD KANKIA a wannan lokacin sai yayi matiƙar jinjina ma dauriyarsa. Ba don komai ba sai don kasancewarsa jajirtaccen Namiji mai iya dannar zuciyarsa a duk lokacin da yake cikin tashin Hankali, duba da maganar da Bahaushe ke cewa labarin zuciya a tambayi fuska wannan yasa daga kallon farko zaka iya fahimtar Rauninsa gamida tsananin ɗaurewar kan da Edriss ke ciki.
Sai dai sam fuskar Idrees bata nuna kaso d'aya cikin d'ari na rad'ad'in da zuciyarsa ke masa ba.
Kotu tayi d'if jikin kowa a sanyaye saboda munanan kalaman da suke fitowa daga bakin BINTU wanda take jifan mijinta Edriss dasu. A duk lokacin da Bintu ta furta wata kalma sai idanu sun koma kan Idrees mutane da dama na mamakin "anya mutum mai cikar kamala irin Idrees zai iya aikata abinda Bintu ke fad'i a kansa?"
Share 'kwalla Bintu tayi yayin da ta gama she'ka 'karairayinta a kotu, ba wannan ne zama na farko da sukayi ba wannan shine zama na uku akan neman sakin da Bintu keyi daga Idrees, saidai hangen nesa da tunanin gaba irin na namiji yasa ya gaza bata takardarta ba don halayenta ba, sai domin darajar 'ya'yan dake tsakaninsu.
Duk wanda aka fara zaman wannan kotu dashi zai tabbatar da maganganun Bintu akwai 'karairayi a cikinsu, amma abin mamaki al'kalin sam baya duban wannan sai tsabar goyon bayanta da yake akan duk wata kalma da ta furta.
Bayan al'kalin ya gama rubuce-rubucensa ya juyo ga Idrees yace "zamu baka damar biko ta 'karshe...".
Kafin ta aje maganarsa Bintu tayi caraf tace "A'a ya mai shari'a banaso, ni wallahi a rayuwata na tsani ganin fuskarsa bana son ko sake had'a inuwa dashi, bana sonshi bana 'kaunarsa a tilasta mishi ya bani takardata".
Gyaran murya Al'kali yayi yace da Bintu "banaso ki sake magana idan ba ni na umarce ki ba". Sannan ya juya ga Idrees yace "na baka damar biko har sau biyu amma baka shawo kan matarka ba".
Gyara murya yayi ya bud'e baki cikin nutsuwa yace "nayi duk abubuwan da suka kamata kamar yanda ta fad'a, ina ro'kon alfarmar kotu ta tausheta ko dan darajar 'ya'yanmu".
"Wasu 'ya'ya? Daga kai har 'ya'yan idrees bana bu'katarku a rayuwata. Babu abinda zaku tsinana min farin ciki nake nema. Ka tattara gayyar tsiyar 'ya'yanka bana bu'katarsu takardar saki kawai nake nema. Wallahi ka sakeni ko kuma kai da farin ciki...".
"Ya isa!". Alkali ya furta tareda dafe kansa. Duk yanda yake ji da Bintu a yau tana nema ta caza mishi kai ta kuma nuna bai isa ba a wurin da shi kad'ai yake da ikon mulkarsa, dole ya nuna mata matsayinta kafin mutane su fara zargin wani abu.
Kafin yayi magana ta sake fashewa da kuka tana fad'in "na gaji da wannan rayuwar Idrees na gaji, shekara Ashirin ina fama da rayuwar 'kunci da takaici. Tunda na aureka ban samu farin ciki ba Idrees".
"Wai ba auren soyayya kukayi da mijinki bane?" Al'kalin ya tambaya yana gyara gilashin idanunsa, girgiza kai Bintu tayi tace "wallahi ban ta'ba sonshi ba asali ma auren dole aka min aka tilasta min aurensa, ban ta'ba jin d'igon sonshi a zuciyata ba ko da da 'kwayar zarra kawai ina zama dashi ne akan dole da kuma biyayya. Bana sonshi bana 'kaunarsa dan girman Allah a saka shi ya sakeni".
"Kaji idrees me zaka ce game da maganganun matarka?"
Takaici, kunya da mamaki ya hana Idrees magana, domin Bintu dai ba yarinya bace balle kace rud'in zamani da na 'kawaye ne ya sanyata take wad'annan halayen, yanda take surfa 'karya a shekarunta shine abinda yafi bashi kunya. Iya saninsa da tunawarsa auren soyayya sukayi da Bintu, har yanzu ya kan tuna farkon had'uwarsu, zamanin soyayyarsu da irin zaman auren da sukayi cike da soyayya da biyayya, sai gashi ta kau da duk soyayyar dake tsakaninsu akan 'kaddarar da yake tunanin zata fishi d'aukanta, ta fallasar da duk sirrin aurensu, ta kunyata shi wurin 'yan uwa da abokansa, hakan bai mata ba saida ta fito duniya tana tona mishi asiri, amma duk wannan baisa yaji a zuciyarsa yana da niyyar tsinke igiyar auren dake tsakaninsu ba, har wannan lokacin yana jin a ransa Bintunsa zata sauya, zasu koma zamansu na amana kamar da.
" A sake bani dama ranka ya dad'e". Idrees ya furta muryarsa na rawa saboda tsananin takaici, numfashin gajiya al'kalin ya sauke yace "kamar yanda ka nema za'a baka damar biko ta 'karshe, zamu d'age 'kara zuwa 10 ga wata mai kamawa idan Allah ya yarda".
A haka zaman kotu ya tashi, cike da takaici Bintu ta nufo idrees tamkar zata dakeshi tana fad'in "amma wallahi baka da zuciya idan kuma kana tunanin zan dawo gidanka ne bayan duk abubuwan da suka faru to mafarki kawai kake wanda bazai zamo gaskiya ba, har abada zamana da kai ya 'kare ko kana so ko baka so sai ka sakeni wallahi".
Ba tareda ya furta mata komai ba ya fice daga kotun jiki a sanyaye. Ba tareda ya kula kowa ba ya hau motarsa ya d'auki hanya kai tsaye ya nufi gidan mahaifiyarsa domin ita kad'ai ce yake jin zai samu nutsuwa a wurinta.
Dattijuwa ce da bazata gaza shekaru 60 a duniya ba. Zaune take a madaidaicin palonta tana kallon wani shiri da ake gabatarwa a tv hannunta ri'ke da carbi tana ja a hankali. Sallama yayi ta amsa tareda maida dubanta gareshi tana murmushi tace "Sannu da dawowa idrees yanzu nake tunaninka nace wannan zaman ya mi'ka ba kamar na wancan karon ba".
Murmushin ya'ke kawai Idrees yayi baice komai ba tace "A kawo maka abinci ne?"
"A'a Hajiya".
Maida dubanta tayi kanshi taga yanda yake cikin tsananin damuwa, cikin kalamai masu tausasa zuciya wanda a bakin uwa kad'ai zaka samesu tace "Idrees ka barwa Allah komai kamar yanda nake fad'a maka a kowane lokaci. Turjiya a kan abinda baka da iko dashi bazai kaika ga nasara ba, nasan kana son matarka kuma dukkanmu bama jin dad'in sauyin da tayi, amma ya zakayi? Baka da iko a kan rayuwarta tunda ta shigar da maganarnan kotu bana tunanin akwai sauran kalmomin da zasu shawo kanta, kayi addu'a Allah ya za'ba muku mafi alkhairi".
Amsawa yayi a hankali yana jin tamkar ya zubda 'kwalla, dukda zuciyarsa har wannan lokacin bata yanke shawarar sakin Bintu ba amma kalaman da ta furta ke yawo a 'kwa'kwalwarsa suna sosa mishi zuciya, _Daga kai har 'ya'yan idrees bana bu'katarku a rayuwata. Babu abinda zaku tsinana min_
_(wallahi ban ta'ba sonshi ba asali ma auren dole aka min aka tilasta min aurensa, ban ta'ba jin d'igon sonshi a zuciyata ba ko da da 'kwayar zarra)_
A duk kalaman da bintu ta furta a kansa bai ta'ba jin kalmomin da suka sosa mishi rai kamar wad'annan ba, musamman kalaman da tayi akan 'ya'yansa. A tunaninsa yanda uwa ke son 'ya'yanta duk abinda zai faru tsakaninsu bazata guji ko aibata abinda suka haifa ba, sai gashi a gaban duniya ta bayyana 'karara basuda amfani a wajenta, shin me Bintu take nema a rayuwa da zata musu irin wannan?
Tambaya ɗayace take mishi yawo a zuciya "me yaywa Bintou da zafi haka data gwammaci ta wulaƙanta ƙimar da yake da ita a idon Duniya?"
Lumshe idanunsa yayi zuciyarsa na Harbawa tamkar zata keta ƙirjinsa ta fito, haƙiƙa sai yanzu ya ƙara gasgata cewa duk kyan ƙwarya da bazar ragaya take taka Rawa.........
Help us to share pls
YOU ARE READING
MENENE ILLA TA?
Non-Fiction"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar...