47

139 4 0
                                    

Amar kuwa tunda ya iso penthouse dinshi wanka kawai yayi ya shirya cikin wani lallausan shorts baki sai yar vest wadda ta kamashi sosai, daman shi ma'abocin kaya marasa nauyi ne lokacin har anyi sallan magrib, sallah kawai yayi sannan yaci dinner ya sauko parlorn kasa yana kallon world news, gefenshi kuma laptop dinshi ne yana dan ayyukan office wanda aka tura mashi ta email akan wasu yan ta'adda ta suka addabi wani sashe na kasar dukda kasar tasu akwai security mai tsauri amma wannan kungiyar babba ce wadda shekaru da dama suka dauka tun yana junior officer yake ganin manyan ogannin shi suna wahala akansu amma tun alokacin yayi alqawari komin daren dadewa saiya kawo karshen su, domin safarar kwayoyin da human trafficking da suke yi cikin sirrin abin kamar ba aikin bil adama ba amma shi yasan cewa mutane ne kamar kowa suke yi amma kasancewar su kwarru wajen kaucewa duk wani dalilin dazaisa agano su yasa suke kubuce masu kuma abin mamaki da'an yi sa'a za ah kamasu kuma shikenan sai komai ya ruguje.

Yana cikin research dinshi aka danna bell, anatse Pablo yazo ya wuceshi ya danna pins sannan ya bude kofar, hammam ne ya shugo, fuskarnan tarr da murmushi gwanin burgewa, amar najin sallamarsa ya gane shine sbd babu mai zuwa kai tsaye har gaban smart door dinshi ba tare da m-5 yazo ya sanar dashi ba, tun kafin ya karaso amar ya fara Magana ''dude meya kawoka gidana, na dauka ay kwana zakayi da babe din taka zaka zo ka kula,... dariya kawai hammam yayi sannan ya zauna kusa da kujerar sa ''guy ya gajiyan hanya ya kabar Amma da dan iskan qanin ka dinnan ko yayan ka oho de".. yayi saurin kawar da maganr da amar yayi mashi... ''amma is fine, useless bastard dinchan kuma saboda shi na juyo kawai, because babu amfani zama gida daya da mara hankali, mutumin da girma baisan ciwon kanshi ba, kuma babu mai tsaya mashi kamar Ammaa, but dukda haka babu abinda ya dameshi da al'amarin ta...kasan stupid dinnan mai yayi kuwa? Gyara zama hammam yayi sannan amar ya cigaba... ''saboda bashi da kunya mace ya kawo cikin gida fa, kuma abin haushi Amma na kallonshi ta kasa cewa komai, duka ne kawai banyi mashi ba dukda ya girmeni da but babu abinda zai hana na zane shi, I was pissed and I confront him sbd bai dace duk iskancin da zaiyi yayi agabanta ba, atleast sai yayi respecting dinta tunda gidan mijinta ne dukda shima gidan mahaifinshi ne, ni I wonder why amma is living with babanshi, that man is worse anan danshi ya gado halayyanshi'' ...nunfasawa yayi yana furzo wata zazzafan huci, fatar jikinshi har wani jaaa tayi sbd yanda abin ya bata mashi rai sosai''.. kallonshi hammam yayi sannan yace '' come on man, kadaina barin matsalar shi yana damunka, kawai ka kula da Amma ka fita sha'anin su"....hira suka danyi inda ya jefi jefi hammam ke tambayan shi maganar binciken da sukeyi ko ya samu any update... shiru kawai amar yayi baice komai ba, ganin haka yasa hammam cewa ''nikam akwai wani hint dana samu, dagowa amar yayi ya kalleshi kamar bazaiyi Magana ba yace ''uhmm'' kallonshi hamman yakuma yi sannan yes ''na saka secret agent as workers na dessert safari anan na samu labari tanan zasu fitar da sabbin kwayoyi but ina bincikawa saboda naga suna da wayo kuma akwai mai special brain acikinsu but I just hope mu samu yin nasara akansu yanxu kusan shekara biyar fa Kenan ana abu daya''.... Amar kam shuru yayi yana sauraron shi chan kuma yace ''forward all the information to my mail, I will check it, ganin hammam zai sake mashi Magana yasa ya mike yace ''I'm sleepy guy, kasan gobe zamuje private training hope you're ready''... tashi hammam yayi yana nufar kofar fita yace ''yes man good night saimun hadu achan gobe'' sannan yasa kai ya fice..nunfashi amar ya sauke, harga Allah yana son hammam aboki ne na kwarai sun taso tare but this time around bayajin akan wannan case din zai iya fada ma kowa nashi binciken saboda kusan sau uku saiyazo dab da cimma manyan drug dealers dinnan sai kuma su kubuce masa kuma yasan yan Nigeria ne kasancewar shi shima dan Nigeria abin yana damunshi ace wai daga kasarshi mahaifar sa ake wannan ta'addancin, wanda ya kasa gane daga ina aka tsaya masu da har suke kaucewa, dukda yasan gaba daya headquater dinsu wani irin standard tight security ne da babu ma yanda za'ayi ace akwai dan leken asiri acikin su, abinda yafi damunshi shine yanda harda trafficking yara ake yi daga kasashe daban daban kuma azo awuce ta nan abin yana bashi mamaki dukda yankin da akeyi is not popular but yasan manya manya ne acikin wannan harkar, amma sbd kwarewarsu yasa suke duk wani abunsu ta inda ba'a bawa mahimmanci.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now