After years komai ya soma dawowa kabiru, duk abubuwan da yake ciki babu wanda ya sani sai matarshi amina, matar arziki mai rufen sirrin mijinta, AMAR DA AMAN kuwa bayan sun gama secondary school ALH Yunus Taura wato mahaifi awajen amar ya hadasu harda dan kaninshi aman ya turasu uae, inda amar dama tunda ya taho yake son shiga army, kuma cikin ikon allah ubansa ya amince masa saida ya fara degree akan business tukunna ya shiga army service sbd hanya da kuma mutane da ubansa yake dashi yasa bai wani wahala ba ya samu approval daga uae national and reserve service committee ,aman kuwa sai yazo opposite, inda shi kuma ya fara karatan computer science, da farko dai abin gwanin burgewa tsakanin yan uwan, gaba gaba kuma sai ya zamana kamar amar ne babba akan aman wanda ya bashi akallah shekara biyu,ahankali aman ya fara lalacewa yana bin abokanai na banza yau shine clubbing, gobe drugs, tun baya neman mata har yazo ya fara inda amar kuma ya tsaya kan abinda yakeyi, yanxu shekarun amar 7 ah uae, inda yayi achieving abubuwa da dama sosai, tun bayan ya shiga uae army ya samu cigaba sosai a shekarun ne har yakai matakin da yake yanxuna senior officer wanda duk overall officers shine youngest senior officer kuma ya samu rank din yana da shekaru 27 aduniya , nan da shekara biyu zai zama general officer lokacin yakai 30 years aduniya. Zaman aman kuwa ah uae ya gagara saboda ya dauka shekaru kusan biyar yana computer science din da ya kamata y a gama ah shekara uku kacal, ganin asarar kudi yayi yawa yasa mahaifin amar Alhaji yunus taura sa shi dawowa don shi ya cigaba da kula da business dinsu anan Abuja.
Shekarun sunja sosai inda arana daya alhaji yunus ya fadi yamutu wanda mutuwar ta zama kamar abin al'ajabi, babu cuta babu makashi, Maryam taji mutuwar mujinta sosai wanda ya sanya ta shiga wani hali,amar kuwa lokacin yaje wani dogon training ah border inda ba'a samunshi ma kwata kwata ah waye saida ya dauka wata uku tunkunna ya dawo, koda ya dawo ya riski wannan tashin hankali na mutuwar mahaifinsa yasha wahala sosai yashiga damuwa amma kuma da yake yanada ibada da tawakkali yasa shi maida hankalinsa wajen ganin ya farantawa mahaifiyarshi Maryam wadda yake kira da (Amma) da kuma aikin sa.
Bangaren kabiru kuwa shima yaji mutuwar dan uwan nasa saidai abin mamaki shine tunda akai mutuwar nan da wata daya ya karba garamar alqawarin kula da business din dan uwanshi wanda lokacin da alhaji yunus taura ya na raye bai nuna ya damu da al'amarin business din ba, bayan mutuwar taura da shekara guda amina matar kabiru ta fara wata rashin lpy ta kashe sassan jiki, ahankali cutar take cinta harta fara cin jikinta ya zamto gangar jikin ce dai amma babu alamun tashi saidai takan danyi Magana, alokacin Maryam ta kula da ita sosai, kuma babu wanda ya kaisu kusanci sosai, aranar da cutar amina ta tashi gadangadan, idonta yana neman shanyewa anan ta nemi wata babbar alfarma awajen Maryam wanda har yau babu wanda yasan maganar da sukayi akan mecece, kuma Maryam tayi mata alqawari wajen cika mata burinta, aranar kuma allah ya dauka ran amina Allah yayi mata rahama.
Tun bayan rasuwar amina, Maryam ta dauka son duniya ta daura ma aman saboda ta samu kusanci dashi, dukda ta wani bangaren mahaifinshi ya nuna bayaso, daga karshe dai ta dage sosai akanshi har ta kaiga da kanta ta nemi kabiru ya aure ta duk dan ta kare aman dukda babu wanda yasan dalilinta, kabiru kuwa yaji dadin wannan batu saboda daman shi tun lokacin da yunus ya auro ta yaji dama shi ya fara ganinta bayan ga haka ma ayanxu da company ya dawo hannunshi bazai juya shi yanda yake so ba sbd duk wani shige da fice na company din da manyan contract sai yaje hannunta tayi signing before ya je wajen kabiru amma kuma idon tana karkashinsa dole shine zai zama gaba da komai, ganin haka yasashi cewa killing 2 birds with one stone, wato jifan tsuntsaye biyu da dutse daya.
Bayan wata guda kuwa akayi auren kabiru da Maryam, Tunda aman ya dawo Nigeria abubuwansa suka cigaba da zama worse tun Amma tana iya tanqwara shi har yazo yafi karfin ta, daga karshe ma dai addua'a kawai take mashi gashi nan da wasu yan shekaru zaikai shekara 32 wanda hankalinta duk atashe yake idan ta tuna da haka ayanxu shekarunsa 30 chip aduniya.
Wannan Kenan........Cigaban labari.........................
Washegari ta kasance Monday, Yau ne first day din amra a school. Da wuri ta tashi ta shirya cikin wata abaya mai kyau, wadda tadan haskata sosai sai tayi kyau abinta, dan flat shoe dinta ta saka sannan ta kwashi duk wani document dinta da za ta buqata idan taje, tana sauka kasa ride dinta ya iso, cikin mintuna da bai wuce 20minutes ba suka iso, tunda ga bakin gate hankalinta ya tashi, wato wasu zabga zabgan motoci ne suke shiga cikin school din, tunda suka shiga ciki kuwa nunfashinta ya dauke, babu abinda take aranta sai addua,..wato makaranta ce babba mai dogayen buildings aciki harabar makarantar,ga blocks daban daban ko ina sheqin glass yake tsabar tsafta,ga bishiyoyi duk wani lungu da sako, abin saidai Masha Allah ... parking drivern yayi sannan ta fito, parking space dinma abin kallo ne gwanin birgewa zabga zabgan motoci neatly anyi parking dinsu harda symbol din student a parking-space... daburcewa amra tayi sbd ta kasa gane inane ma hanyar reception, ahankali take tafiya harta tsaya wani bulding, ganin fitowa kawai akeyi ta ciki yasa ta kasa ganewa ko ta gaba ne nan kota baya haka yasa kawai ta tsaya abakin hanyar, mutane kuwa baqaqe da farare babu wanda yabi ta kanta, wani security ta gani da uniform hakan yasa ta matsa wajen shi ta tamabaye shi inda reception yake, nuna mata gabanta yayi yace ta shiga ciki, hakanan a tsorace ta kutsa kai cikin katon bulding din, kallon wurin tayi aranta tana cewa ''oh ni amrah ba yar uban kowa ba nice a makarantar yayan attajirai, a natse ta tako gaban kanta wajen wata baturiya wadda tasha suit ta yalce gashinta, karasawa tayi har wajen ta sannan ta fara yi mata bayani, aikuwa baturiyar tana duba system taga sunanta nan take ta turata wani office, tafiya tadanyi mai dan tsayi kafin ta karasa office din, mutun biyu ne aciki duk maza, nanma saida tayi masu bayani sannan suka umarceta data zauna, tana nan zaune sukayi mata komai, suka bude mata portal, suka mata school identification card sannan sukayi mata registration sannan aka aikata wani office din again domin karbar school package, nanma dataje suman tsaye tayi, komai is organize, anan suka bata wani wrapped package wanda batasan mene bama, daganan suka hadata da wata mata domin yi mata school tour idan tana so, ganin sauki yazo mata har gida yasa tace zatayi nan kuwa suka fara zagawa ko'ina harda department dinsu na yan medicine, saida ta jigata tukunna suka gama,babu inda basu jeba, department daban daban, café, wajen activities, halls, kai ko'ina, gwanin burgewa.
Amar kuwa vibration din wayansa ne ya hanashi sakat, ganin call din yayi yawa yasa shi yaye duvet dinshi mai sanyin kamshin daya lullube jikinshi dashi, baccin ne sosai a idonshi sbd bai samu ya runtsa ba sbd aikin da ya tsaya yana yi akan kungiyar nan da yake research akan su wato (The MKS) sai bayan sallar asuba ya samu yadan kwanta, ahankali ya jawo wayar, idonshi biji biji alamun baccin bai ishesa ba, picking call din kawai yayi baima lura da ganin wanda ke kiransa ba, jin muryar hammam yasa shi dan gyara zaman wayan akunnen shi ''dude kana ina ne, nazo headquaters ban ganka ba freshers officers na nan kowa yana zaune kai ake jira koka manta cewa kaine zakayi leading wannan private training din" hamman na kaiwa karshe ya kashe wayan kawai, ahankali ya yaye duvet din, handsome builded body dinshi suka bayyana sakamakon pija's din tashi mai botirs ajiki ce amma duk ya ciresu, miqa yayi bakinshi dauke da salati sannan ya fara kokarin saukowa daga bed dinshi, ahankali ya fara tafiya har ya wuce tapkeken toilet dinshi kamar sarki, wakanshi yayi atsanake ya fito daure da white towel a waist dinshi sai daya ahannun shi yana goge fuskanshi anatse, closet room ya shige direct ya tsaya wajen dresser ahankali ya fara jawo man shafawan shi na HEMZ moist cream ahankali ya shafe jikinshi sannan ya dauko body sprays din hemz din ya fesa, saida yayi ruwan body sprays awajen kamar zasu kare sannan ya wuce wajen closet dinshi, ahankali ya bude wata drawer wadda ke shaqe da kayan army, zaro rigar yayi daga hanger ya aje akan ottoman din dake wajen sannan ya zaro wando da kuma wata farar riga da, bayan ya rufe ya bude bude wata drawer inda cike take tap da shorts da vests farare kal, suma zarowa yayi sannan ya fara shiryawa, kayan sunyi masifar amsar jikinshi, rigace mai pattern din camouflage na uae army, color din medium brown da yellow-greenish da pinkish tan kadan ajiki, nan take ya fito a zallan shi wato SENIOR OFFICER AMAR OF UNITED ARAB EMIRATE ARMED DEFENCE FORCE(UDF) kayan sunyi masifar yi mashi kyau sosai, idonshi har wani sheqi yake yi tsabar kyau,ahankali ya shiga wani corner row ya bude wajen shima ashake yake da takalma, wasu zafafan booth ya kwaso kalar kayan army din sannan ya saka sock ya zura su, saida ya feshe jikinsa da turaren Hérmer pérfumé sannan ya jawo wata army bag dinshi ya kwaso wayanshi da laptop dinshi ya fito, koda ya sauko Pablo yagama shirya mashi breakfast bai wani ci abin kirki ba ya fito, arniyar g-wagon dinshi ce akaiyi parking daidai main entrance din, ahankali m-5 ya fito ya sara mashi sannan ya bude mashi suka fuce, tafiyar minti talatin sukayi suka iso har headquater, security ne sosai tun daga kan layin shiga head quarter din, tunda securities sukaga plate numbern motorn shi basu wani tsaya yin bincike ba kawai aka bude masu first gate, koda suka iso second gate ma hakan akayi har suka isa daidai wannan tapkeken bulding wanda akalla zaikai hawa wajen goma, m-5 ne ya bude mashi kofa bayan ogan nashi ya fito ya kwaso bag dinshi da laptop dinshi, ahankali ya fara takawa har suka isa kofar shiga, saida kofar tayi scanning dinshi sannan ya shiga ciki,,,,wato wani irin kamshi da sanyin aircon ne ya badade duka wajen, wani irin tapkeken reception ne inda mutane armys daban daban kowa yana shige da fuce, ganin wanda ya shugo yasa kowa qamewa suna sara mashi domin girmamawa, hannu kawai shi kuwa yake dagawa har ya isa lift ya shiga tare da m-5 sannan suka wuce 5th floor, lift din na budewa ya tunkari katuwar kofar dake facing lift din, wadda ita kadaice ah floor din, m-5 ne ya bude mashi suka saka kai suka shiga,koda ya shiga mutane ne burjik wanda akalla zasukai su talatin kuma shekarunsu bazai wuce shekaru ashirin ba kowannen su sanye da uniform kusan irin daya dana amar saidai da 'dan banbanci, mikewa duka sukayi sannan suka fara sara mashi, kallonsu yayi daya bayan daya sannan ya daga masu hannu kawai, yace ''get all your ass ready nowww!! Kamar yana fada, aikuwa kowa ya qame sosai suna ''yes sir'' fita yayi suma suka firfito, suka fara sauka wa kasa ta stair case shikuma ya wuce lift suka wuce last floor na chan sama, direct ya wuce wajen army helicopter m-5 yana biye dashi, koda ya shiga hammam ne zaune yana waya, saida yagama tukunna amar ya fara mashi Magana ''dude I'm so sorry earliar kwana biyu bana samun barci wallahi'' kallonshi hammam yayi sannan yace ''amar is there something wrong naga kwana biyu you've been acting kinky, remember we're the closet friends, ko har yanxu binciken ne ya tsaya maka, guy you can just take a break'' jinjina mashi kai kawai amar yayi sannan yadan lafe ya rufe idonshi har suka daga...
Shida hammam ne kawai sai m-5 acikin helicopter din while sauran freasher officers din kuma sukabi manya manyan motocin armys... tafiyace sukayi mai tsayi sosai inda su amar suka isa da wuri har suka shirya camp dinsu da zasu dinga kwana a border din kafin yaran suka iso suma suka harhadu lokacin har dare yayi, daman duk sanda za ayi irin wannan training din sai anyi masu providing komai inda ake hadosu da nurses daga different universities da suke housemanship acikin headquaters hospital sbd babu asibiti anan camp din kuma bayan gari ne sosai wajen border din kuma babu wani electricity awajen sai solar.
note!! Akwai wasu part din da za ayi da larabci tho ban iya ba amma zanyi kokari in sha Allah....
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomanceAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...