MENENE ILLA TA ?
3
Tun daga faruwar wannan abun Idrees ya d’auke ‘kafa daga bikon Bintu, a kullum yana cikin addu’ar neman za’bin Allah har ya rage saura kwana d’aya komawarsu kotu.
A wannan rana yaci alwashin tattaunawa ta ‘karshe da Bintu akan rayuwarsu, ‘ya’yansa kawai yake tunani dukda a yanzun ma suna rayuwarsu lafiya babu ita amma yasan rashinta na matu’kar damunsu musamman Maryam da ta matu’kar sha’kuwa da ita, zai iya cewa bilkisu daddy’s girl ce tafi nuna soyayyar mahaifinta a kan mahaifiyarta domin a lokacin da suke zaman lafiya har kishin wasa Bintu ke nunawa a kan yanda Bilkisu tafi son daddynta akan momynta, amma yasan sha’kuwar uwa da ‘ya daban take.
Tunda suka dawo bilkisu ta rage walwala hakan yasa yake tunanin irin kalaman da ta fad’a ma ‘yar tasa, duk hanyar da zai biyo ma Bilkisu ta fad’a mishi gaskiyar abinda ya faru ta’ki har tana neman nuna ta fishi wayo a shekarunta goma sha biyar, daga ‘karshe ma dena bayyana damuwarta tayi ta koma cheerful kamar da amma yasan abin na damunta a zuciyarta.
Gidan hajiyarsa ya fara nufa kamar ko yaushe ya sameta tana zaune da carbi a hannu, ita kanta ta damu a kan case d’innan nashi domin da farko sam ‘kin amincewa tayi wannan aikin bintu ne ta dage lallai akwai abinda Ahmad ya ma Bintu, saida ya nuna mata cewar ‘kaddarar da ta sameshi ce bintu ta kasa d’auka sannan ta fahimceshi, da farko tana musu fatan sasantawa amma yanda sauran ‘ya’yanta ke bata labarin abinda ke wakana a kotu bata jin akwai alkhairi a cigaba da zamansu amma bazata ta’ba nuna ma d’anta wannan ba, farin cikinsa shine gaba da komai a wajenta.
Bayan sun gaisa sun d’an ta’ba hira yace mata “Hajiya gobe ne zamanmu na ‘karshe a kotu idan Allah ya yarda”.
“To Allah ya tabbatar da alkhairi, kayi iyakar yinka Idrees Allah ya sani suma yaran naka zasu shaida, duk abinda ya faru mai kyau ko akansinsa a gaba ka sani yana cikin ‘kaddararka kaji? Ya Maryam da school? Da kuma waccan tsohuwar mara jin magana?” Ta ‘kare maganar tana murmushin jin dad’i domin tuna rigimarsu da bilkisu, yarinyar tana da halaye da dama irin na ubanta musamman kafiyarsu a kan abinda suka sanya gaba”.
Murmushi shima yayi yace “suna nan lafiya ‘kalau, Maryam bata samun zama kinsan karatun jami’a da d’auke lokaci har tace min zatayi zaman hostel nace a’a, ita kuma bilkisu tana ta cewa zata zo miki kwana biyu ma”.
“Ai da ka taho min da ita na samu gidan nawa yayi albarka da surutanta”. Cigaba sukayi da hira ta sake bashi baki sannan ya nufi gidansu Bintu zuciyarsa na d’ar-d’ar.
Yana zuwa bata ‘bata mishi lokaci ba ta fito, saida taje dab dashi sannan tace “me kuma ya kawo ka idrees?”
“Bintu please…”. ‘Daga mishi hannu tayi tace “babu wani please da zaka cemin, kai wani irin maye ne mara zuciya? Idrees wai aurena da kai dolene iye? Nace ka sakeni ka’ki me kuma kakeso daga gareni?”
“Bintu ki dena d’aga murya a titi muke”. Ya furta ganin duk wanda yazo wucewa sai ya kallesu, ai tamkar ya ingizata ta sake wangale murya tana fad’in “ba zanyi shiru ba Idrees!! Dole ne na d’aga maka murya ka cuceni ka cuci rayuwata”.
“Bintu ya isa haka, duk abubuwan da nake saboda yaranmu nakeyi ba dan ni ba, bintu na san duk abubuwan da kike aikatawa a bayan idanuna kuma na danne d’acinsu da muninsu saboda soyayyar dake tsakaninmu da kuma darajar ‘ya’ya”.
“Don’t tell me rubbish!!”. Ta fad’a a gur’bataccen turancinta sannan tace “ka dena rainawa kanka hankali babu wasu ‘ya’ya da zaka yaudareni dasu, inace tare muka haifi ‘ya’yannan to na bar maka su har abada, babu ni babu su inuwarsu ma banason ganin, duk abinda ya shafeka na tsaneshi Idrees, kuma idan har kana da zuciya a ‘kirjinka to ka sakeni”.
YOU ARE READING
MENENE ILLA TA?
Non-Fiction"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar...