MENENE ILLA TA?
Safa da marwa take a tsakar gida wayarta na kunnenta, har wayar ta gama 'kara ba'a d'auka ba hakan yasa ta ja wani dogon tsaki tana 'ko'karin jifa da wayar sai kuma ta tuna idan ta jefar da me zata kirashi ta 'kare mishi cin mutunci?
'Kura ma wayar hannunta idanu tayi tana fad'in "har ni zai wula'kanta a cikin mutane? Abinda bai kai ya kawo ba kawai ka Kar'barmin takardar saki ka kasa sai jan zaman kotu kake? Zaka gane da wa kake wallahi idan ka shigo hannuna".
Tana rufe bakinta sai ga kiransa ya shigo, cikin sauri ta amsa ta nufi d'aki tareda turo 'kofa sannan tace "Hashim ni zaka wula'kanta a cikin mutane? Duk dramar da nayi a banza nayita kenan? Da kasan baka san aikinka ba tun wuri sai ka fad'a min na dena asarar kud'ina a banza, yardar da nayi da kai yasa na kawo shari'arnan kotunku amma sai zama ake ana tashi kana wani bashi damar biko, bikon uban me zai min takarda kawai nakeso".
"Calm down mana fatima, haba kamar baki san yanayin aikinmu ba? Shari'a fa ba abar wasa bace a haka ma sai magana ake ina d'aga miki 'kafa da yawa. Littafin da kike gani a gabana duk abinda ya faru dole sai na rubuta, duk 'kan'kantar shari'a sai anyi mata zama ya kai uku ko sama da haka kafin a yanke hukunci, idan har na yanke hukunci a 'kasa da haka aka duba littafina aka ga wani kuskure zan iya rasa aikina gaba d'aya. Tunda nace miki zai sake ki ki yarda dani ina bin 'ka'idoji ne kawai tare kuma da had'in kanki zamu cimma nasara. A zama na gaba na miki al'kawarin baza'a tashi ba sai ya sake ki".
Zama tayi tana goge gumi tareda maida numfashi sannan tace "wannan mutumi ko maye wallahi. Nifa da nasan haka rayuwarmu zata koma wallahi da tun farko bazan aureshi ba, banda tsinannen girman kai babu abinda yake nunawa. A kanka wannan 'kaddarar ta fara? Nifa bana tunanin ma 'kaddara ce shi yaso ko ma meye ya sameshi ya sameshi. Wani irin opportunity ne bai samu b ya watsar saboda girman kai da d'agawa irin na matsiyaci? Na gaji fa da igiyoyin aurensa a kaina wallahi aka sake zamannan bai sakeni ba dauya kotu zanyi".
Kwantar da murya AL'KALI HASHIM yayi yace "hakan ma ba zai faru ba insha Allah. Yanzu kina gidanku ko?"
"Ina can mana ina zani? Ai idan kaga na koma gidansa tarkacena naje kwasowa".
"Fatima ki dena tada hankalinki haka banaso na jiki a damuwa fa, karki sa tsufa ya fara bayyana a kyakkyawar fuskarki".
Lokaci guda murmushi ya ziyarci fuskarta ta wani langa'be kai tana fad'in "tsufa na nawa kuma mun aje zaratan 'yammata? Ai sai fatan cikawa da imani".
"Kina kallon kanki a mirror kuwa fatima? Babu wanda zaice ke kika haifi MARYAM saboda kyawun jikinki dan ma wannan mutumin yaso ya fara ma jikinki lahani. I missed you already na 'kagu a gama shari'arnan mu koma kamar da".
Murmushi tayi tareda sauke muryarta tace "me too, zan kashe wayar sai anjima". Ta 'karashe maganar tana lumshe idanu.
Fitowa tayi bayan ta aje wayar ta fara tattare-tattaren gida domin daga ita Sai Halinta take zaune a cikin gidan sakamakon mahaifiyarta tana yawan yi mata faɗa a gameda Rayuwa yasa ta daina zama tareda su. Tun farkon al'amarin mahaifin Bintu yake 'ko'karin nusar da ita illar abinda take 'ko'karin aikatawa ganin ta toshe kunnenta ya sanya shima ya zuba mata ido yana mata addu'ar shiriya domin shi kansa mamaki yake yanda Bintu ta sauya daga 'yar matsalar da ta fad'awa Idrees wanda shi sam bai ta'ba nuna alamun yana cikin wata matsala ba, amma abubuwan da bintu ke fad'i a kan 'kaddarar da ta fad'a ma idrees zakayi mamaki idan kaji.
_________________________
Shiryawa yayi tsaf dukda zuciyarsa a dagule take har wannan lokaci amma zai daure yaje yayi bikon Bintu na 'karshe dukda ya san abu ne mai wuya ta sauya ra'ayinta amma Zai gwada ya gani ko Allah zaisa a dace.
BILKISU ce ta fito daga d'aki cikin ladabi tace "daddy fita zakayi?"
Murmushi yayi sannan yace "eh zani wurin momynku ne na duba ta".
"Oh" bilkisu ta fad'a yanayin fuskarta na sauyawa sannan tace "to Daddy sai ka dawo".
"Okay Auta me kikeso na taho miki dashi?" Murmushi tayi ta kalleshi sannan tace "babu komai Daddy amma kar kayi dare za'a fara wannan film d'in 'karfe tara".
Agogon hannunsa ya duba yace "au kinga ko har na manta abinda za'ayi inaga ki d'auko mayafinki mu tafi tare kema kin kwana biyu baki je kun gaisa ba ko?"
Idanunta kaɗai ya kallah ya san tana kewar mahaifiyarta a tareda ita amma sabida kawaici irin nata sai ta danne tace "Umh daddy ni baranje ba kawai ka tafi sai ka dawo".
"No Bilkisu ni kaina nafi son tafiya tareda ke wataƙila sabida ke momynku zata iya Sauya Ra'ayinta. Zanso muje tare kema ki tayani bata baki ko Allah zai sa ta Amince, Idan muka je tare zamu dawo da wuri i promise in yaso sai muyi kallon dukda banaso kuna kaiwa dare da sunan kallo ga school".
"daddy 10 za'a gama film ɗi kuma ina tashi da wuri".
"Naji maza d'auko mayafinki mu tafi".
Cikin sauri ta koma ɗakinta sai yaji tausayinta ya kama mishi zuciya, yana jin kunyar abinda suke aikatawa shi da mahaifiyarsu a kotu, yana takaicin yanda ta wofantar da ƴaƴanta a kan abin duniya yana kuma jin ƙunar rai a duk lokacin da kalamanta suka faɗo mishi a ransa. Yasan shaƙuwarta da maryam babbar yarta tafi yawa amma yana fatan bilkisu ma zata iya shawo kanta ta amince su koma family ɗaya kamar yanda suke a baya
A mota babu wanda yayi ma wani magana har suka isa. Sannan ya aika bilkisu da kayan da yay mata shopping a H-MEDIX dake cikin gwarinpha ta kaima Bintu. Dukda bashi da tabbacin cewa zata karɓa ɗin amma haka yay ƙuru ya bayar a kai mata darajar ƴaƴan dake tsakaninsu,
Sannan ya gayawa Bilkisu cewar ta sanar da Bintu cewar yana Gaisheta kafin ta fito, sai dai ga mamakinsa sai ga bilkisu ta fito da ledojin da ta shiga dasu a hannunta, yayin da wasu kayan ta naɗosu a cikin mayafin data yafa ta dawo motar tana zubar da hawaye masu zafi da raɗaɗi....
Cike da damuwa gamida mamaki baiyananne yace "mai Gadon Zinaren Daddy meya sameki haka kike kuka?"
Tana shessheƙar kuka tace "cewa tayi na fitar mata dasu daga gidanta kuma wai bata buƙatar mu a cikin Rayuwarta har Abadah don babu abinda zamu tsinana mata sai Wahala...!" kuka ne ya kwace mata nan ta shiga yi kamar zata shiɗe.
Sai da tayi mai isarta sannan ta yi ƙoƙarin saita kanta gidun karta ƙarawa mahaifinta damuwa tace,"Dady ina ganin gwara mu tafi don ba zata fito ba na tabbatar da hakan..."
Yanda yaga zuciyar ƴarsa a karye ya sanya shima tasa zuciyar ta fara ƙoƙarin karaya. Amma kuma jarumtarsa da dauriyarsa irinta ɗa Namiji tasa ya kasa baiyana nasa Raunin a fili, don baiga dalilin da zai dinga addabar zuciyarsa da fitinar Bintu ba, koda itace Autar mata a Duniya lokaci yayi da shayar da ita ruwan mamakin da bazata taɓa mantawa ba.
Nan take wani ɓangare na zuciyarsa na cika da tarin takaici da nadamar sako bilkisu da yayi cikin matsalarsu. dukda wannan ba shine karo na farko da ƴaƴan nasa suka ga irin wannan Rashin ɗa'ar daga mahaifiyarsu ba.
Daidaita nutsuwarsa yayi tareda ƙoƙarin haɗiye ɓacin Ransa ya soma baiwa bilkisu haƙuri yana rarrashinta, cikin ƙanƙanin lokaci Yarinyar ta dena kukan Sabida indai baiwar iya tsara zance ne to Allah yayiwa EDRIS MUHAMMAD KANKIA wamnan ilhamar.
Duk ƙoƙarin danne kukanta da tayi hawaye bai fasa bin fuskarta ba, Shi kansa Idrees ɗaurewa kawai yakeyi sabida a yanzu haƙurinsa ya fara ƙoƙarin Gazawa. Tayiwa maryam a karo na farko ya danne yanzu kuma ta ma bilkisu, bazai bari ta wargaza mishi farin cikin ƴaƴansa ba sabida hujjarta mara tushe ba, haka kuma baya jin zai ɗauki mugun halin Bintu a wannan taƙin.
Don haka ya ƙudurtawa kanshi cewa sai ya shayar da ita ruwan mamaki idan har da rai da numfashi a tareda shi.......
Dn forget to vote
YOU ARE READING
MENENE ILLA TA?
Non-Fiction"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar...