ABUJA NIGERIA
MAITAMA
Wata matace da bazata wuce shekaru 40 ba, azaune kan wata luxurious kujera, tana sanye da lace red yasha dinkin stones kana ganinta kaga kudi ya zauna, jin karar saukar motoci yasa tadan mike, ba ayi ko minti biyu ba saiga wani babban mutun ya shigo da sallama, da fara'arta ta karaso har gabanshi sannan tace sannu da dawowa, kallonta yayi sannan yace ''yawwa'' na sameku lpy, takawa sukayi har sama wajen part dinshi, saidata taimaka mashi ya yi wanka sannan suka sauko kasa, dining direct suka wuce tayi serving dinshi abinci kala kala wanda tunda ta bude warmers din kamshi ya cike parlorn, abincin ya fara ci atsanake, jin takun tafiya yasa shi dagowa shida ita, wani saurayi ne yana sanye da kaftan brown hannunshi rike da waya kanshi yasha wani dan iskan aski na zamani, gefenshi wata chika ce da alamu daga daki suke ya fito rakata, saidaya rakata waje ya juyo ya shiga cikin sitting room, direct dining din ya wuce fuskarshi sakayau babu alamun jin kunya yace ''Amma mai kike dafa ne naji duk kin cika gidan da kamshi'' ganin wanda ke gefen wadda ya kira da amma yasashi cewa ''ahh dad yaushe ka dawo daga US din ne'' kallonshi yayi sannan yace Aman what is the meaning of that? Shi iskancin naka bai tsaya awaje ba har cikin gida? Ban hanaka yin komi ba amma ka daina kawo min any trash cikin gida," sunkuyar dakai kawai yayi sannan ya kalli Amma yace 'atura yar aiki ta kawo min part dina sannan ya fuce abinshi,'.... Allah ya shirya kawai amma ta furta sannan ta cigaba da abinda take...
Abinci ta shiryama aman sannan ta kira yar aikin gidan lantana takai mashi,Alhaji kabiru kuwa daya lura matar tashi Maryam bataji dadin abinda aman yayi ba sai yayi kokarin tausasa ta har ya samu ya sakko suka wuce part dinshi biya buqatarshi sannan ya fuce daga gidan domin attending wani aiki,..sabon wanka Amma tayi sannan ta sauko kasa har kitchen domin bata cikin matan da suke bari yan aiki suyi masu girki, suna cikin aiki itada yar aikinta lantana suka jiyo sallama daga parlor, saidata aika lantana domin dubo ko wanene tukunna kafin ta fito daga kitchen din, da fara'arta ta karaso parlor sannnan tace ''malam labaran yauma anzo kwasar gaisuwar ne'' dariya wanda aka kira da labaran yayi sannan yace ''barka da fitowa hajiya Allah ya kara daukaka''..wuri ya samu ya zauna suka gaisa sannan daga bisani ya fara Magana ''hajiya bazan taba gajiya da yi maki godiya ba da dawainiya, hajiya kinyi min rufun asirin da alokacin nafi buqata, Allah ya albarkaci zuri'ar ki nagode sosai''....murmusawa tayi sannan tace haba mlm labaran nayi nayi dakai kadaina min godiyar nan yau shekara kusan bakwai Kenan, ko gajiya baka yi, ai duk mai Imani ya ganka alokacin dana ganka dole ya taimaka maka, Allah dai ya rufa asiri, kana dai shan magungunan ka ko?'' kansa akasa yace ''nagode sosai hajiya inasha, yanxu ina dan tuna wasu abubuwan,alqalami ne dai idon na gani saina dunga fargaba amma shima cikin ikon allah komai zaizo da sauki nagode sosai, Allah ya kara arziki nagode sosai'' nunfasawa tayi sannan tace ''ya gidan gonar kuwa? Nasa aman ya sa asiyo taki akawo'' ..kallonta ya danyi sannan yace ''toh inaga ya manta kuwa domin abinda ya kawoni kenan''... shuru ta danyi daman tasan aman bazai yi ba..dukda ba wani nisa gidan gonar nata yake ba daga gidan.. sallama labaran yayi sannan ya fuce, kitchen din ta koma tana yaba halayya irin ta labaran, tunowa da ranar data fara ganinshi tayi lokacin suna kan hanyar dawowa daga Bauchi ita da aman, yawo yake duk cikin jini daga gani kasan accident yayi gashi baya iya cewa komai dalilin juyewa da kwakwalwarshi tayi (memory loss) haka ta dauko shi tundaga Bauchi har Abuja wanda aman baiso haka ba, ita ta taimakeshi har ya fara iya Magana daganan ta bashi amanar gidan gonarta yana kula mata dashi.Amar kuwa Yau kwana biyu rabonshi da baccin kirki bayayi, yana jira order daga manyanshi domin kamo mutanen da yake hari, yasha wahala yau kusan shekara guda da dawowan shi dubai babu abinda yake sai binciki, ganin kamar ogan su general officer bai maida hankali gurin target dinshi ba yasashi kawai shiri domin gudanar da qudurinshi dukda hakan zai iya saka aikinshi at risk kuma bai fadama kowaba banda amintaccen guard dinshi m-5,tafiya sukayi mai tsayi sosai shida m-5 sun tsallake safari dessert inda suka samu makafa, shikanshi yasan it's risky saboda basuda yawa amma dukda haka yaci alwashin kawo karshen su kobai samu ya kasha su duka ba atleast zai samu ya kama wasu daga cikin mutanen su, boyewa sukayi bayan sun saita bindigunsu, daga gefe kuma m-5 ya rike da cobalt bomb, sun dauki wajen mintuna ashirin kafin motocin targets din suka fara wucewa kusan guda uku, saita su yayi sosai, ya fara counting one two... karar walkie talkie ta dawo dashi, kamar bazai dauka ba sai chan kuma yace copy...jin muryar hammam hankali atashe yana cewa ''amar amar can you here me? It's a trap get out of where you are now, your life is at risk your work is also at risk''..dipp wayan ya dauke, hankali atashe ya kalli m-5 yace widraw it's a trap... aguje sukabar wajen sannan suka shiga motorn su, suna fitowa daga dessert din kuwa signal din wayanshi ya dawo, saiga call nan ratata, kanshi kawai ya kwantar yana maida nunfashi, ya rasa wannan wani irin abu ne, second daya ya rage ya cin masu saidai kuma ya makaro, daman abinda yake gudu Kenan gashi ya tabbata, dunkule hannunshi yayi ya buga gaban kujerar moton har hannunshi yayi jaa, iska ya furzar mai zafi sannan yacen ''damn itt'' kallon m-5 yayi sannan yace "get us out of here in ten minutes, aguje m-5 ya fara fusgar moton within 20 minutes suka isa headquarters koda ya shiga office din nashi ogansa ya gani da wasu biyu daga cikin ogannin sa sai hammam,wanda yana qame kamar zaiyi kuka idonshi yayi ja sosai... sara masu aman yayi sannan yace ''generals greetings sir from senior officer rank 5 sannan shima ya kame '' kallonsa sukayi sannan daya daga ciki ya fara Magana ''how could you take a serious operation without an order'' da sauri amar yace ''I'm sorry sir'' kallonsa wani shima yayi sannan yace ''inbanda kana cikin manya manyan senior officers da muke dasu da yau dinnan zaka bar aikinka".. kallonsa ya kuma yi sannan yace "you're suspended for two weeks and this case has been transferred to hammam shuraim abdulsalam, do you have any objections?".. da sauri amar ya amshe da "no sir"... fucewa duka sukayi ya zamana dagashi sai hammam, wucewa amar yayi baiko kalli hammam da ya kasa hada ido dashi ba yace ''congrats dude'' juyowa hammam yayi sbd baiyi tunanin zai kulashi ba ayanxu sanin halinshi... kallonsa yayi fuskarshi gwanin ban tausayi yace ''I'm so sorry dude, I try to explain it to them but''.. katseshi amar yayi yace ''no need'' sannan ya miqe yayi fucewanshi, gida ya tapi direct lokacin har anyi sallan isha'I...wanka kawai yayi sannan yayo sallah ko abinci bai nema ba ya kwanta saboda wani azababben ciwon kai dake damunshi.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomanceAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...