46

139 3 0
                                    


Yau Sunday antashi garin da 'dan banzan zafi, amra kam baccinta ta dunga yi sbd gajiya, already daman tayi planning Sai Monday zata fara zuwa school domin ta karasa duk wani registration dinta, cikin sauri ta shirya cikin wata doguwar rigar material tayi mata kyau, daga wajen cikinta ta daure da igiyar sai kayan ya fidda shape dinta ya maidata kamar doll baby,

wato amra irin matanda ake kira da hour glass babe ce, donma rashin jin dadi da hutu duk ya danne duk wani sirrin kyan ta, ahankali ta kwashi purse dinta da wayanta sannan ta fito bayan ta kulle kofan ta da pin, ahankali ta sauka daga lft din apartment dinsu sannan ta duba wayanta ko rider dinta ya iso, ba'a fi 2mins ba saigashi ya iso, kutsa kai tayi cikin taxi din,.. within some minute sai gasu sun iso mall dama already acikin app din da tayi requesting ride din ta rubuta inda zai sauketa,...anatse ta bashi kudinsa 30 dirhams sannan ta wuce cikin mall din, ahankali take tafiya tana kallon yanda mutane ke shige da fuce, gudun kartayi kauyenci yasa ta fara bin masu wucewa ciki, saidata zagaye first floor sannan ta hau second floor, ahanakli take fitar da wani sirhintattcen murmushin jin dadi da farin ciki, wajen ya matukar burgeta gashi babu mutane sosai kodan yau Sunday, saidata zagaye ko ina sannan ta fara siyan abubuwan da zata buqata, wajen kayan man shafa ta tsaya dukda batasan wasu ba, da daimakon attendant din wajen tayi mata recommending na skin dinta, ahankali ta dunga zagawa, saida tayi siyayya daidai karfin ta sannan ta shiga wani grocery shop acikin mall din, nan ma few abubuwan buqata ta saya irinsu fresh milk, hydrated water, apples, banana, da vegetables, saidatayi leda wajen uku manya sannan ta fara jin kugin yunwa dama bataci komai ba ta fito, wani dan karamin restaurant ta gani acikin mall din, ahankali ta taka har cikin restaurant din sannan ta zauna ta duba menu sannan tayi order ganin kudin abincin nasu is reasonable, saidata zauna for almost ten minutes sannan aka kawo mata ordern ta fara ci....

Amar's resident.
Amar ne zaune ah sitting room dinshi da alamu yana shirin fita ne, wayansa maqale akunnen sa yana magana cikin harshen turanci, sautin muryarshi ahankali yake fita tare da lumshe ido, sanye yake da white t shirt wadda tadan kamashi sosai qirjinshi ya cuko sosai cikin rigar tasa tayi mashi wani irin bala'in kyau sai wandon rigar shima fari yayi tucking din rigar acikin wando, kafarshi na sanye da wani black sandals wanda ya fito da siraren faratunan shi, wato Amar wani irin gaint cool guy yet arrogant guy ne mai ji da kanshi ga dukiya.
Tunda ya dawo daga Nigeria yake jin shi babu dadi kwata kwata gashi Monday zasu fara private training na new freshers armys, gaba daya babu wanda yasan da dawowar shi harda office dinsu achan headquater gaba daya, abokinshi hammam ne kawai ya sani wanda suka hadu tun farkon zuwan amar dubai tare suka kammala karatunsu ah lugard university lokacin suna samartakar su, hammam da ne ga babban mashahurin dan kasuwa anan kasar dubai kuma iyayenshi haifaffun yan kasar ne wanda ya zamana shima haifaffan dan kasar ne, shekarunsu kusan daya da amar, duk yanda kaga tsarina amar da kudi da isa duk hammam shima yanaji dasu kuma kusan halinsu daya saidai hammam yafishi sauqi sosai, he's easy going person not like amar wanda yake opposite.
Dariya amar yayi wanda ya karama fuskarshi kyau kumatunshi yadan loba dan dimple dinshi kwara daya ya fito, ''dude kaifa dan iska ne, daga dawowata zaka cikani da zancen mata, kai babanka fa ance malami ne amma abubuwan da kakeyi wallahi wani idan yaji sai yayi mamaki'' Magana akayi daga chan bangaren wayan, mikewa amar ya farayi har lokacin wayan na kunnenshi, katse wanda yake waya dashi yayi sannan yace ''let me get back to you'' sannan ya datse call din... dialing wasu numbers yayi sannan ya kara wayan akunne yace ''get the cars ready, will be out in a minutes'' kashe call din yayi sannan ya dauka yar karamar briefcase dinshi black leather sannan ya kama hanya fita daga parlour din, ahankali ya sauka har ya fito main compound din penthouse dinshi, motoci guda biyu ne ajere, daya escort car ce  wanda mutun biyu ne kawai aciki wasu black americans karfafa sai wata army green G-wag wanda tasha tint abayan plate din motor an rubuta (uaeaf) -1 kamar sauran motocin dake pake ah compound din anyi masu lillibi, ahankali daya daga ciki escort din da yake cikin g-wag din wani farin balarabe ya fito sannan ya sara mashi,hannu kawai amar ya daga mashi sannan balaraben ya bude mashi kofar seat din baya, anatse amar ya shiga ya zauna suka ja moton.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now